BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL
*Wani* k’akk’arfan nishi ta sauke mai tafiya da numfashi, hannayenta gaba d’aya ta luma kan damatsanshi wanda yasa faratunta shigewa sosai a damtsen shi, idonta rufe suke ruf sai kai da take girgizawa hawaye na fitowa a idonta suna bi ta bayan kunne, Inna lillahiwa’inna ilaihi raju’un da kalmar shahada ne a bakinta, zafi ne mai tafiya da k’walwa, lokaci d’aya taji shigar abinda ba tayi tsammani ba, abu ne da bata isa ta kwatanta girmansa ba, ita dai tasan a lokacin daya shiga ne ruhinta ya bar gangar jikinta, mamakinta d’aya shine yanda akayi take motsi bayan kuma tasan gawa bata motsawa. Babu alamar raguwa sai k’aruwa da rad’ad’in keyi, dan haka ta sake lik’e idonta sosai ta cije leb’enta na k’asa tana jan hannunta kan damtsenshi, hakanne yayi sanadiyar fitar da jini daga damtsenshi saboda kaifin akaifunta masu d’an tsayi saboda gyaran da aka musu saboda bikin, tumurmusa kanta kawai takeyi tsakiyar tattausan pillown, inda take ta yin sama tana son zamewa amma sai k’ara lik’e mata yake.
Duk abinda ke faruwa bai sani ba, abinda ke zautar da tunaninshi kawai yake son yaji ya samu sauk’inshi, amma abun ya ci tura sai k’ara lik’ewa yar mutane yake, ba ita ba da a jikinta suke shi kanshi da yake tsutsarsu har bakinshi yayi zafi, ya gyara kwanciyar yafi kala hud’u duk dan yana so ya hutar da ita, amma ya jarabar ta k’i kwantawa, a daidai lokacin da yaji zafin yaginshi da tayi a lokacin yayi wata zabura ya sake k’amk’ameta yana wani jijjiga yana k’ara shiga jikinta, daga haka kuma sai yayi sanyi zufa ta keto mishi lokaci d’aya, gefenta ya fad’a yayi ruf da ciki yana sauke numfashin samun nutsuwa, ya jila haka kafin ya iya d’aga kanshi ya kalleta, ganin kanta na kallon gefe d’aya yasa hannu ya juyo da ita, murmushi ya saki ganin har yanzu idonta rufe suke, yunk’urawa yayi ya sauka daga kan gadon ya d’auki gajeran wandonshi ya mayar ya shiga ban d’aki.
Zaune ta mik’e tana cije leb’e, saida taji ta wartsake kafin ta tashi ta d’auki kayanta tayi saurin barin d’akin kafin ya fito, tana zuwa d’akinta ban d’aki ta shiga ta saka rigar wanka sannan ta fito, madafa ta shiga ta dafa ruwan zafi masu yawa kafin ta juye a bokiti ta shiga dasu d’aki, tana shirin shiga ban d’aki taji ya shigo d’akin, garin saurin shigewa ban d’akin yasa bokitin ya bugi k’ofar ban d’akin ruwan suka zuba a k’afarta, sakin bokitin tayi tare da sakin k’ara lokaci d’ayakuma take furta Inna lillahi wa’innailaihi raju’un, da gudu ya k’araso ya fitoda ita yana kallon fuskarta cikin fad’a yace “Meye haka? Kina haukane? Wa yace ki fito daga can?”
Hijabinta tasa tana goge hawaye, tausayinta ne yasa shi rumgumeta yana shafata yace “Yi hak’uri to, amma me yasa kika taso? Ba zaki iya kula da kanki ba, ko baki yarda dani bane?”
Girgiza kai tayi dan haka ya kama hannunta suka shiga ban d’akin, da kanshi ya had’a mata ruwan ya kalleta yace “Zaki iya ko na taimaka miki?”
Girgiza kai tayi alamar a’a, barinta yayi ta gyara kanta tsawon lokaci kafin ta kammala ta fito, kwantar da ita yayi yaja mata bargo, kallon fuskarta yayi yana murmushi mai tsadar gaske yace “…
*Comment*
*Alhamdulillah*
14/10/2020 à 00:58 – Ummulkhairi: ❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️
*BADAK’ALA*
❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️
*Labarin Gaske*
*NA*
_SAMIRA HAROUNA_
*Litattafan marubuciyar*
*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D’AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD’I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K’ADDARARMU_
*8* _K’ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k’ura)…_
*14* _BADAK’ALA…_
*SADAUKARWA GA*
_*AHALI NA*_
*TAURARIN NIGER*
“`(Tsintsiya mad’aurinki d’aya)“`
✪{T . N}✪️
https://www.facebook.com/101305508365889/posts/101311008365339/?substory_index=0&app=fbl
_Bismillahir rahamanir rahim_
_42_
“Nagode, aljannata.”
Murmushi ta masa mai tafiya da imanin mutum kafin ta fara lumshe ido, sumbatar goshinta yayi tare da gyara mata bargon sannan ya kwanta gefenta, bata jima ba bacci yayi awon gaba da ita, amma shi bai samu damar yin baccin ba sai durmiya da yayi tunanin rayuwa a sanda yake wanke zanin gadon da yaji matsa shi kanshi, yana wankin yana tunanin waccen ranar ma da halak d’inshi ce da shi zai wanke zanin nan, amma baisan waya wanke ba tsabar masifa. Yasan da babbar matsala a gaba idan asirin abinda ya aikata ya fito, amma a shirye yake da duk wanda zai tuhume shi, yana da hujjjojin kare kanshi ko da ba’a gamsu ba. Ko ya take? Ita ce tambayar daya ma kanshi, nan ma zurfafa tunani yayi sai yaga watak’ila tafiyartata zama alkairi a gare shi, tunda ya auri k’anwarta, hakan zaisa ya mayar da hankalinshi kan matarshi. Amma me yasa Ummy ta shiga firgici sosai daga yana son duba kankana? Me yasa daya anbaci ciki duk suka rud’e kamar dai cikin ne da ita? Akwai wani abu! Shine abinda zuciyarshi ta fad’a masa, da wannan tunanin bacci b’arawo yayi gaba dashi.
Tun *08:00* na safe colonel ya gama haramar tafiya shi da yaranshi masu tsaron lafiyarsa, yayi sallama da kowa sannan ya fito, a lokacin Ammar ya zo sukayi sallama, colonel zai shiga mota mai gadi ya taho da sauri ya gaishe shi, amsawa yayi kafin ya mik’e daga rusunawar da yayi ya bawa Ammar wata takarda yana fad’in “Wannan wani ne ya bayar yace a baka.”
Karb’a yayi ya bud’e ya fara karantawa ba tare da yace mishi komai ba, wani shegen murmushi ya saki kamar an bashi katin shiga aljanna, ganin haka yasa colonel tsayawa yace “Yaro na ya dai? Lafiya ko?”
Ba tare daya daina wannan murmushin ba ya kalleshi yace “Lafiya lau tonton, wani k’aramin d’an daba ne zai min iskanci, amma zan nuna mishi na fishi iya buru’uba.”
Yana fad’a ya tunkari hanyar komawa b’angaren shi yana fad’in “Za muyi waya tonton.”
Cike da bala’i colonel yace “Da kyau yaro, karka ragamar duk uban da yace zai taka ka, a shirye muke muyi shari’a da uban ko waye, kaje Allah ya tsare.”
*Da sannu halin kowa zai fito*
Yana shiga d’akinshi ya wuce ya d’auko makulin mota da wayarshi ya fito, ba dan ta fito daga d’akin ba a lokacin da ba zata san fitarshi ba, amma yana ganinta saiya jawota jikinshi yana kallon fuskarta yace “Matarmu zan fita, ki kula da kanki sannan ki ci abinci idan kin dafa, karki saka dani kuma karki jirani, ba zan dawo da wuri ba.”
Tsoro ne ya fara bayyana a fuskarta tace “Lafiya yah Ammar? Ina zaka je?”
Shafa kumatunta yayi yace “Ba komai, zan dawo amma ba da wuri ba.”
Yana fad’a ya saketa ya tunkari k’ofa kamar zai tashi sama, da kallo ta bishi sai gabanta da taji yana d’an fad’uwa, ba komai ta gani a idonshi ba sai bala’i, tana jin tsoron amsa gayyatar katin masifa ne yayi daga gurin wani, ita kam ina zata saka kanta da tashin hankalin bawan Allahn nan? K’arasawa tayi ta zauna kan kujera ta zuba tagumin zaman jiran tsammani. Jikinshi har rawa yake ya matsu ko ya isa ofishin, tunda ya cije leb’e ya kasa sakinshi sai k’yaci da yake yafi dubu, to wai shi Jano zaiyi k’ara? To ai ya ma raina masa hankali da baiyi k’ararshi wajen sojawa ba ko jendarme, sai wajen masu saka kakin police, jar uba! Da wannan bala’in ya isa wurin har gaban inspecteur d’in daya shirya sulhunta tsakaninsu da kanshi, dan baya so rikicin yayi girman da sunan gidan Gaga zai b’ace.