BADAK'ALA COMPLETE HAUSA NOVEL

BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL

Wannan Izzar ta ta da kwarjini yasa wasu daga cikin matan ma suka manta da matsayinsu suka fara gaisheta, tabbas suna jin muryarta na amsawa amma basu ganin labb’anta na motsawa, nan dai *Hassana* (yar uwar Husseina) ta umarci a shigo da kayan, mace uku ce ta mik’e suka d’auko akwatinan masu bakwai bakwai a ciki har kala uku, da kuma d’aurin goro har guda biyu, har gaban Hajia suka diresu tana kallon akwatinan, wani matashin saurayi ne ya shigo da wani dallelen moton har falon ya aje shi inda babu mutane a ledarshi, Hassana ce ta kalli Hajia tace “To alhamdulillah, kayan Jibril ne muka kawo na Jamila, ga akwatina, ga moton da yace a kawowa amaryarsa dan ci gaba da zuwa makaranta, sai kuma…”

Ta fad’a tana saka hannu cikin jakarta ta fito da kud’i ta d’ora saman d’aya daga cikin akwatinan tace “Sai wannan, million biyu ne, sadakinta kuma sai ranar d’aurin aure.”

Ko ba komai bajintar tasu ta birge Hajia, amma saita dake ta kalli Hassana wacce ita ma ba shiri suke ba tace “Ba laifi, amma yasan da cewa buzuwa zai aura ta b’angare na, ba zai birge ni ba har sai yayiduk wani abinda akeyi idan za’a auri buzuwa.”

Wani murmushin gefen labb’a Hassana tayi tace “Wannan ba matsala bane, sai dai zaifi kyau ki fad’a mana yanda al’adun suke dan mu sani, duk da shima dai akwai abinda dole amaryar tayi kasancewarshi babarbare.”

Wata hamshak’iyar dariya Hajia ta saki wacce ni dai tunda na fara rubutun nan banji inda tayi dariya ba, kallon Hassana tayi tace “Babarbare? Ta ina? B’angaren uwa?”

Murmushi tayi kafin ta kawar da kanta tace “Ba zan tsawwala muku ba, ina so kawai naga anyi guitar (jita) a daren d’aurin aurensu, za ayi shiga irinta buzaye ko kuwa mutum baya so, sannan ba wai Jibril ba kad’ai, har sauran angayen dole kowane ya kawo min kyautar rak’umi wanda ya amsa sunan rak’umi bayan tarewarsu da matansu, hakan kuwa shine zai sake nuna darajar yaran da kuma d’aga martabarsu.”

Wani kallo Husseina dake gefe ta mata tace “Amma ai na d’auka wannan al’adar ana cikata ne idan aka samu yarinyar da mutuncinta?”

Murmushi Hajia tayi ta kalleta tace “Kina tsammanin duk yanda nake saka ido kan ‘ya’ya da jikokina za’a iya samunsu da rashin kamun kai, ai wannan ba abu bane da za’a same shi a zuri’ata ba.”

Murmushi Husseina tayi ta sassauta muryarta tace “Ke ina taki kyautar?”

Hassana ce ta kalleta sannan ta kalli Hajia tace “Ba damuwa, zamuyi duk abinda kika ce, ai Jamila da Jibril yan uwan juna ne, ko kyauta zai iya siya mata jajayen rak’uma bare kuma ya karb’i budurcinta.”

Suna kammalawa sukayi sallama inda Hajia ta bud’a jakar hannunta k’arama ta bawa Sa’ada kud’i har jaka d’ari biyu tace ta basu tukuici kamar yanda akeyi, su kansu k’in amsar tukuicin sukayi suka ce ai yayi yawa, da k’yar Sa’ada ta matsa musu suka karb’a suka bar gidan kowa da abun fad’a a baki.

Suna tafiya Ummy ta zarce b’angaren samarin ta shiga da sallama, Amar Jibril da Junaid da kuma Ammar ta samu zaune a falon, gaishe ta sukayi dukansu banda Ammar da hankalinshi ke kan tv, zaune tayi tana kallon Jibril tace “Bak’i har sun tafi, munga kaya masha Allah, Allah ya sanya alkairi?”

Da murmushi ya amsa da “Ameen aunty.”

Kallon Amar tayi tace “Saura ku, na ku sai yaushe?”

Amar ne yace “Ummy gobe mu ma zamu kawo.”

Dukansu ta kalla tace “Sai kun shirya da kyau, dan Hajia tace za’a gudanar da wasu daga cikin al’adunsu na buzaye, musamman ma ku.”

Ta fada da nuna su Ammar ta ci gaba da cewa “Tunda kunga ni kaina buzuwa ce, dan haka dole zata fi karkata abun ta b’angaren ku.”

Amar ne yace “Ba damuwa bane Ummy, matsalar ni dai wannan k’aton rawanin ne bana tunanin zan iya d’aurawa.”

Dariya tayi tace “Da kaina zan d’aura maka, tunda saika d’aura shine zaka fito a buzun.”

Mik’ewa tayi tace “Saida safenku, ku kwanta da wuri kunsan gobe ne fa auren ubanku.”

Sai lokacin Ammar ya kalleta ta wutsiyar ido ya kuma d’auke kan shi, fita tayi inda Ammar ya mik’e zai shiga d’aki, Amar ne yace “Ka tabbatar ka tashi da wuri fa, dan Abba yace ni da kai ne zamu take masa baya muna karb’ar bak’i.”

Juyowa yayi ya kalleshi k’ala baice ba ya shige ciki ya barsu, Jibril ne ya gyara zama yace “Yau fa mutanen sun motsa.”

Murmushi Amar yayi yace “Allah dai ya kyauta.”

“Ameen.” Cewar Junaid.

A nesa da k’ofar gidan ya paka mota ya tsaya inda kawu Mamu ya shiga dan kiran Zeituna, ba laifi gidan ya kaure da cacaniya alamar dai biki za ayi gobe, tuni dama ansa Zeituna ta shirya cikin wani kalar d’inki na atamfa wanda ba dan ta sanya hijab ba sai a mata dariya, dan kaf dangin babu mai wayewa ta zamani haka ita ma, dan ba k’awaye gareta ba bare tasan abu mai kyau ko marar kyau, lalle da kitso ma tayi sa’a a unguwar aka samu wanda suka iya suka mata, wata doguwar jagira aka ja mata tare da shafa mata jan jan-baki, fitowa tayi tana hard’e k’afafu saboda tsoron abinda zata tarar, tana isa ta inda yake ta tsaya kanta k’asa, tunda ta taho lieutenant ke hangenta yana raya abubuwa da dama, tana tsayawa ya sauke gilashin murya a d’an kausashe yace “Sai ki shigo ko, kinga ni ba yaro bane bare na fito na tsaya kowa na kallo na.”

Gabanta ne ya tsananta fad’uwa ta zagaya ta kama k’ofar ta shiga, da k’yar ta janyo k’ofar ta rufe ta sake mayar da kanta k’asa tana wasa da yatsunta daga cikin hijabi, kamar yace ke ta zuba a guje take ji, wai yau gata a mota da Abban Ammar ana shirin d’aura musu aure gobe, jin shirun ne yasa ta tsargu ba tare data d’ago ba tace “Ina wuni.”

Ajiyar zuciya ya sauke dan dama yana jiran tayi magana ne, kallonta yayi yace “Lafiya lau, ya hidima?”

Shiru tayi kamar ba taji ba, kallonta yayi kamar ya shareta sai kuma yace “Tun yaushe kike so na? Kuma kina ganin hukuncin da Alhaji ya yanke bai tauyeki ba? Har zuciyarki zaki iya zama da ni?”

Zeituna dake jin tambayoyinshi kamar saukar guduma a kanta tasan ba zata iya amsawa ba, sai kawai ta fashe da kuka tasa hannu ta toshe baki, sororo yayi yana kallonta da mamakin kukan na meye? Wani abu ya fad’a daya b’ata mata rai? Ko kuma sangarta ce tana so ya fara rawar k’afa yana rarrashinta? Ai ko abinda ba zai yiwu ba kenan, fuska ba annuri yace “Meye na kuka kuma? Na fad’i wani abu ne? Ko kuma dai takuraki akayi?”

Girgiza kai tayi hakan yasa yace “Shin akwai wani abu da kike buk’ata ne?”

Nan ma girgiza kai tayi hakan yasa ya kawar da kansa yace “To ni zan tafi, saida safe ko?”

Ji tayi wani kukan ya taho mata wanda yasa tayi saurin bud’e k’ofar ta fito, rufewa tayi ta taka da hanzari ta tunkarin gidan, saida ya ga shigarta kad’ai ya ja d’an k’aramin tsaki ya tayar da motar ya bar unguwar.

*11: 49* na dare Ammar ya mik’e zaune tsakiyar gadonshi, tsaki yayi tare da kama hantsar wandonshi yace “Shikenan mutum idan baida aure baya da nutsuwa har abada.”

Sakin wandon yayi ya sauko daga kan gadon, ban d’aki ya shiga ba wani jimawa ya fito, rigar wandon baccinshi ya d’auka fara ya saka ya fito, duk wani kwanon abinci daya gani a falon nasu saida ya duba amma babu abinci, fridge ya duba nan ma sai lemu kawai da ruwa, wani tsakin ya kuma ja tare da nufa k’ofar fita, acan bayan gida yake jin hayaniyar matan suna aiki, kai tsaye falon Hajia ya shiga wanda ke bud’e har yanzu saboda matan basu shiga ba bare a rufe, madafa ya wuce da niyyar shiga sai yaji k’ofar a rufe, baiyi mamaki ba dan dama idan dare yayi ana rufe k’ofofin ko ina, dawowa yayi da niyyar fita kawai dan ba zai iya jura jin bak’ar magana daga bakin kowa ba, ta kusurwar d’akin Alhaji yabi zai wuce sai yaji motsi, d’an murmushi yayi ya matso ya kama k’ofar zai bud’e sai yaji muryar Alhaji na magana da alama addu’a yake yana fad’in ” *Allah kaine Allah, Allah kai kace mu rok’eka zaka amsa mana, gashi ina rok’onka kaina k’asa, Allah ka kare min zuri’ata da ahalina, Allah ka karesu daga aikata alfasha, Allah ka kare min ‘ya’ya da jikokina daga sharrin zina, Allah ka kub’utar dasu da ikonka, Allah kai shaidane ban tab’a aikata zina ba, ban tab’a k’etara iyakar wani ba ta hanyar cin zarafin iyalinshi, amma ya zama dole na rok’awa iyalina kariya saboda sharrin zamani, sannan iyali suna kimtsuwa ne idan ka zab’ar musu uwa ta gari, nayi kuskure tun farko dana amince da auren Zeeya’atu, duk da a waccen lokacin ina da k’arancin ilimin addini ban kuma farga ba saida muka hayayyafa, Allah ina rok’onka ka kare min zuri’ata kada zunubin zina da mahaifiya ko kakarsu ta aikata a lokacin k’uruciyarta ya shafesu, Allah ka nesanta su da laifin zubar da cikin da mahaifiya kuma kakarsu tayi kar ma ya shafesu daidai da k’wayar zarra, Allah ka sani baiwar nan taka har yanzu bata neman shiriya daga waccen laifin, kullum tsanar mazinata take k’arawa a zuciyarta saboda tasan muninta, Allah ka shiryeta dan tsarkin mulkinka, Allah ka farkar da ita ta gane kurenta na baya ta buba gareshi, astagfirullah, astagfirullah, astagfirullah ya Allah.*”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231 232 233 234 235 236 237 238 239 240 241 242 243 244 245Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected