BADAK'ALA COMPLETE HAUSA NOVEL

BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL

*Tunda safe* lieutenant yaje dan su tafi, k’in fitowa tayi da farko amma tanti Ardayi tace ba za ayi wannan da ita ba, hannunta ta kamo ta damk’awa lieutenant sannan tace “To Allah ya kiyaye gaba, Allah ya kaiku lafiya sannan aci gaba da hak’uri.”

Saida ya duk’a har k’asa yace “Nagode Hajia, Allah ya k’ara girma da d’aukaka.”

Ko da suka fito waje ta fincike hannunta ta tafi da sauri ta shiga ta zauna inda dreba ya bud’e mata, rumgume hannaye tayi sai had’e rai take har suka d’auki hanya, babu wanda yace ma wani uffan har sukayi doguwar tafiya, lokaci lokaci ya kan kalleta sai yayi murmushi ya juya shima, wai hushi take bayan ita ce mai laifi, saida sukayi doguwar tafiya suka tsaya kan hanya wata k’aramar shago ya kalleta yace “In akwai abinda kike so ki fad’a min?”

Shiru tayi kamar ba taji ba saida ya sake maimaitawa tace “Bana buk’atar komai.”

Kallonta yayi sannan ya kalli dreba yace “Mu tafi kawai.”

Suna hanya Hadiza ta kirata sosai suka gaisa kamar yanda suka saba kafin daga bisani suyi sallama, ko da yaji yasan da wa take magana dan haka ba tare daya kalleta ba yace “Mutuniyar kirki ce, dukansu sun yafe laifin da aka musu.”

Ita ma ba tare data kalleshi ba tace “Uwa ce ita, dole ta fahimci abinda yanda ya kamata.”

Murmushi yayi ya lumshe idonshi, shima fa yanzu baya jin haushinta kan abinda tayi, irin dai kawai shi namiji ne ba zai sauko da wuri ba, to kuma sai ita ma Ummyn ta hau sama, dan tun daga maganar nan bata k’ara cewa komai ba har suka isa garinsu.

Hajia da kanta ta kira Hadiza ta sanar da ita maganar nan fa babu fashi, kawai su ma yaransu addu’a ta alkairi, haka ma Gambo ta kirashi ta fad’a mishi ya kuma ce wuk’a da nama na hannunta duk yanda tayi su addu’a da kuma yanda take so ne nasu, da kuma su Ummy suka dawo da dare take sanar dasu, duka dai kowa farin ciki ya nuna, amma da Ummy ta samu Hamna da maganar saita nuna ita fa bata so, duk k’ok’arin Ummy na son fahimtar da ita ta dage kan ita bata son auren Ammar, ba wai ba zata iya aurenshi bane kasancewarshi tsohon mijin yer uwarta yasa ba zata iya zama dashi ba ita, k’arshe dai haka Ummy ta rabu da ita dan karta takura ta har ta amince ba da son ranta ba.

*Da sauri*

*Abu* kamar da wasa sai magana ta girmama inda Hajia tace mishi za’a saka musu rana, amma fa duk abinda yasan ya ma Amna sanda zai aureta ita ma saiya mata shi, bai musa ba yace ya ji ya gani shi ai yaga abinda ya gani kuma yaji abinda yaji a na farkon ma, dan haka ribarshi ce bata wani ba.

Tana ji sama sama aka saka ranar kawo kayan, haka duk take kallonsu da wutsiyar ido da gari ya waye taga suna shirin tarban bak’i, dan wannan karan tunda abun ya sauya daga dangin lieutenant zuwa na Ummy ga kuma abokan arzik’i da dangin Hadiza duk sun hallara, kamar yau ake d’aurin auren saboda yanda ake ta kayaniya ta ko ina.

Da yamma aka shiga shigo da akwatina, tunda taji bud’a gabanta ya shiga fad’uwa tana tambayar kanta wai dama da gaske suke? Ammar? Ita? Lallai za’a mutu, tana sama ita dai tana jin gidan kamar zai tsage, a sama sama take jiyo maganganun mutane inda suke fad’in “Lallai wani hanin ga Allah baiwa ne, wani jinkirin kuma alkairi ne.”

Saida aka ci aka sud’e an kawo ashirin ta arzik’i an koma da arba’in ta arzik’i, dan Hajia ta bud’e bakin jakarta ta zazzagawa kud’i rashin mutumci, a cewarta *auren sabon shalelenta ne* sannan ba k’arya k’ok’arinshi ya birgeta duk da dai tasan kud’i sun sake zaunawa yanzu, amma shima ya rintse ido sosai wajen kashe yayan banki.

Cikin k’ank’anin lokaci Hamna ta fara ganin statu d’in yan uwa har sun manna hotonta dana Ammar da kayan da kud’i da goro, statu d’in Sayyada (gaisuwa gare ki, sannunki da k’ok’ari da juriyar bayar da labarin yan uwan nan naki, wallahi kina k’ok’ari dasu amma dan Allah karki fad’a ma cousine d’inki Hamna), d’aya hoton akwatina ne har goma ras an jerasu wasu na bin wasu, sai hoto na gaba inda aka bud’e dukansu kowa taf take da kaya har suna amai, sai na gaba d’aurin goro har guda hud’u da kud’i zube kan carpet yan jaka goma goma na million biyu, sai wata malet daban mai d’auke da tanfatsetsiyar sark’ar zinariya k’irar Agadez babu algus a cikin tare da awarwaro, wacce ita kad’ai ma kud’inta sun ishi mai rai rayuwa.

Ba tace bata ji dad’i ba gaskiya, dan saida ta murmusa ma amma bata san na miye tayi ba, amma daga nan ta shiga tunanin yanda zasu yi rayuwa da mutumin nan, a gaskiya ba zata iya rayuwarshi ba ta sani, bata sani ba waye zai wahalar da wani cikin ita ko shi, gashi bata da ta cewa yanzu tunda sun riga da sun gama magana ba zata kunyata su ba, idan kuma iska ne jikinta dake hanata aure, to ta sani shi zai dakatar da auren inhar lokacin aurenta baiyi ba.

Washe gari tana duba sak’onni WhatsApp d’inta ta samu sak’on Amie wacce rabonta da ita har ta manta, sak’o ne na neman tijara gajera kamar haka _”Burinki ya cika tunda gashi zaki auri mijin da yer uwarki ta bari bayan ta mutu.”_

Ji tayi ba zata hak’ura ba ta maida mata da _”Na d’auka kin jima da fahimtar bana mu’amula da munafiki, amma bansan wace uwar kike nema tare dani ba.”_

_”Ba ko d’aya, sai dai har yanzu ina tausaya ma yar uwarki, sannan da kike cewa baki zama da munafiki, ni ya kamata na fad’i haka, ko ke baki lura dana bar kulaki ba tunda nasan wacece ke ba.”_

_”To kenan meya kaiki yi min magana kenan?”_

_”Dan na tayaki murna.”_

Cewar Hamna _”Na ko gode.”_

_”Mtsssss, anji haushin duniya, ki rasa wacce zaki ci amanar sai yar uwarki.”_

Fita harkarta kawai tayi dan a ganinta ba zata b’ata lokaci kanta ba, sak’on Sayyada ta shiga wacce ke tambayarta ankon da zata fiddo musu, dariya kawai ta mata ita ma ta share ta, dan haka ta turo mata da “Karki d’aukeni yar iska mana Hamna, zan zo gidan da kaina naje na fito da anko.”

Maida mata tayi da _”Hakan shi yafi, amma duk abinda zakuyi tsakaninku ne ni bana ciki.”_

Dariya ta mata ita ma tace _”Zaki sauko ne daga inda kika hau wallahi.”_

_”Babu abinda zai sauko dani.”_

Dariya ta sake mata tace _”Ai kuwa d’an uwana zai sauko dake da k’arfin cin tuwo.”_

Maida mata tayi da _”Ke dashi duk baku da aikin yi.”_

_”Ke ma zaki samu aikin yi idan aka d’aura, dan tunanin d’an uwana ma kad’ai ya ishe ki.”_

_”.”_ Shine abinda ta tura mata.

A safiyar aka raba goro wani kamar zaiyi wanka dashi, sam kowa ya goyi da bayan a saka k’ank’anin lokaci, hutu aka saka na babbar sallah da za ayi na yan makaranta wanda duka *sati uku* ne ya rage, ai sai Ummy ta aje maganar aiki gefe ta fara shiga da fita tana gyara yar tilon yarta data rage mata mace, duk abinda ta wa margayiya shi take mata yanzun har da k’ari na sabbin sirrika, ita kanta Hamna wani abun in tasha sai jikinta yayi sanyi, wani in tasha tsikar jikinta ce zata dinga tashi, wani kuwa sai taji jikinta har rawa yake, turaren da take sawa a ruwa wurin wanka har gadonta ya kamu da k’amshin shi ma, ta samu gyaran fata tayi luwai luwai abinta tayi masara shar da ita, kullum kuwa tana sama d’akinta bata ganin ko falon Hajia bare rana, har yanzu kuma basu had’u da jarabun nata ba dan ba d’akin yake zuwa ba, dan danan kuwa sai gashi an gama shirye shiryen sallah an gama.

_Zuma_
Idon zakara_
_Kanunfari_
_Garin rud’i_

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231 232 233 234 235 236 237 238 239 240 241 242 243 244 245Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected