BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL
Dariya tayi tace “Fad’uwa ta zo daidai da seat kenan, ai shi tuni ya rigaka isa can.”
Da sauri yace “No wonder yau mukayi magana dake perfect, banji yana ta min iskanci ba ko yana shinshinarki yana kissing d’inki ba, ashe jarababben baya gari.”
Dariya tayi harta fito suna ci gaba da raharsu, cikin zolaya yace “Dallah ni bani uwata na kwashi albarka.”
Saida ta k’araso kusan Ammie tace “What are u eaten na baka na following down? Gata in dai Ammie duk tsiyarka zaka bar min abata.”
Ammie ta ba wayar suka gaisa harda su Imranatu ma da sauran yaran kafin daga bisani suyi sallama.
♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡
Sai dare kad’ai Imran ya samu uwar d’aki ya fad’a mata abinda suka tattauna da takawa, ranta ya kai k’ololuwa wajen b’aci, ace d’an ta kuma babban d’anta wai ba zai iya fara sirri da ita ba, ba yabo ba fallasa ta nuna mishi ai ba komai kawai Allah yasa alkairi, dan tasan waziri zai lalata komai, shi kuma mamaki ne ya sa shi mik’ewa da k’yar ya mata sallama.
*Me waziri zaiyi? Wa sarki zai aura? Me zai samu takawa?*
_See u.✋_
03/06/2020 à 23:33 – Ummulkhairi: ❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️
*BADAK’ALA*
❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️
*Labarin Gaske*
*NA*
_SAMIRA HAROUNA_
*Litattafan marubuciyar*
*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D’AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD’I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K’ADDARARMU_
*8* _K’ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k’ura)…_
*14* _BADAK’ALA…_
*SADAUKARWA GA*
_*AHALI NA*_
*TAURARIN NIGER*
“`(Tsintsiya mad’aurinki d’aya)“`
_Bismillahir rahamanir rahim_
_7_
“Dan Allah baiwar Allah ki tsaya, zo ki shiga mota saina kaiki duk inda zaki je.”
Kasa had’a ido tayi da shi sai lumshe ido take kamar jiri zai deb’eta, jin ba tace komai ba sai k’ok’arin tafiya da take yasa ya sake tareta yace “Ki dubi girman Allah baiwar Allah ki saurare ni, ki zo na kaiki asibitin, zan taimakawa mahaifinki ya samu lafiya, karki d’auki abinda ya faru yanzun da son raina nima wall…”
Bai k’arasa saboda tafiya data fara yi, ji take kamar ta watsa mishi mari ko guda goma ne ko ta huce, amma kuma tsoronshi take ji, karta mareshi ranshi ya b’ace ya sake murk’usheta a wajen, dan ta fahimci sunyi hannun riga da imani, sake wucewa tayi ko kallonshi ba tayi ba bare ta saurare shi, shi kuma tausayin yarinyar ne ya kama shi sosai, juyawa yayi yana kallonta tana tafiya da k’yar waacce ya gani cikin karsashi wani lokaci daya wuce, wata zuciyar ce ta fad’a mishi “To me kenan kayi Jibril? Ka lalata rayuwar yarinyar daka had’u da ita yanzun nan? Yarinyar da ko sunanta baka sani ba, shin baka tunanin sanadiyar abinda ya faru ta rasa mijin aure? Ba ma wannan ba Jibril, shin kasan me zai iya biyowa baya sakamakon hakan? Kai tirr da wannan rayuwa taka.”
Da gudu ya sake tare gabanta kamar zai rik’e ta saboda yanda ya bud’e hannayenshi a dole tareta zaiyi yana fad’in “Kinga baiwar Allah, dan Allah ki zo muje mota sai mu tafi tare, na amince ki kaini wajen iyayenki na taimaka miki, idan har mahaifinki ya samu lafiya na miki alk’awarin zan aure ki, ki zo muje dan Allah.”
Wani kallo ta watso mishi dake nuna me ka d’auke ni? Amma ba tayi magana ba ta sake giftawa zata wuce, hijabinta ya rik’e tana juyowa suka had’a ido, ruwan dake sauka da k’arfi ne suka fara tsagaitawa a hankali, cikin raunin murya yace “Idan ba zaki aminta da ni ba dan Allah ki fad’a min sunanki da gidanku, zan zo, zan zo wajen iyayenki na nemi izinin aurenki.”
Wasu hawayen takaici ne taji sun taho mata bata shirya ba, wai yau ita ce wani namiji da bata san shi ba kuma akan hanya ya mata fyad’e, kamar a film ko kuma tatsuniya, ko kuma kamar ana rayuwa a garin maguzawa, da k’arfi ta bige hannunshi ta sake juyawa tayi tafiyarta, baya da zab’in daya wuce ya shiga motarshi ya tayar ya bi bayanta, ba jimawa suka isa asibitin, tana zuwa a k’ofar d’akin da mahaifinta ke kwance ta samu duk dangi an fito sai sharar hawaye suke, mahaifiyarta da ke kuka sosai ta matsa kusanta tana tambayar lafiya, shirun da kowa ya mata ya tabbatar mata da mahaifinta ya rasu, Mari na gamsuwa da abinda zuciyarta ta fad’a mata sai lokacin ta ji wani azababben kuka na bak’in cikin mutuwar mahaifinta da abinda ya faru da ita yanzun, durk’ushewa tayi wajen ta fashe da kuka sosai kamar ranta zai fita, nan dangi har da kakarta suka dinga rarrashinta suna bata hak’uri, amma Mari ta zama kamar dutsi ko jinsu ba tayi sai kuka kawai, duk abin nan dake faruwa a idon Jibril dake hangensu daga nesa, lura da abinda ke faruwa yasa ya k’ara jin ba dad’i sosai, gyara tsayuwa yayi da niyyar ko zai kwana nan sai ya ga gidansu, amma rashin sa’a sai kiran gaggawa ya shigo wayarshi cewa ana nemanshi, dan a lokacin bai jima da fara aiki da wannan projetn ba, kawunshi Gambo ya shiga gaba har saida ya ga ya samu wannan aikin, dan haka baya da zab’in daya wuce ya shiga motar ya bar wajen.
Ko da ya isa inda suka sauka ya d’auka kira ne na ka zo yanzu ka koma, ashe a lokacin wani abu ne ya taso da dole za’a tura su wani garin, kuma shine zai wakilci tawagar, haka suka kama hanya zuciyarshi kamar zata fashe, ya rasa meke mishi dad’i a rayuwa, kamar ya fasa ihu yake ji ko zaiji sauk’in abinda ke ranshi.
Nan gawar mahaifinta ta kwana zuwa safe aka yi bisarshi, har lokacin Mari kuka take ga azabar ciwon kai da zazzab’i da suka tasota gaba, ta k’i ci ta k’i shan komai sai kuka kawai, kowa kuma tunanin shi kukan mutuwar mahaifinta ne dan haka sai dai ace kiyi hak’uri mana, duk mai rai mamaci ne, addu’ar ki yake buk’ata ba kuka ba, a kwana a tashi sai gashi sun kwashe *sati d’aya*, a ranar wanda suke haya gidanshi ya zo yace sai dai su tashi ya samu wanda zai zuba a gidanshi, dama kuma bashi ne a kansu sosai, da k’yar wani mak’wabcinsu ya bashi hak’uri yace shi zai dinga biyan kud’i har zuwa lokacin da mahaifiyarta zata gama takaba, dan d’akinta ya dace tayi wanka.
Haka suka ci gaba da rayuwa tare da kakar Mari a gidan, basu da matsalar abinci saboda lokacin zaman makoki an kawo musu, har lokacin kuma Mari ta k’i sakin jikinta, duk wani motsi da zata yi sai taga kamar suna kallonta kuma zasu fahimci abinda ya faru, dan haka kullum da hijabi a cikin gida, mahaifiyarta kuma tuni ta kafa mata na mujiya tana bin dindigin kowane motsinta dan tasan ba haka take ba, kwatsam sai aka kwashe *wata uku har da kwana sha biyar* Mari babu al’ada, abinda ya kusa tarwatsa zuciyar mahaifiyar ta.
Ta fito daga ban d’aki da hijabinta da bokiti a hannu mahaifiyar take kallonta tayi wani fes sai d’aukar ido take, cikin kallon nan tace “Zo nan Mari.”
A hankali ta aje bokitin ta k’araso kusanta ta tsaya, hannu ta zura da nufin kama nata hannun ta duk’ar da ita sai kawai Mari da babu gaskiya ta zille, kallon mamaki ta mata tace “Meye? Mari kar dai abinda nake tunani ne ke shirin faruwa dake?”
Cije leb’e Mari tayi tuni ta fara sharar k’walla tana fik’i-fik’i da ido, dafe k’irji *D’iyar baba* (sunan da suke kiranta dashi kenan kasancewarta ‘yar fari kuma kakanta ne yayi rainon ta) tace “Na shiga uku na lalace, Mari iskanci kike dama? Yaushe kika lalace ban sani ba?”