BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL
Shima cikin hadd’ad’ar fuskarshi yace ” Abba, wallahi tallahi saina raka ka ko baka so, kawai muje.”
Gyara tsayuwa lieutenant yayi yana kallonshi da mamaki, hannunshi ya kama ya nufi dashi babban falon yana fad’in “Muje haba na sadaka da ita, ina fatan dai ba sai ka tsaya wani ja musu kunne ba? Tunda ai uwarmu ba hayaniya gareta ba, kawai kayi tazarce.”
Dariyar da Alhaji ya tintsire da ita ne ta dawo da kallon lieutenant kanshi, ba tare daya tsagaita da dariyar ba Alhaji yace “Kawai kuje babba, koba komai shi d’in babban d’an ka ne kamar yanda ya fad’a.”
Nuna Ammar yayi da yatsa yace “Alhaji da wannan mahaukacin? Haba dai.”
Sai lokacin ya daina dariyar yace “Kuje kawai ba komai.”
K’iiiii Ammar yaja hannunshi har cikin falon, bai kuma yi alamar tsayawa ba har suka tunkari d’akin Zeituna, suna kaiwa bakin k’ofar babu wani tsayawa kawai ya kama murfin k’ofar zai bud’a, da sauri lieutenant ya jawoshi baya yana fad’in “Wai kai wane irin mahaukaci ne dan Allah? Haka zaka shigar mata d’aki babu k’wank’wasa k’ofa ko sallama? Kasan a wane yanayi zaka sameta?”
Wata shegiyar dariya yayi yace “Ikon Allah, Babanmu tun kafin ka shiga cikin? Ni ko a tunani na dai amarya indai budurwa ce ai yanzu za’a sameta zaune ne akan gado, akan gadon ma a tsakiyarshi.”
Tsaki lieutenant yayi ya k’wank’wasa k’ofar d’akin yana hararan Ammar dake kallonshi ido cikin ido, murmushin zaka shiga hankalinka Ammar ya mishi sanda ya bud’a d’akin ya shiga, bin bayanshi yayi ba tare da yayi sallama ba kamar wanda baisan mahimmancinta ba.
Suna shiga ba b’ata lokaci ya samu kujerardake gaban madubi ya zauna, tsaf ya k’arewa d’akin kallo tare da k’urawa Zeituna ido wacce taja kallabin rigarta ta rufe fuska, ganin kallon da yake mata gashi baida niyyar fita baya so ya mishi b’aram-b’arama yasa yayi gyaran murya, a hankali cike da k’asaita ya juyo ya kalli lieutenant d’in sannan ya kalli Zeituna, ledar dake hannunshi ya aje mata gabanta yace “Amm…Zeituna ko? To ga kazarki.”
Wani kallo lieutenant ya mishi amma shi ko kulashi baiyi ba sai kallon Zeituna daya sake yi a nutse ya d’an tab’e baki yace “To wai ke da wannan rigar aka kawoki ne? Meyasa baki saka leshe ko chadda ba? Ba’a miki d’inki bane?”
Wurk’il wurk’il Zeituna tayi da ido a cikin kallabinta, duk da Ammar ko ma tace mazan gidan ba mazauna gida bane, amma dai tasan Ammar baud’add’en mutum ne, lieutenant kuma kallonshi yayi rai a b’ace yace “Malam nagode da rakiyar da ka min, zaka iya tafiya ko?”
Gira ya d’aga tare da jinjina kai ya mik’e tsaye ya kalleta yace “Amaryar Abba, nasan dai kinsan mahaifiyarmu kuma kinsan wacece ita, ina fatan kafin ki shigo gidan nan kin tsarkake zuciyarki, dan akasin haka ba zai mana kyau ba mu duka, domin kuwa mahaifiyata ita ce komai nawa, zan iya yin komai akan ta duk wanda yace zai b’ata mata, fatan za’a kiyaye saimu zauna lafiya.”
Kallon lieutenant yayi yace “Abba, Allah yasa auren nan daka k’ara ba zai zama silar da za ayi sanadiyar zubar hawayen Ummyna ba, dan gaskiya ba zan juri haka ba, saida safe Abba na.”
Yana gama fad’a yasa kai ya bar d’akin, lieutenant kam kasa motsawa yayi kafin daga bisani ya kalleta yace “…
*Alhamdulillah*
09/09/2020 à 17:58 – Ummulkhairi: ❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️
*BADAK’ALA*
❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️
*Labarin Gaske*
*NA*
_SAMIRA HAROUNA_
*Litattafan marubuciyar*
*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D’AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD’I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K’ADDARARMU_
*8* _K’ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k’ura)…_
*14* _BADAK’ALA…_
*SADAUKARWA GA*
_*AHALI NA*_
*TAURARIN NIGER*
“`(Tsintsiya mad’aurinki d’aya)“`
_Bismillahir rahamanir rahim_
_29_
“Tashi muje wajen uwarsu Ammar ko.”
Hawayen da take wanda baisan dasu bane ta shiga gogewa, shiru yayi yana kallonta yana mamakinta, jin shiru ita ma yasa ta fara d’aga sautin kukanta saboda ita dai abun ya fara bata tsoro, bata gama gamsuwa da cewa ita matar lieutenant bace aka samu matsala tsakanin Hamna da Amna, yanzu kuma ga kashedin da Ammar ya mata wanda yake d’a ne ga mijinta, ita kam sai yanzu ta fara hangowa kanta uk’ubar data jefa kanta ta yarda da auren Abban Ammar, kamar daga sama lieutenant yace mata “Idan kin gama kukan ki tashi mu tafi to.”
Cikin rawar jiki Zeituna ta mik’e har ta k’afafun ta na hard’ewa, lura da hakan yasa lieutenant tambayar kanshi “Anya kuwa wannan mu’amular ce ta dace ka mata a matsayinta na yarinya?”
Ganin sai sauri take ta fita daga d’akin yasa ya rik’o hannunta ta baya, cak ta tsaya ta juyo da sauri ta kalleshi, suna had’a ido saita sake b’arkewa da kuka ta rufe fuska da hannu d’ayan, a lokacin tausayinta ne yaji ya daki zuciyarshi, tunawa da yayi har yanzu baiji muryarta ta fito fili ba, a hankali ya jawo hannunta ya kwantar da ita kan k’irjinshi, wani lafiyayyan masauki ya mata a cikin jikinshi tare da zagayeta da hannayenshi ya fara daddab’a ta alamar tayi shiru, Zeituna kam take kukanta ya tsaya kamar anyi ruwa an d’auke, shiru tayi yayin da bak’on al’amarin ya nemi zautar da tunaninta, a d’aya b’angare kuma numfashinta ne taji yana kokawar barin gangar jikinta, wannan mafarki mai cike da tarin al’ajabi da rud’u ya addabeta, har yanzu ta kasa tashi daga wannan baccin da ba zata kira shi da mummunan bacci ba, haka kuma ta kasa yin farin ciki ko da a iya mafarkin ne, wani zazzab’i ne taji yana neman rufeta har jikinta ya fara b’ari saboda rashin sabon yanayin data tsinci kanta a ciki. Shi kanshi lieutenant wani bak’on al’amari ne ya ziyarce shi, amma saiya dake ya ci gaba da shafa har yayi k’arfin halin fizgo nutsuwarshi ya d’an sunkuyo yana lek’o fuskarta cikin dakusashiyar murya yace “Kukan ya isa haka, karki damu da halin Ammar, muma kanmu haka muke fama da shi, ya kamata ace kinsan shi bai kamata ya baki wahala ba, kinji ko? Ka da ki sake zubar masa da hawaye, idan ya fahimci haka zaki shiga tara a hannunshi, ba zai duba matsayinki na matar mahaifinshi ba, dan ko uwarshi ce zai iya yi mata haka, karki damu kinji.”
Har ga Allah Zeituna ba kukan abinda Ammar ya fad’a mata take yi ba, amma jin abinda lieutenant ya fad’a saita tambayi kanta “Meyasa yake tunanin Ammar ne ya sani kuka? Me Ammar yayi da har yayi tunanin maganganunshi ne suka b’ata min rai? Soyayyar mahaifiyarshi ce ya nuna min a fili, hakan kuma ya birge ni sosai, tabbas shi d’in mai k’aunar mahaifiyarsa ne, tunda har kai mahaifinshi ya maka kashedi akanta.”
A hankali lieutenant ya raba jikinsu tare da nufa k’ofa, hakan kuma shi ya dawo da hankalinta kanshi, a hankali ta bi bayanshi gabanta na fad’uwa na fargaban abinda zata tarar, yana shiga d’akin da sallama ya samu Ummy ta fito daga wanka da doguwar rigar bacci mai laushin gaske ta zallar audiga, kanta babu d’an kwali sai dogon gashinta daya sha kitso yake kwance har gadon bayanta, tana ganinsu tayi saurin juyawa bayanta ta d’auki wata hula ta d’ora akan tana mai fad’ad’a murmushinta tana fad’in “Sannunku da zuwa.”
Murmushi ya mata yace “Sannu da hutawa uwar ‘yan biyu.”