BADAK'ALA COMPLETE HAUSA NOVEL

BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL

Cike da k’aguwa yace “Hajia ba komai fa, dan Allah abar maganar.”

Juyawa yayi da nufin komawa d’akin shi yace “Ni zan shiga ciki.” Da kallo kawai ta bishi har ya fita daga falon, nan kowa ma ya nufi na shi d’aki dan huta gajiya.

Lieutenant na shiga wanka yayi ya sake sabon shiri ya fito, kai tsaye wajen aje motoci ya nufa wanda ke sank’ame da motoci kamar na siyarwa, dan akwai motoci a wurin kusan guda bakwai, a hankan ma dan babu ta colonel sannan Jamil ma moto ne da shi, haka su Hamna ma duk da kuwa akwai halin da zasu hau motar suma, katari akayi Zeituna na share wurin saboda ‘ya’yan bishiyoyin dake zuba suna yawon b’ata wurin, duk’e take kusa da motarshi da tsintsiya tana shararta da kuzari kamar yanda ta saba, duk da ba motsin mutum taji ba amma k’amshin turarenshi ya sanar da ita yana tahowa, tana d’agowa ashe ma harya k’araso kusa da ita zai bud’a motarshi, idonsu ne suka had’u wanda hakan ya haifar mata da shiga wani yanayi na shauk’i, shi kuma yana kallonta kai tsaye yayi k’asa da idonshi wanda cikin akasi suka sauka kan k’irjin dake pam-pam a gabanta kamar mai jaririn ciki, gashi dai budurwa har budurwa amma datti ya b’oye hallitunta, yatsina fuska yayi saboda kallon tsaf daya mata, hijabinta kalar ruwan toka ne amma tsabar daud’a har yayi wani duhu, k’afafun nan nata fari k’al da su kamar na mai d’aukar kanwa amma fa daga ciki bak’i k’irin yake, kallon fuskarta ya sakeyi wacce ke fitar da zufa daga goshinta zuwa saman hanci, gashi zufar har cikin kanta zufa yake har tana gangarowa a fuskar, da sauri ya d’auke idonshi ya mayar kan mota ya bud’e zai shiga, cikin ladabi ta sunkuya tace “Abban Ammar a dawo lafiya, Allah ya tsare.”

Fuskarshi ba yabo ba fallasa ya amsa da “Allah yasa.”

Tayar da motar yayi tana kallonshi ta kasa ci gaba da aikinta har yayi baya baya ya saita motar daidai k’ofar fita, mai gadi ne ya bud’e masa ya fita duk tana kallo kafin ta ci gaba da shararta.

Ashe duk kallon nan da take masa yana hangenta ta madubin motar, saida ya fita yake tunanin wannan kallon duk na miye haka? Ita bata san ba kowa ke son yawon kallo ba? K’aramin tsaki yayi tare da sakin tunanin Zeituna, wayarshi ya d’auka da nufin kiran Ummyn yan biyu saboda ta kira shi yana wanka, kuma yasan ta kira ne taji sun iso lafiya, yana dannawa lambar ta ta ido sai kawai hoton Zeituna da k’irjin ta ya dawo mishi a ido, muryar Ummy ce ta dawo da shi hayyacinshi ya amsa mata sallamar data masa.

*Bayan fitar Zeituna*

Kawu Mamu na zaune k’ofar gida da redionshi yana saurare wannan mutumin ya zo ya paka mota, fitowa yayi cikin wata arniyar shadda wacce tasa kawu Mamu sanin tabbas babban mai kud’i ne, gaisawa sukayi yace mishi “Baba dama wurinka na zo.”

Saida ya nuna kanshi yace “Wuri na kuma Alhaji, Allah yasa dai lafiya ko ba wani laifin mukayi ba.”

Murmushi yayi yace “Babu laifin daka aikata Baba, alkairi ne ke tafe dani.”

Murmushi ya saki ya mishi izini ya zauna kan tabarmar kusa da shi, ya mik’e yace “Bara na kawo maka ruwa Alhaji.”

Da sauri ya katse shi da cewa “A’a Baba ka barshi, ai babu k’ishin ruwa a tare dani.”

Zaune yayi suka sake gaisawa kafin yace “Baba ni dai sunana *Jano*, kuma ni d’an kasuwa ne, a garin nan nake da zama, daren jiya ina kan hanyata ta zuwa gida a kan motona saina had’u da wata budurwa, sanin ba zata tsaya ta sauraren ni ba yasa bai tsayar da ita ba, amma a hankali na dinga biyo bayanta naga ta shiga gidan nan.”

Ya fad’a yana nuna gidan da suke fuskarta ya ci gaba da cewa “To a gaskiya yarinyar ta kwanta min, ina sonta idan har ka amince da hakan.”

Kallonshi kawu Mamu yayi yace “Janna ka ke ko?”

Murmushi yayi yace “A’a Jano ne Baba.”

Sake kallonshi yayi yace “Amma dai sunan nan bana musulmi bane ko.”

Ba fargaba yace “Eh Baba, ni ba musulmi bane, jimawa a cikin musulmi da kuma zama tare da hausawa yasa ba’a iya tantance gaskiyar waye ni, amma ni asalina ma d’an bagwari ne.”

Gyara zama yayi yace “Wannan ai ba wani abu bane, gaka ‘yarmu ka ce kana so kuma mun baka har abada.”

Kallonshi Jano yayi yace “A’a Baba, bana har abada nake buk’atar ta ba, zan fad’a maka gaskiyar abinda nake so daga jikin yarinyar.”

_Ba aure ya kawoka ba dama?_

*Mu had’e a pegi (page) na gaba insha Allah.*
29/05/2020 à 16:33 – Ummulkhairi: ‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍
*SANIN MASOYI*
_(sai Allah)_
*BAYA DA K’URA*
‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍

*NA*

_SAMIRA HAROUNA_

*Litattafan marubuciyar*

*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D’AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD’I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K’ADDARARMU_
*8* _K’ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k’ura)…_
*14* _BADAK’ALA…_

*SADAUKARWA GA*

_*MASOYA NA*_

_KUNA CIKIN RAINA_

*Raheenat M. Abbakar*
_(My Heenat)_
*Jameela AHK*
_(My Meelat)_
*Ma chérie Hakeema*
_(Mom Teema)_
*Momyn Dady*
*Maman Labyb*
*My Hawwer*
*Aunty Hawwer*
*Ummi&Ummi*
_(Lil sister’s)_
*Nazeefa*
_(My k’awa)_
*Sis Chappa*

*TAURARIN NIGER*
“`(Tsintsiya mad’aurinki d’aya)“`

_Bismillahir rahamanir rahim_

_5_

Bud’ar bakin tsohon sarki cewa yayi “Allah da na shi iko, Imran ai dama ya kamata ka k’ara auren ko dan matsayin da kake da shi, sai dai kuma wani hanzari ba gudu ba.”

Cikin nutsuwa Imran ke kallonshi yana kuma sauraro, d’orawa yayi da “Shekarun baya da suka shud’e nayi magana daga ni sai liman akan ina son ya baka auren ‘yarsa *Saratu*, amma lokacin daka kawo wacce kake so kuma za’a maka nad’i sai kawai muka bar maganar, a k’a’idata kai ka sani bana sab’a maganata, dan haka har yanzu nake son cika wannan alk’awarin dana yi tsakani na da liman wanda Allah ne shaida.”

Sunkuyar da kai Imran yayi yana jiran umarnin mahaifin na shi, ci gaba yayi da fad’in “Ka cika min burin nan nawa Imarn ta hanyar had’a zuri’a data liman, tun yaya na (mahaifin Sameera) yana mulki suke tare da shi, amintaccenshi ne, ni ma kuma banda amintacce sama da shi, mutum ne mai rik’on sirri da amana, baya duba matsayinka ko kuma muk’aminka, idan har kayi ba daidai ba take zai sanar da kai ba tare da shakku ba, babu tsoro ko shakkar wani mahaluki a tare da shi inba ubangijin daya halliceshi ba, yaranshi sun samu tarbiya wacce nake da yak’inin zakayi alfahari da auren tsatsonsa.”

Cike da gamsuwa da bayanin mahaifinshi ya d’ago yace “Mahaifi na wannan hallayar liman ce, dan haka a shirye nake da na bi umarninka.”

Cikin jin dad’i yayi murmushi yace “Alhamdulillah, ita Saratu yanzu tana gidan mijinta har da ma yaranta, amma akwai k’anwarta wacce akayi wa saukar hardar Qur’ani mai girma satin daya wuce, a lokacin kana k’asar *Paris* shiyasa ma baka samu halartar taron ba, sunan yarinyar *Safiyya*, na yarda da tarbiyarta saboda nasan mahaifiyarta, idan har ka amince da zab’in nan to zanyi magana da liman, amma ka sani, kai ba k’aramin mutum bane da za’a tsaya b’ata lokaci ba.”

Cikin girmamawa yace “Na amince mahaifina, duk abinda ka zab’a min yana zama alkairi a gare ni, zanyi biyayya ga wannan auren na kuma rik’e yarinyar da daraja fiye da yanda zan kula da kai na.”

Da haka suka gama tattaunawarsu ya taso ya fito, fadawa biyun ne suka rufa mishi baya izuwa komawa b’angaren shi, yana zuwa ya shiga suka sake tsare bakin k’ofar, d’aya bafaden ne ya kalli d’an uwanshi yace “Zan d’an kewaya, ina zuwa yanzun nan.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231 232 233 234 235 236 237 238 239 240 241 242 243 244 245Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected