BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL
Tattare rigarta tayi ta tafi a guje, takon da baifi uku ba ya rik’o wuyan rigarta da k’arfi yayi baya da ita, k’ara tayi wacce tasa Hajia k’arasa bud’e idonta ta kallesu, hannu ya d’aga da niyyar kasheta da mari, amma me sai yaji ba zai iya tab’a lafiyar jikinta har haka ba, tsaki ya ma kansa kafin yasa k’arfinsa ya damk’i gashinta yana fad’in “Sa’anki ne ni?”
K’ara tayi tare da rintse ido tana k’ok’arin cire hannunshi a kanta, hannu ya d’aga kamar zai mareta, da sauri ta rik’e k’afarshi cikin kuka tace “Yi hak’uri to zanyi, zan zuba, zan zuba wallahi, dan Allah yi hak’uri.”
Da k’arfi yace “Tashi to.”
Tashi tayi ta dawo inda ta aje kwanukan ta fara zubawa, saida ta gama ta mik’a mishi tace “Gashi.”
D’aga idonshi yayi ya mata wani kallo yace “Aje a kaina.”
Saida ta turo mishi baki kafin ta aje gefen gadon, juyawa tayi saida ta bud’a k’ofar tayi shirin rufeta sannan ta zuro kai tace “Allah ya saka min cutar daka min.”
Tana fad’a ta ari na kare, cikin nutsuwa ya bita da kallon rashin fahimta, cutar daya mata? Wace cutar kenan? Abinda ya faru baya ko kuma yanzu? Tab’e baki yayi ya mik’e ya kama Hajia ta tashi, saukowa tayi daga kan gadon yana rik’e da hannayenta, ta mik’e tsaye Zeituna ta shigo da sallama, da sauri ta k’araso tana kwance goyon Fatima ta aje kan gadon tace “Yah Ammar bari na kaita.”
Sakinta yayi suka shiga ban d’aki shi kuma ya d’auki Fatima yana mata wasa, baki kawai ta wanko ta fitota koma ta zauna, ita ta zuba abinci ya bata da kanta ta ci tasha lemu, maganin ya bata ta bata sannan yace ta d’an zauna, amsar Fatima tayi suka fita dan aikin gabanta, kallonta yayi shima yace “Hajia nima zan tafi asibiti yanzu, dan Allah kada kiyi wasa da magunan nan.”
Ya fad’a yana nuna mata su, juyawa yayi zai fita tace “Ammar zo.”
Juyowa yayi ya tsaya ta nuna masa kusa da uta tace “Zauna mana.”
Zaunawa yayi yana kallonta, saida ta sunkuyar da kanta tace “Ammar tun yaushe kasan da haka kuma baka fad’a ba kowa ya ji?”
Da mamaki ya kalleta yace “Subhanallah! Hajia na fad’a? Na fad’a ma wa to?”
Kallonshi tayi tace “A gani na k’iyayya na nuna maka, shiyasa nake tunanin ko zaka iya fad’a dan ka kunyata ni.”
B’ata fuska yayi yace “Haba Hajia, ke fa kakata ce wacce ta haifi abun tutiyata, taya zan miki haka? Hajia duk abinda kike min gaskiya ne ina jin zafi a zuciyata, amma kuma bana rik’e ki ta yanda har zanyi tunanin d’aukar fansa a kanki ko kunyata ki, Hajia duk da kina fad’a min gaba da gaba cewa baki sona ni ban tab’a yarda ba, abu d’aya da nayi imani dashi shine babu wanda zai k’i nasa sai dai ya k’i wani halinsa.”
Jinjina kai tayi alamar gamsuwa kafin tace “Tun yaushe kasan da maganar nan Ammar kuma kayi shiru?”
Murmushi yayi yace “A k’alla wata goma yanzu, wani dare ne naji yana fad’a tsakaninshi da mahalincinsa, dare ne da ni kaina ya shiga cikin tarihin rayuwata, domin abinda ya faru a daren bayan naji abinda ya fad’a ne ya tabbatar min da lallai duk abinda magabatanmu suka aikata yana iya dawowa kanmu, sannan na tabbatar da abinda ya fad’a miki yanzu cewa dole sai kin tuba Hajia, inba haka ba akwai wasu abubuwan da zaki k’ara ji nan gaba wanda a gaskiya zasu iya k’arasaki ga kushewarki.”
Abun mamaki da al’ajabi, abunda ko a mafarki baiyi tsammani ba shine ya faru, Hajia Zeeya’atu, Hajia dai sarauniyar izza ji da kai tak’ama da alfahari, ita ce wai ke kuka da idonta tana rik’e hannunshi tana fad’in “Ammar ka fad’a min dan Allah me yake faruwa a cikin iyalina? Ammar na fara jin tsoro, sai nake ganin kamar shashashar uwa ce ni.”
Da sauri yace “A’a Hajia, ke uwa ce tsayayya kan iyalinta, Hajia akwai wuya samun uwa kamarki, ba kowace uwa bace ke tsayawa har kan tarbiyar jikokinta ma bayan ta tarbiyaccin ‘ya’yanta, kawai dai yar matsala ce aka samu daga wani wurin.”
Ba tare data saki hannunshi ba tace “Ka fad’a min Ammar idan kasan wani abu dake faruwa, dan Allah ka fad’a min kaji.”
Girgiza kai yayi yace “Hajia bana so hankalinki ya sake tashi, k’azantar da baki ganta ba kuma baki jita ba tsabtace a gareki.”
Cikin kuka mai matuk’ar nuna nadama tace “A’a Ammar ka fad’a min zan d’auka, zunubi na ne bai kamata ya shafeku ba, nayi alk’awarin tuba ga Allah abisa cin amanar mahaifina da nayi da kuma zina, zan rok’i Allah ya yafe min zubar da cikin dana tab’a yi, dan Allah ka fad’a min Ammar ko zan samu na nemi iyalina gafara.”
Da k’yar ya iya b’oye tashin hankalinshi da tsoron al’amarinta, shi bai ma san ta zubar da ciki ba sai yanzu, lallai abun azimun ne, shirun da yayi yana kallonta yasa ta kalleshi tace “Ammar yanzu ne na fahimta banda masoyi a duniyar nan sama da kakanka, ashe duk yasan da abun nan kuma bai tab’a nuna min ko ya fad’a min ba, duk irin rashin mutumci da wulak’anci dana masa…”
Kuka ne ya k’wace mata ta sunkuyar da kai tana kuka, saida ta nutsu ta d’ago tace “Da wane ido ne zan dinga kallonshi yanzu, Ammar babu irin k’ask’ancin da ban mishi ba a rayuwa, a rayuwar aurenmu nasan akwai lokacin da yayi farin ciki, amma bak’in cikin da yayi ya ninka farin cikin sau ninkin ba-ninkin, duk da yasan lagona yasan makullin ruguza duk wani gidan rashin mutumcina amma bai bud’e ba, Allah sarki bawan Allah, wannan dalilin ne yasa nake k’ara son shi kullum, *hak’uri*, yana da matuk’ar hak’uri.”
Murmushi yayi yace “Hakane Hajia, amma ki gode Allah da yasan kika fahimci haka tun dukanku kuna raye, kinga kenan akwai damar neman yafiya da gyara kuren gaba.”
Kallonshi tayi tace “Hakane Ammar zanyi, amma dan Allah ka fad’a min idan kasan akwai wani abu daya kamata na sanshi?”
Shafa gemunshi yayi yana nazari, sake matsowa yayi kusanta ya rik’o hannunta yana kallon idonta cikin bin kowace kalma daki-daki yace “Hajia, bansan komai a game da kowa ba sai wanda ke fitowa yanzu, kaina kawai na sani.”
Bakinshi ta k’urawa ido tana kallo kamar mai son fahimtar yarenshi tace “Ka aikata wani abu ne kai ma daya kamata na sani?”
A hankali ya jinjina mata kai alamar eh ba tare daya rusuna idonshi daga kan fuskarta ba, cikin zak’uwa tace “Meye? Me ka aikata Ammar? Kenan pentina ya shafeka?”
Kai ya fara jinjina mata tare da cewa “Eh, Hajia nawa yafi na kowa muni, kowa abun bai faru dashi da wani na shi ba, amma ni da yer uwata haka ya faru, wacce muka tashi tare uwa d’aya ta rainemu, da ita d’in ma hakan ya faru ne a d’akin uwata mahaifiya.”
Yanda suke kallon juna kai kace basa gane yaren junansu, cikin mamakin dake son kasheta tace “Wa kenen? Ka fad’a min kaina ya kulla na gaza tuna komai.”
Marairaicewa yayi yace “Wallahi Hajia tsautsayi ne da kuma k’addara, ban shirya yin hakan ba, banyi niyyar yin hakan ba kawai aikatawa nayi.”
Fahimta da tayi yasa ta kafeshi da ido tace “Hamna ko Amna?”
Saida yayi k’asa da idonshi yace *”Hamna.”*
“Inna lillahi wa’inna ilaihi raju’un! Hasbunallahu wa ni’imal wakil.”
Wani irin kallo ta masa taja baya sosai tace “Wallahi Ammar ba dan kana d’aya d’aga cikin wanda suka min sanin shanu ba da yau saika raina kanka.”
Sunkuyar da kai yayi baice komai ba, d’auke kanta tayi daga gareshi tace “Jikana da jikanyata? A cikin gidana suka aikata zina? La’ilaha illallah.”
Jujjuya kai ta dinga yi tana ta fafutakar saita nutsuwarta, kallonshi tayi ta mik’e tsaye da duka sauran k’arfin daya rage mata ta gaura masa mari a kumatun dama tace “Kasan kayi wannan ta’asar akan me ka yarda aka aura maka yer uwarta? Kai wane irin shaid’ani ne Ammar, kayi tarayya da babba kuma kayi da gaba d’aya tazarar lokacin dake tsakaninsu bata wuce minti biyu zuwa uku ba.”