BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL
Suna cikin wannan ture turen Jibril ya juyo yace “Billahil-azim duk wacce naga ta turi yar uwarta saita yabawa aya zak’inta, kunji na fad’a muku.”
Jin haka yasa suka harari juna sukayi shiru, da wannan kuma suka isa cikin yardar ubangiji, nan dai suma sukayi tasu ta’aziyar, sun samu Hajia kuma ta dire tace da ita zasu koma dan ta gaji da hayaniya da zahi, suna haka colonel ya samu kira na gaggawa a babban birni Niamey, dama tare da mutanenshi yake dan haka ya musu sallama suka d’auki hanya.
Bayan sallah azahar kuma saiga Ammar da su Junaid da Amar a mota d’aya, basu wani shiga cikin gida ba nan suka zauna ana ta hira da jimami, bayan sallah la’asar kuma Hajia ta fito cikin shirin tafiya tace gobe ta dawo sai ayi sadakar uku, loiacin Amar suna d’an nesa da gidan dan haka bata ganshi ba, nan aka had’a ta da yan matan da samarin da kuma iyayen maza aka ce su tafi gida tunda babu kowa, saida kowa ya gama shiga aka fahimci Hamna bata shigo ba, saida aka kirata ta fito ashe tana can tana gyara jikinta tana fesa turare, kasancewar Hajia na tsaye ta fito nan ta duba motar da zata shiga sai taga babu wuri, dan haka ta nuna mata motar Ammar data hangeshi shi da Junaid kad’ai, can ta nufa zata shiga baya Junaid ya fito yace “Gimbiya Hamna shigo gaba, ni na ma samu motar da zan shiga.”
Ita kuma murmushi tayi ta shiga kamar yanda yace, a ranshi kuma cewa yayi “Ba gaira ba dalili na had’a mota da ku kafin mu kai ta kama da wuta, ai wannan tafiyar babbar tafiya ce.”.
Saida Ammar ya ji motoci na oda alamar sun fara tafiya ya d’ago kanshi, juyawa yayi inda Hamna ke zaune suna had’a ido gabanshi yace wani “Dassss.” Ya fad’i ba tare da sanin dalili ba.
Inda ita kuma na ta gaban yace “Dammm.” Kallon tsoron da take mishi ne yasa ya had’e fuska yace “Dallah ni bari kallo na sai kace mayya.”
Da sauri ta kalli gabanta a ranta tana fad’in “Toh, aifa kuma na shiga uku, gashi yanzu babu ni babu guduwa idan ma na k’ular da shi.”
Tashin motar yayi ya fizga da gudu inda ta bi hannunshi da kallo yanda ya murza sitiyarin, k’aramar jakarta ta fito da ita ta d’auki abun sauraro (écouteur) ta danna a kunne saboda tasan zaman shiru ne za ayi, suna shiru haka tana sauraren wak’ok’inta kira ya shigo wayar, d’auka tayi suka fara hira ita da saurayin na ta duk da ba wai son shi take ba, yanda take kashe murya dan kar Ammar yaji yace tayi laifi ashe dai bata tsira ba, dan yanzun ma haushi ne ya kama shi wai akan me zata wani kashe murya haka tana hira da saurayi, cikin hassala ya fizgo wayar hakan yasa abun sauraron ya fita muryar saurayin ta bayyana, yanda shima ya kashe murya ne ya k’ara tunzura Ammar, dan haka saurayin da baisan meke faruwa ba yace “To ai dole ne ko? Yanda kika kashe min jiki haka da muryaki ai sai bacci ya d’auke ni alhalin ina cikin tuk’i.”
Tsabar neman fita Ammar sai ce mishi yayi “Insha Allahu kana baccin nan ba zaka bud’e ido a ko ina ba sai cikin k’abari, ku ko kunya baku ji ku tsaya hira da ‘ya’yan cikinku haka, yanzu haka matarka na can ranta a b’ace amma baka san ya zakayi ka kwantar mata da hankali ba, k’aryar banza kawai.”
Kashe wayar yayi ya cillata k’asan k’afafun shi inda birki yake yana jan wani tsakin, Hamna dake kallonshi ta kasa gane me yake nufi tace “Yaya Ammmm…”
Bai bari ta k’arasa ba ya nuno mata yatsa yace “Kar ki sake ki min magana.”
Yanda ta ga fuskarshi yasa taja baki tayi shiru, suna tafiya taji shirun yayi yawa, hannu ta zura ta kunna redion motar dan shi tsabar baya son hayaniya ko redio na mota baya kunnawa, tana kunnawa yayi daidai da tashar ana wak’a, cikin jin haushi ya buge hannunta yace “Kar ki sake tab’a komai dake motar nan.”
Tab’e baki tayi suka ci gaba da tafiya, ana haka ta ji masuburbud’ar sanyi (ac) na bata sanyin dayawa ita kuma bata so, sai kawai ta zura hannu zata d’an juyar da shi gefe, ai kuwa sai ji tayi kanta ya bugu da abun sanyin saboda wani wawan birki da Ammar ya taka, kafin ta ankara taji ya fizgo hijabinta dake jikinta wanda dama ta sanya ne saboda zasu zo wajen rasuwa, kamo hannayenta yayi duka biyun ya had’e wuri d’aya yasa hijabin ya d’aure su tamau, kallonta yayi da jajayen idonshi yace “Kinfi kowa sanin bana magana sau uku akan abu d’aya, nayi biyu ba zaki sani bayi uku ba, idan har na ji bakinki yanzu wallahi bolar dake kan hanyar nan zan tattaro na tusa miki su a baki har sai mun kai gida.”
Hamna da ido suka cika da hawaye shiru tayi dan babu damar bashi ko da hak’uri ma, bai sake kallonta ba har saida suka isa cikin gari ya kalleta yace “Ke gaki marar kunya, a gabana wani d’an iska zai kira ki har kina kashe mishi murya, shi kuma dayake babban kwarto ne har yana fad’a miki wai zai yi bacci, haba.”
Hamna dai ko kallonshi batayi ba har suka isa gida, motoci na tsayawa a farfajiyar gida aka firfito, Hamna babu hannayen bud’ewa saida Ammar ya bud’e mata k’ofar ta zuro k’afafu ta fito, take kallo ya koma kanta inda Junaid da dama yasan abinda zai faru kenan ya riga kowa bushewa da dariya, da sauri Amna ta k’araso ta kunce mata hannuwa tana fad’in “Yaya Ammar ne ya d’aure ki? Ke kuwa me kika masa haka kamar wata dabba?”
Kamar zatayi kuka tace “Me kuwa zan masa, bak’in halin ne ya motsa da mugunta.”
Lieutenant ne yace “Yanzu Ammar d’aure yarinyar nan kayi kamar wata dabba, me tayi maka to?”
Yana cikin rufe mota ya nufi b’angaren su yana fad’in “Bata jin magana.”
Cikin b’acin rai lieutenant yace “Kai maganar kake ji? D’an iska kawai yarinya bata maka komai ba ka kamata ka d’aure.”
Juyowa Ammar yayi ya kalleshi, juyawa yayi ya ci gaba da tafiyarshi haka suma, ana shiga falo Hajia tace “Wai ina shalele na? Ance tare muke amma har yanzu ban ganshi ba.”
Umaima ce ta tab’e baki a ranta tace “Mu da ba shalelenki ba ma dai gamu ko ba’a san ganinmu.”
Sai lokacin sukayi ido hud’u da Amar, ai kuwa sakin jakarta tayi ta zaburo ta daddafe fuskarshi tana tambayar “Shalele lafiya? Meya sameka a fuska haka? Ba dai hatsari kayi ba kuma shine babu wanda ya fad’a min.”
Cikin halin ko in kula yace mata “Eh, ba wani babban abu bane, karki d’aga hankalinki.”
Hamna ce tace “Amma yaya Amar na d’auka cewa akayi fad’a kukayi kai da yaya Ammar.”
Da sauri kusan kowa ya kalleta inda Amar har saida yaji kamar ya mareta, Hajia ma kafeta tayi da ido tace “Fad’a kuma? Waya fad’a miki?”
Yanda duk taga wasu na kallonta ne yasa tayi shiru, cikin zaro ido Hajia tace “Ba dake nake magana ba kina ji na kinyi shiru.”
Cikin duburburcewa tace “A’a Hajia nima ban sani ba, jiya dai naji su aunty suna fad’in ko sunyi fad’a ne lokacin da zasu tafiya, amma bansan meya faru ba, mu bamu ma gidan a lokacin.”
Lieutenant ne ya kalli Amar yace “Amma ai jiya ba haka kuka fad’a mana ba, ka ce hatsari kayi da moto.”
Hajia ce ta mishi wata tsawa kamar k’aramin yaro tace “Rufe min baki malam, dama ko kun sani wace tsiyar zaku tsinana, duk ba ku kuke d’aure mishi gindin ba.”
Amar ta kalla tace “Shalele da gaske ne abinda ta fad’a?”
Ba tare daya had’a ido da ita ba yace “Ba gaskiya bane, ni banyi fad’a da shi ba.”
Wani murmushin yak’e Hajia tayi tace “Shalele kasan dai zansan abinda ya faru ko? Ka fad’a min ko kuma na tambayi wanda zai fad’a min komai daya faru.”