BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL
Kama hannunta tayi tana fad’in “Muje ciki na samu zagina a wurin Ummy tun yanzu, yau nasan har uwata sai Ummy ta ci.”
Cike da raha tace “Ai ko ni zan kama mata, kina matar uban d’aurin aure ace anyi biki babu ke.”
Bushewa sukayi da dariya inda Hamna tace “Kinsan kuwa mutumin naki ya tafi majalisarsu wai zaiwa duk wanda bai zo d’aurin auren ba rashin mutunci, sannan su biyashi katin d’aurin auren daya raba musu.”
Girgiza tayi tana dariya tace “Yer uwa wannan mijin naki ki dinga tofa masa lahaula kowace safiya, sannan ki dinga binshi da ayatul kursiyu dan bai rasa shafar mutanen b’oye.”
Hararanta tayi tace “Sayyada bana son iskanci fa, mijin nawa?”
Cikin dariya tace “Ai ni labarinku ma zaki ban wallahi ina da marubuciyar da zata rubuta min shi.”
Dafe k’irji tayi tace “Ni? Rufa min asiri, idan ya gani babbaka ni zaiyi da raina.”
“Ba wani nan, ni zanje har gidan na same shi sai ya yarda ko baya so.”
Dariya tayi tace “Gaki gashi ne ai kar tasan kar.”
*Ammar* na zuwa duk ya tashi hankalin bayin Allah, kububuwa ya dinga musu ai duk sai ya ci ubansu tunda basu je d’aurin auren fari daya fara ba, sannan su tattara mishi katinshi su bashi inba haka ba zasu ga tsiya, su uku ne a wurin da basu je ba su dai hak’uri suke bashi amma da yake sauran da suka je suna zuga shi saiya dinga botsarewa, fad’i yake ai basu da mutumci ne shiyasa suka mishi haka, kenan ko auren Amreerarsa ya tashi haka zasu mishi? K’arshe dai yace a bashi katinshi kad’ai zai hak’ura, biyu daga ciki har motarsu suka duba basu ga katin ba suka ce bari suje gida su d’auko.
Rigarsu ya rik’e yace “Yo ni saida naje gida na d’auko muku? Anan na baku nima anan zaku ban kayana.”
D’aya ne yace “To ai shine zamu d’auko maka a gidan ko.”
“Ban yarda ba, a bani yanzu kawai hankali ya kwanta, ko a biyani da kud’i.”
Wani daga zaune dake ta musu dariya ne yace “Eh su biyaka da kud’i, kati fa yanzu tsada yake, kuma irin wanda kayi ma na manyan mutane ne mai tsadar gaske, ya kai jaka goma fa wannan.”
Kallonsu yayi yace “To kunji dai da kunnenku, dan haka a fiddo a bani kud’i na yanzu.”
D’aya da abun ya dame ni ya fiddo jaka gomar ya mik’a mishi yana fad’in “Allah ya rabaka da wannan jaraba Ammar, wallahi ni daga matata ta farko har ta biyu babu wacce ta tab’a titseni irin haka akan abu, yo ni naga jaraba da zafi zafinta.”
Saida ya soka jaka gomar aljihu yace “Yo suma sakarkaru ne matan basu san yanda zasu amshi kud’i a hannunka bane.”
Haka dukansu suka biyashi kud’in katinsu kafin ya rabu dasu, mik’ewa yayi yana fad’in “Sai anjimanku to.”
D’aya daga ciki ne yace “Allah raka taki gona.”
Saida ya kwaso shoki ya yarfa mishi yace “Na dai ji, sai dai haushi wallahi.”
Suna kallo ya tayar da mota yayi gaba, wajen wani mai soya doya da kw’wai da kaji ya tsaya, ya mik’a mishi abu amma kuma bai amshi komai ba ya wuce, saida suka ga ya bar wajen inda wani ya tintsire da dariya yace “Ammar jaraba, Ammar bala’i, Hamna na hak’uri da bawan Allahn nan.”
Cikin wanda suka bashi kud’in ne yace “Ni yanzu kud’in nan daya raba ni dasu daya bar min kayana wallahi dana bawa amarya data nemi kud’in anko.”
Wani ne yace “Saika bata wasu mana.”
Babban aminin Ammar ne yace “Kar ma kace zaka mishi Allah ya isa, kud’inku bashi zai cisu ba, in kuma kayi gardama je ka tambayi Buharin kaji.”
Tashi yayi kuwa da sauri yaje waben mai doyar Buhari, ko da ya ganshi yace “Mutumin yane?”
“Lafiya lau, wai Ammar da naga ya tsaya nan me yace maka?”
Cikin murmushi yace “Kud’i ne ya bayar yace duk magidancin da ya zo siyan abu a bashi kaza d’aya.”
Cikin kafe shi da ido yace “Nawa ya baka?”
A tak’aice yace “Jaka talatin.”
Juyowa yayi yana fad’in “Ta tabbata gaskiya ya fad’a, kud’inmu ne yayi sadaka dasu, to Allah ya bashi ladar da mu baki d’aya.”
*Ameeeeeeeeen*.
*Alhamdulillah*
04/11/2020 à 14:40 – Ummulkhairi: ❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️
*BADAK’ALA*
❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️
*Labarin Gaske*
*NA*
_SAMIRA HAROUNA_
*Litattafan marubuciyar*
*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D’AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD’I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K’ADDARARMU_
*8* _K’ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k’ura)…_
*14* _BADAK’ALA…_
*SADAUKARWA GA*
_*AHALI NA*_
*ALHAMDULILLAH Allah abin godiya, kamar jiya ne na fara BADAK’ALA yau gashi na kawo k’arshenshi cikin hukuncin mai duka, Allah ya gafarta kuraraina da zunubina, Allah yasa muyi tarayya daku a cikin ladar baki d’aya.*
✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*
_(Tsintsiya mad’aurinki d’aya)_
☆ *[ T.M.N.A]* ☆ ️
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Bismillahir rahamanir rahim_
*FIN*
_80_
*Laraba* ce yau amma ko da ya fito zai tafi masallaci ya mik’ar da ita tsaye yace “D’auko hijabinki.”
Kallonshi tayi tace “Hijabina kuma? Ina zamu je?”
Fuskar nan a had’e yace “Hijabinki nace ki d’auko, ko gani kike zan siyar dake ne?”
Girgiza kai tayi ta juya ta d’auko hijabin ta dawo, hannunta ya kama har sun kai k’ofa taga ba mota zasu shiga ba, gabanta ne ya shiga fad’uwa ta tsaya tace “Yallab’ai lafiya? Dan Allah ka fad’a min me ke faruwa? Ina zamu je yanzu da rana haka?”
Ba tare daya kalleta ba yace “Masallaci.”
Da k’arfi tace “Masallaci? Yin me?”
Juyowa yayi ya kalleta yace “Me akeyi acan?”
Cikin tsoron kar ya zabga mata mari tace “Sallah.”
“To ita zamu je muyi, yan uku nake so na haifa, ko jiya saida Hajia ta min gori wai mijinta kad’ai ke da wannan bajintar, ni kuma ina so na kafa mata tarihi.”
Karantar yanayinshi ta shiga yi, indai bata amince ba zai ci ubanta, in kuma ta amince zata jawa kanta yan kallo, a k’arshe shi da kanshi zai iya mata hukunci yace ai ta shiga cikin maza, a hankali ta d’an girgiza kai a ranta tana fad’in “Ba fa yau na fara saninka ba Ammar, ka daina wahalar dani.”
Saida ta dafa kafad’arshi cikin rarrashi da taushin murya tace “Duniyata, kayi hak’uri mana kai ka tafi yanzu, nima zanje nayi sallah nayi mana addu’a, insha Allahu ranar juma’a tare zamu tafi masallaci, amma yanzu kaga ni ba nik’ab gareni ba, kuma maganar gaskiya ina maka kishin kaina bana so kowa ya kalleni.”
Yanda ta k’are maganar da shagwab’a saiya kalleta yana murmushi yace “Ja’ira kuma fa gaskiyarki, amma gaskiya Allah ya taimake ki dan da ace kin bini kuma naga ana kallonki…hummm da uwar mutum ta haifi wani yau.”
Wani kallon ba ga irinta ba ta mishi kafin tace “Gaskiya kam, shiyasa nake kiyaye duk abinda zai tayar min da kishinka, ai bana so ka k’ara karya ‘ya’yan mutane ba.”
Dariya yayi yana kallonta yace “Yar banza kice dai ba kya son jaruminki ya sake kwana a gidan maza.”
Dariya tayi tana fad’in “Ina zan so haka kai ma, Allah yanza ka sake tsokano rigima aka kamaka sai na zubar da cikin nan na jikina.”
Da k’arfi ya juyo yana kallonta yace “Ciki Hamna? Yaushe ki kayi cikin ban sani ba?”
Har ta juya da niyyar guduwa ya rik’o hannunta, da k’arfi ya matseta ya d’aga rigarta yana d’an tausa cikinta, ko da ya kai ga mararta ya danna tayi wata yar k’ara mai d’an k’arfi tare da ja baya, sake rik’ota yayi yana kallon idonta yace “Yanzu kankana dan kar na samu yan ukun shine kika samu ciki da wuri?”