BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL
Gambo ne ya kalle shi yace “Ku daina bashi hak’uri ma dan Allah, yanzu zai tura dreba ya d’aukota ya dawo da ita.”
Wani kallon ban son iskanci lieutenant ya mishi, shi ma hararanshi yayi yace “Allah sai kayi ko baka so, ba dan ma raini ba matar taka ta shekaru zaka yarda ta bar gidanta a wannan lokacin, to ina kake so taje? Ko kunya abun ba zai baka ba ace ta tafi gidansu, da yaranku da jikoki ku tsaya kuna abu kamar yara.”
Had’e fuska yayi yace “Gambo, kayi shiru da bakinka kafin ranka ya b’ace.”
Shi ma ba alamar wasa yace “Ya b’ace d’in mana, an fad’a maka ina jin tsoro ne.”
Tasowa lieutenant yana fad’in “Zan tosheka kuwa yaro.”
Da sauri Gambo ya tashi yayi baya yana dariya yana cewa “Ni ne yaron? Ni kake kalla ka kira ni yaro? Haba.”
Hajia ce tace “Karka tab’a min auta wallahi, inba haka ba ranka zai b’ace.”
Dawowa Lieutenant yayi ya zauna yana murmushi, Hadiza kam banda k’yalk’yata dariya ba abinda take, komawa yayi shi ma ya zauna yana dariya, Hajia ce tace “Dole zaka tura a d’aukota, kuma ba dreba kad’ai nake so ba, har da kai ma zaka tafi.”
Kallonta yayi yace “Haj…” Bata barshi ya k’arasa ba tace “Bana son jin wata magana, abinda ka mata zaisa taji kamar ba a bakin komai take a wurinka ba, ba zan lamunci haka ba gaskiya, matar data k’arar da shekarun rayuwarta a tare damu, ta maka biyayya ni kuma ta min bauta, haka kawai yau ka wulak’anta ta.”
Cikin marairaicewa yace “Shikenan Hajia zan tafi, amma ki min uzuri dan Allah har zuwa gobe, wallahi yau ina da muhimmin aiki a gaba sosai.”
Fuska a d’aure tace “Shikenan, kaje Allah ya bada sa’a.”
Da farin ciki ya amsa da “Ameen nagode.”
Tashi yayi ya kallesu yace “Sai anjima.”
Husseina ve tace “Allah ya tsare.”
Sada ya fita Gambo ma yace zai fita ya dawo kafin Hadiza ta shiga d’aki ta samu Hamna, kwance ta same ta gefenta farantin kankana amma da alama bata sha ba, zaune tayi tana kallonta tace “Tashi zaune zamuyi magana.”
Cikin muryar kuka tace “Dan Allah Mama in akan maganar nan ne kawai ki barta, ba zan iya ba wallahi.”
Ajiyar zuciya ta sauke tace “Tashi Hamna, c’est très important.”
Tashi tayi ta zauna tana ci gaba da share hawaye kuma wasu na bin wasu, kallon basira ta mata kallon fahimta tace “Hamna, me yasa kika ce ba zaki iya auren Ammar ba?”
Da sauri tace “Mama je ne peut pas, ba zan iya auren mijin yer uwata ba, kuma ni bana son shi ko kad’an.”
Saida ta karanci yanayinta kafin tace “Corrections, mijin yer uwarki data rasu zaki ce, sannan Hamna zaki iya aurenshi ko da baki son shi, kinsan me yasa?”
Da ido ta kalleta hakan yasa tace “Saboda shine uban d’anki Shureim.”
Da fari zaro ido tayi tana kallonta a firgice, sai kuma ta fad’a kan k’afafunta tana kuka tace “Mama kiyi hak’uri ki yafe min dan Allah, wallahi ba laifi na bane shine ya tirsasa ni, Mama bana manta tunatarwarki a kanmu kullum, dan Allah kiyi hak’uri.”
D’agota tana share mata hawaye tana ji kamar tayi kukan ita ma tace “Karki sani kuka Hamna, na riga dana yafe miki har da shi ma, bana so ki karyar min da zuciya kuma.”
Sassautan kukan tayi sai ita data d’ora da cewa “Hamna a gani na ki amince da auren shi, sai nake gani kamar ba zaki samu wanda zai dace dake ba kamar shi, sannan Hamna duk wanda zai fito neman aurenki yanzu ya zama dole a sanar dashi kina da yaro, kina ganin zai amince ya aureki duk yanda yake son ki? Ba lallai bane gaskiya a wannan yanayin da ake ciki, amma kinga shi ba zai k’yamace ki ba, zai rik’e ki kuma ya rik’e d’anku hankali kwance.”
Girgiza kai tayi tace “Mama zan samu amma ba dai Ammar ba, mutumin daya rabani da mutumci ne yaushe zan iya rayuwar aure dashi? Kuma shi ma fa kinji abinda yace yana da wacce yake so, to me zaisa na tusa kaina gare shi.”
Murmushi Mama tayi tace “Wallahi baya da wata wacce yake so Hamna, kawai ya fad’a ne saboda kinsan shi ba rainin wayo yake so ba, nasan yanzu yana can yana bala’i kin kalle shi kince baki son shi.”
Kallonta Hamna tayi tace “Mama kawai ko bar maganarshi, ni idan ma ban samu mijin aure ba zan zauna na ci gaba da kulawa da yara na.”
Da sauri tace “To ba gashi ba, Hamna kina son yaran nan sosai kuma kin k’i yarda kowa ya kama miki kula dasu, indai kina son ki ci gaba da rayuwa da su dole ki auri mahaifinsu, amma ba zan takura miki ba ki zauna kiyi tunani sosai, duk abinda kika yanke ki kira ni ki fad’a min.”
Tashi tayi zata fita tace “Mama ina zaki je.”
Juyowa tayi tace “Zan je gida na dawo na d’auki Ahmad.”
Fkta tayi inda Hamna ta shiga d’aukar kankanarta da d’aya d’aya tana sha tana kuma tunanin abinda Mama ta fad’a, lallai indai zata rayu da yaran da ko kukansu bata so dole ta bi shawarar Mama, amma kuma Ammar? Kai! Tana cikin wannan tunani wayarta ta shiga k’ara, d’auka tayi ta ga ko suna babu a lambar, d’auka tayi suka gaisa kafin ta tambaya wake magana, nan ya fad’a mata sunanshi tace bata gane ba, dan haka yace ta bashi izini ya zo zai ta ganshi ido da ido, burinta na son samun wanda ya dace yasa ta amince da ya zo anjima.
*Tsautsayi*
Bayan sallah isha’i ta gama shirinta cikin doguwar rigar shadda, duk da ba tayi kwalliya ba amma tayi kyau, wayarta ya kira ya shida mata ya zo, ko da ta aje wayar Imam ya shigo yana kuka wai Shureim ya dake shi, jawo shi tayi tana lallab’a shi ta bashi wayarta tace “Ka je kayi kallon abinda ka fi so karka bawa kowa, kuma zan ga Shureim d’in saiya gane kurensa.”
Cikin jin dad’i ya karb’a ya fita, ita kuma saida ta shafa turare sannan ta d’auki gyale ta yafa tasa takalmi ta fito, su Zeinabu ta samu a falo ta fad’a musu tayi bak’o a waje zata shigo dashi ciki, fatan alkairi suka mata ta fice.
Tana fita ta shiga mamakin wanda ta gani, kusa da salon d’inta yake nan take ganinshi zaune a wata fada, da mamaki tace “Kai ne?”
Murmushi yayi “Kin gane ni ashe? Na d’auka yanzu ma saina kwatanta miki.”
D’an murmushi tayi tace “Na gane ka mana.”
Gyara tsayuwa yayi yace “To ya kike?”
“Lafiya lau, mu shiga ciki ko, ba’a barinmu tsayawa kan hanya.”
Gabanshi ne yaji ya fad’i sosai, tambaya ya wa kanshi to me ya kai na shiga ciki? Shi fa ba wata babbar magana bace ta kawo shi wajenta. Murmushin yak’e ya mata yace “Amma kafin nan mu gaisa ki san suna na, in ya so sai mu shiga ko.”
“Amma ai duk zamu iya yi a ciki.” Ta fad’a fuskarta a d’an had’e, kallonta yayi yace “Hakane, amma in d’an jin tsoro.”
Wani irin kallo ta masa tace “Tsoron me kuma?”
Cikin rashin gaskiya yace “Eh to, kin gane? Kawai dai, gidan na ku ne, nasan mutanen cikinshi, akwai abokaina dayawa.”
Wani kallo ta masa zatayi magana Imam ya fito daga cikin gidan da gudu yana kuka, tana ganinshi ta durk’usa ta rik’eshi tana fad’in “Imam me ye? Waya tab’a ka?”
Kafin yayi magana Shureim ya fito da wayarta a hannu ya zo ya tsaya yana fad’in “Aunty wai dan na ce ya bani nayi jeux (game) shine ya k’i.”
Ranta a b’ace ta kalle shi tace “Shine ka fizga da k’arfi?”
Mik’ewa tayi tsaye ta kamo kunnenshi ta kwad’a masa mari tana fad’in “Shine zaka saka min yaro kuka? Dan ubanka ban hana ka tab’a min su? Wallahi ka sake karb’ar min a waya a hannun sai na ci ubanka a garin nan.”
*Hamna kin taro match fa, da kin duba bayanki kafin ki fad’i haka.*
*Ammar* da saida ya kusa kawowa gida motarsa ta tsaya, makanikenshi ya kira shi kuma ya k’araso k’asa saboda tafiyar ma na da anfani ga lafiya, tunda ya hangeta ya ganeta, k’ara hassala yayi dama a tafashe ya fita daga gidan, har yanzu yana nanata kalmar data fad’a ta *ina da saurayi*, ya rasa dalilin da yasa Hamna ta soka mishi wannan iskancin, a gaban iyayensu tace tana da saurayi kuma bata son auren shi. Sannan yazu ya dawo ya tarar da ita da saurayi a k’ofar gida tana hukunta masa yaro, wannan wace irin uk’uba ce? Bayan ta gaura masa mari kuma ta bishi da zagi, zagin ma ubanshi kawai take zaga, wato dan ta ga wani d’an iska a gabanta shine zata tsaya tana zaginshi, tunda dai ta zagi yaronshi ai da shi take.