BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL
Tintsirewa tayi da dariya abinda ya k’ara bashi haushi kenan, da gudu ta nufi falo inda tasan Ammie na nan, da k’arfi ta shiga falon tana dariya tana juyawa taga ko ya taho, shi kuma a sukwane ya taho yana kawowa falon ya fara tafiya a hankali, Khalifa na ganinsu yace “Yeah, anzo gurin.”
Duk da kujerar da Ammie ke zaune ta zaman mutum d’aya ce amma bai hana Sameera zaune a k’afafun Ammie ba ta d’ora kanta a k’irji kamar wata beby tana fad’in “Ammie kin ganshi ko.”
Ammie kuma dan taya b’era b’ari saida ta fara shafa bayanta kafin ta harari Abbas dake kallon Sameera tace “Kai kuma meye haka da sanyin safiya zaka taso min ‘ya gaba da gudu? Wallahi fa bana son abin nan da kake min, yarinya ko babu laifin bak’i bana fari saika dinga cutar min ‘ya.”
Abbas kallon ikon Allah yake, hakan yasa Sameera yi mishi gwalo tana dariya, Abba ne ya kallesu yace “Wallahi wata rana saita karya miki k’afafu, kuma a k’arshe yaro na za’a bari da kashin kud’i wajen neman magani.”
Ammie ce tace “To idan bai kashe na shi kud’in ba ai muma muna da kud’in kashewar, sannan shi kud’i zai kashe auta ta kuma jinyata zatayi.”
Saida Sameera ta sake cukuikuyeta tace “K’warai kuwa Ammie na.”
Wata jar harara Abba ya jefa mata wacce tasa ta mik’ewa daga k’afafun Ammie bata shirya ba, dan har yanzu akwai wutar bala’i a jikin mahaifinta wacce ta ninka ta ta sau dubu, tsaf ta fahimci me hararan daya mata ke nufi, shiyasa ma ta mik’e tayi shiru, juyawa Abbas yayi zai bar falon yana fad’in “Allah ya shiryaki.”
Muryar Abba ce ta dakatar dashi da yaji yace “Liman kuma? A wannan lokacin.”
Juyowa yayi ya ga Abba ya mik’e ya nufi k’ofar fita yana d’aukar kiran da liman ya mishi, bayan sun gaisa ne Abbas yayi saurin tambayar lafiya? Dan haka kawai ba zai kirashi ba a wannan lokacin, cike da muryar jimami liman yace “Yallab’ai sai dai hak’uri, kamar yanda muka sani ne kowane mai rai lokacinshi yake jira, to a daren jiya Allahn daya bamu takawa ya fimu son shi ya kuma karb’i abinshi, sai hak’uri kawai.”
Duk da Abba bai zubar da hawaye ba, domin kuwa mutuwar mahaifiyarsu da kuma ta mahaifiyar Sameera *(Khadija)* ne kad’ai ya zubar da hawaye, amma hakan ya girgiza shi sosai, cikin sanyi jiki da maimaita kalmar inna lillahi wa’inna ilaihi raju’un ya shigo falon, suna ta hayaniyarsu, wajen Ammie ya nufa inda Abbas ya bi bayanshi ya tsaya saboda ganin yanayinshi, saida ya kalli Sameera da Abbas da Ammie kafin yace “Ku shirya, tafiya basraba ya kama mu yanzun nan.”
Sameera da gabanta ya fad’i ne tace ” Abba, lafiya? Meya faru a basraba?”
Ko kallonta baiyi ba dan haka Ammie ta mik’e tace “Yallab’ai lafiya? Meya faru ne? Ko wani ne ya rasu?”
A hankali ya jinjina mata kai alamar eh, Abbas ne yayi saurin cewa “Abba waya rasu?”
Saida ya had’e yawun da suka bushe mishi a mak’oshi kafin ya kalleshi, kamar ba zaiyi magana ba saboda yanda ya kafeshi da ido, can kuma sai yace “D’an uwa na, d’an uwana da shi kad’ai ya rage min, *Musayyib* ne ya rasu daren jiya.”
Yana fad’a ya juya a sukwane ya bar falon alamar yana son b’oye yanayinshi, Sameera da ko da aka fad’i haka ta tuna da kiran daya mata jiya bayan sallah isha’i yana sake mata nasiha data dinga hak’uri da rayuwa, bayan haka har suka tab’a hira yana fad’a mata ya nemawa d’an uwanta auren ‘yar liman, sun jima suna waya amma yanzu ace babu shi, neman durk’ushewa tayi hakan yasa Abbas saurin tallabota ya rumgume a jikinshi, tana jinta a k’irjin shi saita fashe da kuka sosai tana cakumar rigarshi tana k’ara sautin kukan, Ammie da ba zata iya hanata kuka a wannan lokacin ba dan tasan yanda suke da kawunta, soyayyar da yake nuna mata ko mahaifinta baya nuna mata ita, fita tayi ita ma dan suyi shirin tafiyar, yaran na ganin haka suka mik’e kowa ya nufi d’akin shi zuciya cunkushe saboda ganin mahaifiyarsu na kuka, Raihan saida ta rik’o hannun Sameera cikin rawar murya tace “Dan Allah Ammie kiyi shiru ki daina kuka, takawa addu’arki yake buk’ata yanzun, shine soyayyar da zaki nuna masa.”
D’akinta ta haura ita ma sai Abbas daya nufi da Sameera b’angaren shi yana rarrashi, ita kuma sai fad’a masa take jiya fa ya kirata sun jima suna magana, yanzu ace wai ya rasu, a ciwon komai da komai, yana shiga d’akin shi ya zaunar da ita bakin gado ya d’auki wayarshi, Bashir ya kira ya fad’a masa, Bashir da a lokacin ke zaune falo yana sauraren hayaniyar yara Imranatu kuma da Ma’awa da ke ta k’ok’arin shirya abun kari, kallonta yayi baiwar Allah tana cikin farin ciki, taya zai fara fad’a mata rasuwar mahaifinta, ajiyar zuciya ya sauke ya mik’e ya tunkareta, hannunta ya kama har zuwa d’akin kwanansu kafin ya fara mata da nasiha sannan ya rarrasheta, yana fad’a mata ita ma ta fashe da kuka ta fad’a saman k’afafun shi, haka dai ya lallab’a ya taimaka mata ta shirya dan Abbas yace yanzu zasu tafi, wajensu Bilkis da Naseer ma haka abun yake, inda Abbas bayan ya gama waya dasu ya kira captain Ali ya sanar dashi zasu tafi basraba.
Cikin k’ank’anin lokaci kowa ya gama shirinsa ya fito, Sameera kitchen ta nufa ta samu Razeena ta fad’a mata su kula da gida sosai, sannan tace wa Harira ta kula da yaran, a wannan lokacin da Sameera a cikin nutsuwa take data fahimci kallon da Harira ta mata na kin ma raina min hankali ne, haka suka fito sun kuma samu driver har ya zo d’aukar yaran zuwa islamiyya, saida suka ga tafiyar yaran kafin suma Abbas ya jasu a d’aya motar kuma Naseer ne, suna isa airport captain ya riga daya iso, ba b’ata lokaci suka shiga kowa ya kimtsa suka d’aga sai masarautar basraba.
Da saukarsu mota uku ce sarki Imran ya turo dan d’aukar su, masha Allah, unguwar cike take da mutane da ababen hawansu, rasuwa ce data jijjiga masauratar dama kewayenta gaba d’aya, jimamin da mutanen gidan ke ciki yasa tsohon sarki mahaifin Sameera da ma ita kanta Sameera da kuma yar sarki mai mutuwa Imranatu basu samu gaisuwa da irin wasasun da ake ba idan sun zo, k’arfe *08:30* motoci sukayi gudan layi mai tsayin gaske zuwa mak’abarta.
*Allah ka mana kyakyawan k’arshe.*
*Muje da sauri*: Abba ne ya bayar da umarnin ayi addu’ar uku har ta arba’in ma, domin kuwa irin mutanen da suka halarci jana’izar bai kamata ace sai sun sake dawowa ba, dan har masarautun dake kewayensu ma sun hallara, take aka had’a akayi addu’ar amma hakan baisa jama’a barin gidan sarautar ba, kamar da wasa sai gashi har anyi *kwana biyu* da rasuwar sarki mai murabus, a wannan kwanakin kuma uwar d’aki hankalinta ya tashi sosai, tunaninta ya karkata kan wane irin banzan mataki ne waziri ya d’auka akan mijinta? Me yasa bai fad’a mata irin wannan matakin zai d’auka ba? Da tayi gaggawar dakatar da shi, har yanzu tana so ta keb’e dashi dan suyi magana, amma rashin gaskiya yasa duk wani motsinta sai taga kamar wani yana kallonta, dole ta hak’ura da tunanin idan anyi uku kowa ya watse zata neme shi.
*Yau kwana uku*, Sameera dama jiya gidansu kawu Bakura ta kwana tare da mijinta, hakan yasa yanzun sukayi sammakon shigowa masarautar dan shirya komawa, tun farfajiyar gida bayi ke durk’usawa suna gaisheta tana amsawa, ita da Abbas b’angaren uwar d’aki suka nufa dan tunaninsu kowa na can, amma suna daf da kaiwa sai jakadiyar uwar d’aki *Lami* ta taho a sukwane ta sunkuya tana wasata tare da fad’a mata ana mata magana a falon mai rasuwa takawa, juya akalarsu sukayi zuwa can, suna shiga tare da sallama suka samu taron jama’a, uwar d’aki, mahaifinta da mahaifiyar Abbas, waziri da matarshi ga kuma liman da sarki Imran, gefe ma dai duk su Naseer ne da su Imranatu, wuri suka samu suka zauna kusa da juna, Abba ne yayi gyaran murya ya kalli liman yace “Liman jiya munyi wata magana da kai akan auren Imran da kuma yar wajenka, hakane?”