BADAK'ALA COMPLETE HAUSA NOVEL

BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL

*Allah ka mana kyakyawan k’arshe.*

06/06/2020 à 12:38 – Ummulkhairi: ‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍
*BADAK’ALA*
‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍

*Labarin gaske*

*NA*

_SAMIRA HAROUNA_

*Litattafan marubuciyar*

*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D’AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD’I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K’ADDARARMU_
*8* _K’ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k’ura)…_
*14* _BADAK’ALA…_

*SADAUKARWA GA*

‍‍‍ _*AHALI NA*_‍‍‍

*TAURARIN NIGER*
“`(Tsintsiya mad’aurinki d’aya)“`

_Bismillahir rahamanir rahim_

_11_

Husseina dai dama ba nisa akayi da ita ba daga gidan iyayen ta, dan daga gidan ana hangen gidan nata iyayenta, sai dai kuma a wannan rana taga tashin hankalin da bata tab’a gani ba a tsawon rayuwarta, dan wannan daren nata na farko daren tonon asiri da tashin hankali ya zamar mata, sam *Salisou* bai mata da kyau ba a wannan rana ko nace dare, domin kuwa dukan mutuwa ya mata tare da yi mata saki har uku, daga shi har ita da sauran matanshi babu wanda yayi bacci, kumfar baki kawai yake yana fad’in shi taimakonsu ne yayi ya aureta saboda ganin ta jima babu aure, ashe dai da dalili shiyasa basu samu miji ba, tunda gudun-gudun safiya ya shiga gidan mahaifiyarshi dake had’e da nashi gidan, kaf ya kwashe ya fad’a mata abinda ke faruwa, nan fa ita ma ta d’ora ta ta kalar tijarar tana sababi, abinka ga sanyin safiya da sannan duk wanda yasan unguwar d’an gulbi yasan unguwa ce da babu sarari sosai, hakan yasa kowa kamar har gidanshi akaje aka fad’a mishi saboda yanda mutane dayawa suka fito kallon k’wam, kamar a tatsuniya haka Salisou da uwarshi suka dinga watso yan kayan da aka kaiwa Husseina wacce ita kanta suka turo k’eyar ta waje, banda kuka babu abinda take kamar zata had’e zuciya ta mutu, ga shegen dukan daya mata wanda yasa jikinta yin tsami.

Labari ne ya samu mutanen gidansu suma suka fito dan jin ance da Husseina abin ke faruwa, a lokacin tana tafiya a hankali zata zo gidansu, tana zuwa k’ofar gidan Hassan ya tare k’ofa yace “Gidan nan kike nufin shiga? Ai in kinga haka ta faru to babu raina ne, dan haka tun wuri ma kisan inda dare ya miki, dan ni ba’a zina aka haife bi ba kuma duk zuri’ar mu babu mazinaci, dan haka wallahi ba zan haifi karuwa a gidana ba.”

Ramma dake daga cikin soro ce tace “Alhaji haihuwar karuwa na nawa kuma, ai sai dai kar a k’ara, amma kam ka riga daka haifeta.”

“Ai kuwa ba dai a gidan nan ba wallahi.” Ya fad’a lokaci d’aya ya kalli Husseina da banda kuka babu abinda take yace “Zaki b’ace min da gani ko sai ci uwarki a wurin nan, k’ur’ani ba zaki shiga gidan nan ba, idan kuma uwarki ce ke saki duk iskancin to ki fad’a min saina turo miki ita ku tafi tare.”

Zubewa tayi kan gwiwoyinta cikin tsananin kuka ta had’e hannayenta tace “Dan Allah Baba, dan annabi, ka dubi girman Allah ka barni na shiga ciki, Baba bana da inda zanje idan na bar nan.”

“To ni ina ruwa na, wannan matsalarki ce ba tawa ba, da da kike iskancin baki tuna da irin wannan ranar ba.”

Saratu na k’ofar d’akin ta tana hango duk abinda ke faruwa daga nan, kuka take tana addu’a tare da tunanin yanda akayi haka ta faru, tana cikin wannan tunani ne ta sake jin ihun Husseina wacce Ramma ta sake mik’owa Hassan wani ice daga nan soron wanda ake ajewa saboda lokacin damuna ya fara jibgarta a filin Allah yana fad’in “Kije ki yi karuwanci mana, wannan keta shafa bani ba, dama karuwar gida ce bamu sani bane.”

Lokacin ne Saratu ta fito tana kuka tana bashi hak’uri, amma a k’arshe sai yace ta zab’a ko zama dashi ko da ‘yarta, bud’ar bakin Saratu cewa tayi “Ita fa ‘yata ce data fito daga jikina, ko ka manta da karin maganar nan da ake cewa *namiji goma ba uba goma bane*? Zanyi farin cikin k’arar da rayuwata a tare da ‘ya’yana, dan haka na zab’i na tafi tare da ita duk inda zata saka k’afa.”

Kama Husseina tayi amma saita sake sulalewa tana kuka tace “A’a Inna, ban cancanci ki ruguza rayuwar aurenki ba a kaina, shekararku talatin da hud’u tare, ba zan yarda yau na zama silar wargajewarshi ba, komai daya faru laifina ne.”

“Nima kuma ba zan tab’a bari taki rayuwar ta lalace ba, dan ni tawa rayuwar dama ta jima da gurb’acewa tunda na shigo gidan mahaifinku, dan haka ba zan tab’a barinki ke kad’ai ba bayan bansan ina zaki je ba.”

Hannayenta ta rik’e sosai tace “Inna kiyi hak’uri ki barni na tafi, na miki alk’awarin kare mutumci na, sannan zan dawo nan bada jimawa ba, Inna yanzu ran Baba a b’ace yake, zuwa lokacin da zai huce zan dawo nasan zai karb’e ni.”

Sun jima suna wannan musayar yawun kafin Husseina ta saki hannunta ta fara tafiya, za tabi bayanta Hassan yace idan har ta tafi bada yawunshi ba Allah ya isa, juyowa Husseina tayi taga tabbas mahaifiyarta fa idonta sun rufe, hakan yasa ta kalli gabanta ta ari na kare da gudu ta ratsa mutanen dake kallonsu ta bar wurin, saboda a lokacin akwai kula da hakk’in mak’wabtaka yasa wani mak’wabcinsu ne ya bi bayanta ya tafi da ita gidanshi.

Kwanan Husseina *takwas* a gidan nan babu wata matsala, babu wani abu da mutanen gidan ke nuna mata na k’yama ko banbanci, duk da Saratu bata zo ta ganta ba saboda tun ranar da abun nan ya faru doka mai tsanani Hassan ya kafa mata, wanda yanzu ko abincin gidan baya bata sai Suley ne idan yayi fafutuka yake kawo mata, sai Suley ne ke ziyartar Husseina yaga halin da take ciki, haka ma yar uwarta Hassana ta zo ta ganta, ana haka kuma sai wata matsalar ta kunno kai, domin kuwa ciki ne ya bayyana jikin Husseina, bayan ta tabbatarwa da kanta tana da ciki shigar wasu watanni da suka gabata sai kawai ta yanke hukunci a kai, da asuba ta bar gidan *malam Yacub* ta shiga gari, dan a tunaninta bata da ciki ma aka wulak’anta ta bare yanzu asan tana da cikin banzan malamin nan.

Yawo take babu wurin zuwa, wanda a lokacin kud’in mota kawai take nema da zai kaita Diffa wajen dangin mahaifiyarta komai rashin dad’in can d’in zaifi mata, amma sai gashi har magriba ta mata bata ma samu abinda zata saka a bakinta ba, dan duk wanda ta nema taimako sai an mata kallon tsaf, ganinta zaune da kyau tsaye da kyau amma tana neman taimako dan mutuwar zuciya, dan haka babu wanda yayi yunk’urin taimaka mata, tana cikin yawo ta had’u da wani babban mutum ta nemi taimakonshi, amma saiya nuna mata idan ita ma zata taimaka masa saiya taimaka har da wurin kwana ma, mik’ewa tayi daga durk’ushin da tayi ta juya baya zata tafi, hawaye ne suka fara mata zarya a ido inda kalmar mahaifinta ke dawo mata a k’wak’walwa ta cewa ” *Kije kiyi karuwanci mana*, wannan ke ta shafa bani ba, dama karuwar gida ce ke bamu sani bane.”

Wannan maganar ita ta tsaya mata a rai sosai inda shed’an kuma ya rad’a mata tashi hud’ubar a kunne, juyowa tayi da sauri wajen mutumin ta same shi yana shirin tashin motonshi, tana zuwa yace “Ke ya dai, me kika dawo yi?”

“Na yarda.” Abinda ta fad’a kenan, kuma wannan kalmar ita ce duk wani makulli na ruguza rayuwarta, shi dai dama d’an tasha ne na gaske, yana d’aukarta daga nan wata unguwa ya nufa da ita inda matattara yan bariki ne, *kara*, wani fili ne da duk wata karuwa ko karuwi ke zama anan, suna zuwa ya abka da ita wata bukka dan dama ba d’akunan basa wuce na kara, saida ya fara cika mata cikinta da gasasshen nama tasha ruwan rada sannan sukayi abinda ya kawo, farkon al’amarin Husseina taji wani iri da ita ga matuk’ar kunya data hanata katab’us, amma bayan komai ya kammala ta kalleshi take shed’an ya cire mata duk wata kunyar da take da ita.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231 232 233 234 235 236 237 238 239 240 241 242 243 244 245Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected