BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL
Matsowa tayi ta d’an sunkuya tace “Ina kwana Hajia.”
Ba annuri a fuska tace “Lafiya lau.” Mik’ewa yayi yace “Kewace irin gaisuwa ce haka? Dallah malama haka zaki mata, rumgumeta zakiyi, ina so kema ki zama mafi soyuwa a zuciyarta kamar yanda tafi so na sama da kowa.”
Da k’arfi ya jawo Amna ya tallabo Hajia ya mannesu wuri d’aya yace “To rumgumeta ki sumbaci kumatunta.”
*Covid19 inji aunty*
Amna dake jin abun wani iri kasawa tayi, Hajia kuma sai k’ok’arin tureta take kamar kashi tana fad’in “Kai kana da hankali kuwa?”
Bata ankara a sunkuyawar nan da tayi sai kuwa ya sauke mata k’ulli a baya yana fad’in “Ke dan ubanki rumgumeta.”
Bata shirya ba sai kuwa ta fad’a kan Hajia da k’arfi tana sakin tarin da bata shirya zuwanshi ba, da sauri ta rumgumeta ta raba jikinta da nata tana dafe bayanta tana kallonshi, yanda duk ta shagwab’e fuska kuma saita kashe shi a wurin, take ya jawota ya rumgume kuma yana shafa mata bayan yace “Yi hak’uri kinji chouchouta (shoushouta), kin yafe min ko.”
D’aga kai Amna tayi ta raba jikinta da nashi saboda fitowar iyayensu, kafin su gaisa kuma Marya suka shigo ita da Junaid.
*Alhamdulillah*
*Yawan sharhi yawan rubutu.*
14/10/2020 à 00:58 – Ummulkhairi: ❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️
*BADAK’ALA*
❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️
*Labarin Gaske*
*NA*
_SAMIRA HAROUNA_
*Litattafan marubuciyar*
*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D’AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD’I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K’ADDARARMU_
*8* _K’ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k’ura)…_
*14* _BADAK’ALA…_
*SADAUKARWA GA*
_*AHALI NA*_
_44_
Ko da ta gaishe da kowa ya amsa da sakin fuska amma banda Zeinabu da Hajia, Amar ne suka shigo shima tare da Umaimah, gaisawa akayi sosai inda Hajia ta zaunar dashi kusa da ita tana ta mishi tambayoyi kamar yaro, shi kuma duk a takure yake jin kanshi a kusa da ita, kallon Umaimah tayi tace “Zo.”
Kusanta taje ta zauna kanta k’asa, saida ta kalleta ta nuna shi da yatsa tace “Kinga wannan? Shine farin ciki na, kiyi iya k’ok’arinki wajen faranta masa rai, ni kuma na miki alk’awarin duk abinda kika nema a wajena zaki samu, kinji ko?”
Kai kawai ta d’an d’aga alamar to, Alhaji ne ya shigo da sallama da farin ciki a fuskarshi na ganin ahalinshi, nan ma wata gaisuwar ce ta b’arke tsakaninsu kafin ya kalli kowa yace “Masha Allah, tunda kusan duk mun taru muje mu ci abinci tare mana.”
Duk da akwai wanda basu buk’atar cin abinci amma basu mishi musu ba sun nufi kan babban teburin, Amar da Hajia ke rik’e da hannunshi yana son ya sub’uce amma ta rik’e, ta bayanshi Ammar ya mazge mishi k’eya yana fad’in “Jiya kaine ka hareri ni ko?”
Dafe kai yayi yana kallonshi, a hassale Hajia tace “Ammar meye haka? Zan ci uwarka fa.”
Ganin ko kulata baiyi ba yasa tace “Yaje ya hararekan to mugu mak’etaci.”
Duk uwayen kowa ya samu ya zauna sai kuma matasan maza, su Amna kuma su suka zuzzuba abinci, ana fara cin abinci Ammar ya kalli Amna ya mik’e tsaye da farantinshi a hannu ya zagaya har inda take, kama hannunta yayi suka nufi hanyar d’akin Ummy yana fad’in “Aljannata zo muje d’akin Ummy na ciyar dake.”
Rufe baki Amar da Jibril sukayi suna dariya, sai Junaid daya bishi da kallo yace “Bak’auye anyi agogo.”
Saida ya wani sassako wandonshi yayi k’asa kamar yanda gayun nan keyi kafin su waye yace “Dole mana, mata wasa ce, ita ce mahutata dole na kula da ita.”
Jibril zaiyi magana yana dariya Ummy ta kalleshi tace “Dan Allah ku rabu dashi, kada kusa muji abinda kanmu ba zai iya d’auka ba.”
Ba tare daya daina tafiyar shak’iyancin nan ba har suka shiga d’akin Ummy su dai suna binsu da kallo, suna kammala cin abincin suka fito, kusa da Amar ya tsaya yace “Yaro tashi muje ka sauke ni, banda mota a hannu.”
Kallonshi Ummy tayi kamar tayi magana sai kuma tayi shiru, Hajia ce tace “Halan ka siyar da motar?”
Kallonta yayi yace “To Hajia idan rashin kud’in ne zaisa na siyar da uwar gidata ai ina ga kina da kadarori ajiye, ko sark’ok’in da kike sakawa ma kad’ai sun isheni rayuwa idan na siyar.”
Wani kallon sai dai haushi ta masa tace “Dad’inta dai gadar arzik’in nayi tun daga gida, a sanda mahaifina yayi zamaninsa babu wanda bai san shi ba.”
Murmushin gefen labb’a ya mata yace “Yanzu? Ai har yanzu mu yana zamaninshi a wurinmu, tunda Alhaji ya fad’a mana duk shine silar arzik’in nan da muke ciki, da taimakon Allah da taimakonshi da yyanzu watak’ila muna can anata fama.”
Wani murmushin jin dad’i tayi ance arzik’i daga mahaifinta ya fito tayi, yana kallonta saiya bushe da dariya yana fad’in “Kinsan wani abu Hajiata, Allah sai naga k’aramin bakinki nan na ki zaiyi mugun kyau idan kina yanko lomar tuwon dawa kina shinfid’ata kan miyar daddawa kina jefawa baki.”
Wata irin tattausar dariya Alhaji yayi yana kallonta yace “Ai kuwa saima ka gani da idonka, abun sha’awa ne sosai, gata kuma gwanar iya tuk’a tuwo yayi taushi laushi da santsi.”
Wannan karan kusan babu wanda baiyi dariyar ba sai Hajia da ranta ya b’ace ta kalli Alhaji, sama da k’asa ta harare shi sannan ta ci gaba da cin abinci ta, Ammar dake dariya har da rik’e ciki ne ya kalli Amar yace “Kai nake jira.”
Lieutenant ne ya d’auki makullin motarshi ya jefo mishi yana fad’in “Je da wannan.”
Cab’ewa yayi yace “Abba kai fa?” Kallon Amar yayi yace “Shi saiya kaini.”
Bai ce komai ba ya zagaya wajen da Hajia ke zaune ba tare data kula ba taji ya sumbaceta a kumci yana fad’in “Uwar gidana saina dawo.”
Kusan Husseina yaje ita ma ta samu nata rabon tare da cewa ” ‘Yar tsakiya kenan mai ban haushi.”
Saida yaje har inda take tsaye ita ma ya sumbaci kumcinta yace “Wannan ce amaryata.”
Kusan lieutenant ya tsaya ya sunkuya ya mik’o mishi kumatunshi alamar ya sulbace shi, saida ya kalli Ummy da Hajia da sauran mutanen wurin wanda suma duk idonsu akansu suke, yana kallon Zeituna ya fahimci ma’anar kallonta sai kawai ya danna mishi wata k’aramar sumba a kumci, mik’ewa yayi daga sunkuyawar yace “Abba baka ce komai ba.”
Kallonshi yayi to shi me zai ce? Saiya tuna da jiya sai kawai yace “A dawo lafiya.”
Murmushi yayi sosai yace “Nagode Abba na, kai bai ma ka dawo lafiya.”
Zeituna ya kalla yace “Uwata saina dawo.”
Da murmushi a fuskarta tace “A dawo lafiya, Allah ya bada abinda aka je nema.”
Murmushi ya mata yace “Nagode.”
Ummy ya kalla, ido cikin ido, kallo mai ma’anoni da dama mai wuyar fassara, ba tare daya daina kallonta ba ya wuce yana dank’ara gilashinshi a fuska wanda ya fito mishi da manyan fararen idonshi. Haka kawai ta samu kanta cikin yanayin rashin jin dad’i, ta kasa d’auke ido daga gare shi har ya fita, kowa ya ma magana banda ita, har gaisawa da akayi tun a falo bakinshi bai had’u da nata ba, tana kallo sai wata ya kira da sunan uwa ba ita ba, sai taji kamar tayi ihu ko wani ya tambayeta lafiya har ta fad’a mishi abinda ke ranta, a hankali ta dawo da kallonta kan farantin abincinta, amma sai taji ya fita a ranta sai kawai ta mik’e zata bar wajen, idonta ne suka sauka kan Zeituna da ita ma a lokacin ta kalleta ganin ta tashi, had’e mata fuska tayi tare da jan dogon tsaki wanda bata san ma ya fito fili ba ta bar wajen.