BADAK'ALA COMPLETE HAUSA NOVEL

BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL

Da k’yar ya bashi hannu yana fad’in “Alhaji Ammar kana lafiya.”

Ta gefen ido ya kalleshi yace “To lafiyar nan dai da dama, jiya ai nayi croisement da kai a babban titi.”

Kallonshi yayi da mamaki dan shi dai yasan jiya duk a yawace yawacen shi bai isa can wajen ba, cikin k’yabta ido na marar gaskiya yace “Wane lokaci?”

Cikin murmushin mugunta yace “Nasan dama baka ganni ba, amma ni na ganka tare da wata cikar, da farko ma na d’auka madame ce wallahi, sai daga baya na ankare ashe ba ita bace, ai na so tsayar da kai dan ni kaina kayan sun birge ni fa, kai Alhajin nan ka iya zab’ar harka.”

Ko da ya gama fad’a kuma ya shige yana mishi dariyar mugunta, kawai ya fad’i hakane fa dan ya ankarar da ita in ma bata san waye ba, in kuma ta sani to tasan da irin mutumin da take mu’amula, kallonshi tayi sai taga kawai yana ta zufa, da k’yar ya kalleta yana washe mata baki, yamutsa fuska tayi tace “Saida safe.”

Da kallo kawai ya bita, tana shigewa ya mik’e ya kalli k’ofar ya nunata da hannu yace “Wannan Ammar wannan Ammar Allah ya tsine maka albarka, shegen yaro mai kama da kafiran farko.”

Juyawa ya fita ba tare da tunanin sake dawowa ba, ita ma ko da ta shiga bata iya cewa komai ba kawai ta zubawa sarautar Allah ido, su Jibril kuma dake fita su suka samo cikakken bayanan shi, dan haka ana jin waye shi aka ce wannan magana ba ita ba kamarta, tayi farin ciki saboda ta tsira daga wannan tullu, *bayan wata d’aya* kuma Allah ya sake had’ata da d’an abokin lieutenant, shima dan danan magana ta kankama har an saka ranar kawo kaya, sai dai shi kuma matsalar ance matarsa ce fitinanniya namber one, dan a cikin gida ma ita ke mulki, lieutenant ne yace baya son tashin hankali dan haka Allah ya fito mata da wani.

*Sanda* ake ta k’ok’arin ganin an had’a Hamna da wanda ya dace, a lokacin kuma Amna taje awo na farko, a cikin tambayoyin da likitar ta mata ne take tambayarta bata jin wata matsala, cikin sanyi jiki tace “Gaskiya ina d’an yawan jin ciwo haka kamar kusan k’uguna da…mtsss ni abun ma wallahi ya fara damuna.”

Tambayarta tayi “Kina jin zafi idan kina fitsari?”

Da sauri tace “Gaskiya ina ji, na jima ina jin haka kad’an kad’an.”

“Kina zubar da farin ruwa ne masu kamar kub’ewa?”

A hankali tace “A’a.”

“To akwai kasala ko ciwon jiki?”

“A’a.” Shima ta fad’a, ci gaba tayi da rubutu tana mata tambaya kafin daga bisani ta rubuta mata wata takarda ta bata tare da cewa “Ki samu rendez vous kiga gynécologue saiki masa bayanin abinda kike ji, insha Allahu idan ma magani ne ko shawarwari duk zai d’oraki akai.”

Tunda taji abinda ta fad’a gabanta ya fad’i, a take jikinta taji yayi mugun yin sanyi, sai taji duk ta sare hankalinta da nutsuwarta suna neman barinta, a daddafe aka gama mata awon nan ta dawo gida, daga Ummy har shi babu wanda ta fad’a ma, tunaninta kawai shine idan taje taga docteur d’in za’a jawo mata ciwon da bai kai girman matsalarta bane, dan haka taja baki tayi shiru bata fad’a ma ko da yer uwarta ba, sanda ya dawo gida saida ya tambayeta ya awonta ya kasance, amma sai tace lafiya lau, a haka aka tafi da lafiya lau ta ci gaba da b’oyewa, saida lokacin komawarta awo na biyu yayi ta samu tayi d’ibar jini shi ma dan tasan sai dashi za’a mata awo na gaba, ko da taje asibitin ta kuma yi sa’a da likitar data dubata a farko ta tambayeta me aka ce mata, sai kawai tace ai ta daina ji ma da aka d’orata kan magani yanzu ta warke, anan likitar ke mata murna dan ita kanta da taji ta fad’a mata abinda take ji saida ta d’anyi wani tunanin na daban.

Duk zaune suke a falo sun gama shirin tafiya barka gidan Nura da matarshi ta haihu, kusan duk jikokin nan yanzu Hajia ce ta d’auki nauyin yin kayan barka indai akayi haihuwa, hakan ya ma kowa dad’i inda addua’r sa albarka ke riskar Ammar kowane lokaci, dama tace sai zasu tafi sai su biya a siye kayan a wuce, Zeituna ce ta kalleta babu fargaba babu tsoro cikin farin ciki tace “Hajia dreba fa na jira a waje, kuma gashi baki fad’i me da me za’a siya ba.”

Kallonta Hajia tayi ta kalli Ummy dake b’allawa Shureim botira tace “Ga Sa’ada nan ta fad’a miki duk abinda ya kamata saina bayar da kud’in a siya.”

Kallonta Ummy tayi ido ciki ido babu wannan sunkuyar da kai ko wani abu tace “Idan mun tafi zai sauke mu tare ai sai mu siya.”

Jinjina kai tayi ta kalli Husseina tace “Kiyi sauri ke kuma ki gama shafa kwallin nan kamar wata budurwa kike ta darzashi a ido.”

Saida ta murgud’a mata baki tace “Babu ruwanki barni na shafa, kika sani ko na samu miji daga wannan fitar.”

Dariya Hajia tayi tace “Ai kuwa dai zai kwashi kabari kusa.”

Kallonta tayi tace “Au! Ke a ganni zan mutu da wuri ne? Ai ko zan tafi tare dake zan tafi, kuma ma ai kin fini kusa da kabarin.”

Cikin dariya Hajia tace “Saboda me?”

“Saboda ke ce mijinki ya mutu.” Ta fad’a tana mik’ewa tana gyara gyalenta, su Zeinabu dai dariya suke har suka rungud’a baki d’aya suka fita, lallai rayuwa yanzu ta sauya sosai.

*Bayan sun dawo* da dare ana zaune ana ta hira gwanin sha’awa, colonel ya diro garin cikin kakinshi marar hayaniya sosai sai tarin galolin nasara da jajircewa, har gabanta yaje zai durk’usa ta rik’e hannunshi da murmushi a fuskarta ta zaunar dashi gefenta, fuskarshi take kallo tace “Hussein an dawo lafiya? Ya aikin kuma?”

Saida ya kalli su Ummy da Zeinabu dake gefe, shi dai baya nan aka samu wannan canjin, hakan bata tab’a faruwa ba sai yau, cikin ldabi yace “Hajia kuna lafiya?”

Cikin murmushi tace “Lafiya lau kowa.”

Dafashi tayi tace “Ka shiga ciki ka samu kayi wanka sai ka zo ka ci abinci ko.”

Sunkuyar da kai yayi yace “To Hajia, nagode Allah ya k’ara girma.”

Da murmushi ta amsa da “Ameen, Allah yayi albarka.”

Shigewa yayi ciki yana jin wani sakai a zuciyarshi, ita kanta yanzu wani sakayau take ji data zama mai bin yaranta da addu’a, duk sanda ta musu sai ta ga tsantsar farin ciki a fuskokinsu, yanzu da take jan kowa a jikinta sai taji tafi ingantacciyar lafiya, bakinta baya zama shiru, yara duk suna sakewa da ita har su zauna gabanta suna hira ko da ta shirme ce, yanzu har basa zama falonsu na sama sai falon tara da ita, kuma a wannan zaman da take tare da su ne take gyara musu wasu k’ananan kurakurai ko da na cikin fad’a ne a kalma, lallai ta jima tana rayuwa cikin kuskure.

*Rayuwa kenan*, a cikin wata hud’un nan sau uku ana d’auko maganar auren Hamna amma sai abun ya lalace, izuwa yanzu kam sai kowa ya fara wani tunanin na daban, Husseina da Hassana ne suka mik’e wajen neman taimakon malamai, sai dai duk inda zasu tafi basa tafiya da Hamna sai dai su fad’i matsalarsu kawai, dan Husseina tace ba zata yarda abinda ya faru kanta ya faru kan jikarta ba, da ire iren haka suka fara takura Hamna da turare turare da shaye shayen rubutu da maganin aniya makomiya, inda abun ya fara girman da ana sauke Qur’ani da sadaka da yanka abun sadaka, an shiga kashe kud’i sosai saboda tunanin ko sihiri ko kuma aljanu, sai dai har yanzu babu wani labari.

*Duk* da ciwon kan da take ji bai hanata kama wankin kayan yaranta ba, dan in suka tafi islamiyya kawai take samun damar yin aiki hankali kwance, duk sanda ta duk’a sai taji kamar kanta zai fad’o k’asa ko idonta, idan ta d’ago kuma saita rintse ido saboda jiri ke d’ibarta, a haka dai ta sake sunkuyawa d’aukar wasu kayan dan ta shanya, tana d’agowa taji kamar an buga mata guduma a tsakar kai, daga lokacin bata sake sanin me ke faruwa a duniya ba, fad’uwa tayi da tsohon cikinta wata takwas wanda aka bata sati biyu idan bata haihu ba ta koma asibiti, bokitin ne ya juye inda ruwan suka malale har suka gangaro inda take kwance suka b’ata ta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231 232 233 234 235 236 237 238 239 240 241 242 243 244 245Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected