BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL
K’anwar Zulai ce tace “Duk da haka dai ai sai ku ragawa ranar bikin, tunda yanzu ne aka fara.”
Pappa ne yace “A’a tanti, mu a wurin mu shagalin bikin Ammar tun jiya aka fara shi, ranar biki ma a shirye muke zamuyi fiye da haka, kawai ku bamu hanya.”
Ai kuwa wucewa sukayi ba tare da sun daina ba, Ammar na shiga mota ya saki murmushi, dan ko ba komai yaji dad’in abinda Pappa ya fad’a, daga nan gida suka wuce, su tarar anata hidima kamar yau ne bikin, kafatanin ahalin Gaga babu wanda baya da ankon gallelen leshin da akayi, sai amare da aka ma shiga irin ta barebari (asalin mahaifiyarsu Suley), sunyi kyau sosai musamman ma Amna kayan sun karb’e ta haka ma kalar shud’i da sararin samaniya, hatta gyaren kan da aka musu irin na barebari ne wanda ya fito sosai ake ganinshi, nan abokan Ammar suka kutsa dashi d’akin shi suka sashi ya canza kaya zuwa chadda kalar ruwan samaniya sannan suka fito, filin taron suka kaishi inda suka d’auke su hotuna shi da amaryarshi, yau ma dai kamar jiya lafiya aka gama caskalewar aka kwanta kuma sai gobe idan gari ya waye a d’ora.
Gida yayi shiru baka jin motsin kowa da komai, Ummy ce tasa lieutenant gaba sai rufe fuska take alamar ita kunya take ji, shi kam banda kallonta babu abinda yake yi har yace “Uwar yan biyu wai meye haka? ko dai kin tuna da k’uruciya ne?”
Sake rufe fuska tayi da pilown dake hannunta tana murmushi, shima fad’ad’a murmushin yayi yace “Dan Allah ki fad’a min meke faruwa, ko kuma nayi hushi.”
D’agowa tayi da sauri ta kalleshi tace “Zan fad’a to.”
Zuro mata kunne yayi yace “To ina jinki.”
Saida ta sake rufe ido tace “Dama ai…dama, nayi b’atan wata ne, kuma n…na auna da kaina na tabbatar, cewa su Ammar zzza..su samu k’ane.”
“Me?” Lieutenant ya fad’a da k’arfi tana kallonta…
*Alhamdulillah*
*Yawan sharhi, yawan rubutu.*
09/09/2020 à 17:58 – Ummulkhairi: ❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️
*BADAK’ALA*
❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️
*Labarin Gaske*
*NA*
_SAMIRA HAROUNA_
*Litattafan marubuciyar*
*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D’AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD’I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K’ADDARARMU_
*8* _K’ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k’ura)…_
*14* _BADAK’ALA…_
*SADAUKARWA GA*
_*AHALI NA*_
*TAURARIN NIGER*
“`(Tsintsiya mad’aurinki d’aya)“`
*A SANADIN K’AUNA*
_Barka my BK, ina tayaki murnar kammala wannan novel naki, Allah ubangiji ya baki ladan fad’akarwa, Allah ya saka miki da alkairinsa, kurakuren da kikayi a ciki ya yafe miki, sai mun jiki a next novel idan Allah ya amince._
_Bismillahir rahamanir rahim_
_33_
Baki har kunne lieutenant yace “Uwar yan biyu da gaske kike fad’a min maganar nan kuwa?”
Kallonshi tayi tace “Da gaske mana, muna irin wannan wasar ne?” Girgiza kai yayi yace “A’a.”
Kallon gefe yayi yace “Kai amma wannan abu sa mamaki da kuma d’aure kai.”
Kallonta yayi yace “Wato ke idan na fahimceki irin haihuwar rak’uma kikeyi, kai Allah nagode maka abisa wannan kyautar.”
*Washe gari* da sassafe lieutenant ya fito cike da farin ciki da zumud’i, duk da yana jin nauyin fitowa kai tsaye ya fad’awa Hajia Sa’ada na da ciki, amma yayi niyyar fad’a mata ko da a birkice ne yanda zata gane ko da kuwa hakan na nufin yayi wani abu a aikace ne da zaisa ta fahimta, dan rashin fad’a mata da wuri zaisa yasa fad’a da tsegumi ranar da cikin ya bayyana. Yana isowa falonta saiya samu Zeituna kwance akan kujera da alamar galabaita a tare da ita, da sauri ya k’arasa ganin babu Hajia a wurin, yana zuwa ya zauna ya kamta ta tashi zaune yana kallonta yace “Zeituna lafiya? Me yake damunki ne? Me kike yi anan kwance?”
Saida ta k’ara yamutsa fuska tace “Bana jin dad’i ne, ko baccin kirki banyi ba saboda amai.”
Cike da nuna kulawa hankali a tashe yace “Subhananallah! Amma kuma shine baki fad’a min ba kika ja baki kikayi shiru, to tashi mu tafi asibiti a duba ki.”
Kallonshi tayi tace “Duk likitocin da muke da su a gidan nan sai mun tafi asibiti?”
D’an dafe kai yayi tare da tashi tsaye yace “Wallahi na sha’afa, bari na wa Sa’ada magana saita duba ki.”
D’akin Ummy ya nufa da rawar k’afa, zai shiga Hajia ta fito daga nata d’akin, ido hud’u da sukayi ya sashi tsayawa ya sunkuya yace “Ina kwana Hajia.”
Saida ta harareshi sama da k’asa tace “Meye kuma na wannan rawar k’afar zaka shiga d’akin ta? Ina ce ga amaryar can ka baro a falo, Hassan anya kuwa baka zama lusarin namiji ba.”
Cike da ladabi yace “Yi hak’uri Hajia, dama yarinyar can ce bata da lafiya, shine zan kira Sa’ada ta dubata.”
Kallon Zeituna tayi ta kuma kalleshi tace “To sai me? Nace sai akayi yaya? Akan bata da lafiya ne kake wannan saurin kamar zaka tashi sama?”
Dogon tsaki taja kafin tace “Meke damunta? Nasan dai ba zai wuce tace ciki ne da ita ba ko? To kayi farin ciki zaka sake zama uba a wannan shekarun naka.”
Lieutenant da yake jin kamar yayi kuka jin abinda ta fad’a yasa ranshi sanyi, idan Zeituna ma ciki ne da ita shi kam Alhamdulillah, mata biyu a lokaci d’aya zasu sake haifa min yara, watak’ila ma a cikinsu wata ta haifi yan biyu, tunanin hakane yasa shi sakin murmushi, yana ganin Hajia ta nufi falon ya biyo bayanta, tana zuwa ta zauna tana k’arewa Zeituna kallo, fuska a had’e tace “Kinyi farin ciki ko? Hankalinki saiya kwanta tunda gashi kin nuna min kun gyauraya ke da Hassan har zaki haihu dashi kema.”
K’asa tayi da kanta tana wanda da yatsun hannunta, tana so ta tashi ta koma d’akin ta sai dai tana jin tsoro, lieutenant da farin ciki ya gama baibayeshi ne ya kalli Hajia yace ” Hajia ai ita kanta Sa’ada bata da lafiya.”
Wani kallo ta watso mishi mai kama dana k’yama tana cewa “Ban gane bata da lafiya? Meya sameta ita kuma?”
Shiru yayi haka ita ma kallonshi take tana jiran amsa, fahimta da tayi yasa ta canza yanayin kallon da take masa tace “Me kake nufi? Hassan wai ita ma Sa’ada ciki ne da ita kake so kace?”
Sunkuyar da kai yayi baice komai ba wanda yayi daidai da fitowar Ummy daga madafa, k’ura mata ido tayi tana kallo harta k’araso kusansu, babu wani abinda ya sauya a jikinta, dama ita d’in jawur yake kuma ba k’iba ce da ita ba, idan da akwai abinda za tace ta mata bai wuce tace ta d’an rame ba, saida Ummy ta gaishe da Hajia da lieutenant tare da bashi kofin shayin dake hannunta, ta juya zata koma ga aikinsu kenan Hajia tace “Sa’ada, wai ciki kika ce mishi kina da?”
Wata irin kunya ce ta rufe Ummy tare da fad’uwar gaba, shiru tayi ba tace komai ba sai zazzare ido take, Hajia na ganin haka cikin hushi tace “Amma dai ke akwai jahila, yanzu Sa’ada da girmanki ne zaki wani d’auki ciki? Shekararki nawa rabonki da ki haihu? Har an fidda rai da sake samun haihuwa daga gareki sai kawai yanzu ki wani ce kina da ciki, anya kuwa dan Allah ne kika yarda kika samu cikin nan, kenan dama can kina haihuwar kawai iskanci ne yasa sai lokacin da kika yi niyya kike yinta, ko kuma dai dan kinga kishiyarki na da ciki ne kema kika d’auka?”
Tsaki Hajia tayi tare da mik’ewa ta bar falon zuwa farfajiyar gidan, Ummy da kanta ke k’asa saida taga fitarta ta d’ago a hankali ta sauke ido akan Zeituna, ido hud’u sukayi dukansu hawaye ne suke, da sauri Ummy ta juya ta shiga d’akin ta tana kuka, ita ma Zeituna fashewa tayi da kuka wanda yasa lieutenant rasa yanda zaiyi, kallonta kawai yake bai iya cewa tayi shiru ba, dan shi kanshi abinda Hajia ta mishi ji yake kamar yayi kukan, dan har yanzu baiga dalilin da zaisa mahaifiyarshi ta dinga tozartashi irin haka haba ba har a gaban matanshi.