BADAK'ALA COMPLETE HAUSA NOVEL

BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL

Irin dai yanayin d’aya ne da Maryama ita ma ta shiga, k’uri ta mishi da ido tana kallo ba ko k’yabtawa, zufa da hawaye kam har tsere suke wajen fito mata, mutumin da kullum saita zage shi kafin bacci ya d’auke ta? Mutumin data rabu da iyayenta a dalilinshi? Mutumin da mahaifinta ya rasu ba akan idonta ba a sanadiyarshi? Mutumin da yake da babban kaso na duk zunubin da take aikatawa? Uban ‘yarta da kullum take son gani? Wai yau shine a gabanta? Wannan wace irin rana ce? *Fara ko bak’a a gurinta*? Tasan dai a wurin Huda fara ce kam, wannan yanayin da Junaid ya gani a tare da su yasa shi dafa Jibril yace “Ya dai malam? Ko ka santa ne?”

Sakaka ya kalli Junaid ya rasa me ma zai fad’a masa, wannan wane irin tashin hankali ne? Maryama ce tayi k’arfin halin kallon Junaid tana shafe zufa tare da hawayen dan kar ya gani tace “Kamar ya ko ya sanni?”

Murmushi Junaid yayi yace “A’a ranki shi dad’e ayi hak’uri, ni ba wani abu nake nufi ba, kawai dai naga yayi wani iri ne.” Ya k’arashe yana kallon Jibril dake satar kallon Maryama, yana ganin sun kalleshi yayi saurin kallon Huda yana cewa “D’an uwa wannan ce matar ta mu kenan?”

Wani kallon mamaki Junaid ya masa dan yanda muryarsa ta fita zaka iya fahimta tashin hankalin dake cikin sautin, ganin Maryama da Junaid duk kallonshi suke kallon daya kasa fahimta gashi duk ya tsargu, dan haka ya sake kallon Huda ya mata murmushi ya zura mata hannu alamar ta taho yana fad’in “Beby ya sunanki?”

Zuro mishi hannun tayi tana fad’in “Nurul Huda.”

Kusa da shi ya tsayar da ita yana kallon kyakyawar fuskarta mai kama data uwarta, gabanshi har yanzu bai daina fad’uwa, ga wani sabon tashin hankali daya ziyarce shi yanzun, *Nurul Huda*, idan fa ta kasance ‘yata ce? Wannan tunanin ne ya sashi jin kamar zai k’urma ihu, jin zuciyarshi na barazanar tarwatsewa yasa shi kallon Junaid yace “D’an uwa ban makullin motarka zanje nan na dawo, kafin lokacin ka ida kai ma.”

Junaid ne yace “Amma ai ba haka mukayi da kai ba, meyasa zaka tafi ka barni nan?”

Abubuwan da yake ji a kanshi yasa yaji ba ma zai iya mishi magana ba, rufe k’ofar daya fito yayi ya zagaya b’angaren matuk’i, ganin haka ba zai gyarata ba yasa Maryama cikin shak’iyanci tace “Amma d’an uwa ko gaisawa bamuyi ba sai tafiya?”

Tsayawa yayi ya kalleta, wannan idon nata har yanzu dai basu sauyawa ba cewar Jibril, kai tsaye ya mayar da kallonshi ga Huda yace “Ba damuwa ai ba jimawa zanyi ba, wani abu na tuna da shi yanzun nan.”

Murmushi ya ma Huda yace “Nurul Huda ko? Zan dawo yanzu sai muyi hira dake.”

Cike da gatsali Maryama tace “Huda, zanyi magana da tonton d’in ki mijin da zan aura, ki tafi tare da waccen *Abban nanki* kafin mu gama kinji ko.”

Huda da har cikin zuciyarta taji dad’i da yau har mahaifiyarta ta iya nuna mata wani namiji ta kuma kirashi da abbanta, da farin ciki ta zagaya kusan Jibril daya kafe yarinyar da ido, *Abbanta*, ta tabbata dai kenan? Na shiga uku ni Jibril, yanzu wannan ‘yata ce? To ya zanyi da ita? Haka kawai saina nunata a gida gida a matsayin ‘yar wacce nayi wa fyad’e ko me? Junaid ma mamaki Maryama a bashi sosai jin yau tana alak’anta Huda da d’an uwanshi, to me hakan ke nufi? Gamon jini ne ko me? Da k’yar Jibril yayi murmushi ya shiga motar ya zauna, zuro hannayenshi yayi ya d’auki Huda ya ajeta mazaunin mai zaman banza sannan ya rufe, suna kallonsu har sukayi nisa kafin Junaid ya kalleta yace “Abun mamaki.”

Kallonshi tayi da fara’a tace “Me fa?”

Ba tare daya daina kallonta ba yace “Wace irin sa’a Jibril ya zo da ita haka da har kika yarje masa ya tafi da Huda haka? Wace irin sa’a ce haka ke tattare da shi da har kika iya kiranshi da Abban Huda kuma a gabanta? Maryama ko dai da wani abu ne?”

Jin yana neman harbo jirginsu ita kuma ba haka take so ba yasa tace “Ba sa’ar shi bace, taka ce, domin nayi niyyar saurarenka, sannan na shirya fad’a maka abinda ke raina a game da kai, ko da baka zo ba yau ni zan neme ka, ina so ne na fad’a maka na amince zan aure ka, shiyasa ma na so sai Huda tayi nisa da ni sannan na fad’a.”

Tunda ta fara magana yake kallonta cike da jin dad’in abinda take fad’a, da farin ciki yace “Mari, kina nufin kin amince zaki aure ni?”

Gyad’a mishi kyai tayi alamar eh, tafukan hannayenshi yasa ya rufe fuska da su, saida yayi godiya ga Allah kafin ya bud’e ya kalleta yace “Nima maganar dake tafe dani mai girma ce, domin kuwa jiya warhaka muna cikin filin gidanku tare da kakarki muna cin abinci muna hira da ita.”

Waro ido tayi tace “Kakata? A ina kuka ganta? Gidanmu kuma?”

Murmushi ya mata kafin ya kwashe komai ya fad’a mata tun daga labarin da Iklima ta bashi har zuwansu garinsu da kuma abinda ya faru gidansu, kuka ta dinga yi tana ji a ranta lallai son ta yake sosai, sai dai kuma ita har k’asan zuciyarta babu wani son aurenshi a ranta, son da take masa ma ba wani so bane na azo a gani, yanzun haka ta amince ni zata aure shi saboda uban yarta data gani, ko ba komai zata gasa masa aya a hannu, saita rama zalincin daya mata, saita d’and’ana mishi irin *uk’ubar* daya sata ciki shima, abun mamaki saiga Junaid sunyi hira ta fahimtar juna da Maryama, kuma duk abinda yace saita amince ta nuna ta yarda, harda cewa yau zai had’ata da dreban da zai mayar dasu gida ita da Huda, gobe kuma za aje nema mishi aurenta, bata mishi musu ba sai cewa da tayi bari taje tayi sauri su had’a kayansu.

Tunda Jibril ya d’auki hanya ya rasa meke masa dad’i, shi fa daya shigo motar ya so ya samu damar da zaiyi k’wararan ihu ne da zaisa yaji sakayau , amma kuma an had’a shi da Huda, tsayawa kawai yayi bakin titi yana kallonta tana ta waige waige a cikin motar da tab’a abubuwa alamar dai kamar shigarta ta farko kenan, a zuciyarshi yake ayyana data hanyar data dace aka sameki da wannan motar zata iya zama taki wacce dreba ma na musamman gareki da zai dinga tuk’a ki, ganin kallon da yake mata yasa ta zauna tsaf ta daina tab’a komai tsoro ya bayyana tare da ita, fuskarshi ba yabo ba fallasa yace “Kina karatu?”

A hankali ta kalleshi tace “Eh Abba ina yi.”

Wani kallon ban gane *Abba* ba? Ya mata kafin yace “Maryama mamanki ce?”

“Eh Abba.” Ta sake fad’a d’orawa yayi da “Ina Abbanki yake? Mamanki ta tab’a nuna miki shi?”

Cikin sanyi jiki Huda ta girgiza kai tace “A’a, nima ban sani ba, amma dai yaran unguwarmu suna ce min shegiya ce ni ‘yar karuwa, kuma Mamana kullum sai tayi fad’a da mutanen gidanmu idan suka ce min shegiya ce ni ko ragon suna ba’a yanka min ba, kuma idan na tambayi Mamana waye Abbana saita dinga hushi tana min tsawa da fad’a tace na tashi na bata wuri.”

Rintse ido Jibril yayi saboda jin hawaye sun cika idonshi har suna neman zubo mishi, *ragon suna*? Shine abinda yafi tsaya mishi, ‘yar dana haifa a cikina ko bata hanyar aure bane ace ba’a yanka mata rago ba, ya ilahi, shine abinda ya fad’a k’asa k’asa, d’an bud’a idonshi yayi ya juya inda Huda take, sai gani yayi tana ta goge hawaye da bayan hannayenta wasu na biyar wasu kam, gyara zamanshi yayi ya kamo hannunta ta mik’e tsaye ya d’auke ta ya zaunar da ita kan cinyoyinshi ya fara share mata hawayen yana fad’in “Yi hak’uri kinji ‘yata, ba dai yana suna tsokanarki ba? To daga yau ba zasu sake ba saboda Abbanki ya dawo, kuma maganar rago ma ki fad’a min me kike so a yanka miki, kama daga rak’umi, saniya, da kuma raguna, ke da ana yanka zaki da su gwiwa ma ni zan yanka miki.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231 232 233 234 235 236 237 238 239 240 241 242 243 244 245Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected