BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL
Bai wani damu ba dan in bai d’auki wayar ba dama text ake turo mishi, ana sake kira ya d’auka ya kara a kunne, muryar Ma’arufa ce a kunnenshi tana fad’in “…
*More comment plsss*
16/06/2020 à 13:22 – Ummulkhairi: ❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️
*BADAK’ALA*
❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️
*Labarin Gaske*
*NA*
_SAMIRA HAROUNA_
*Litattafan marubuciyar*
*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D’AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD’I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K’ADDARARMU_
*8* _K’ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k’ura)…_
*14* _BADAK’ALA…_
*SADAUKARWA GA*
_*AHALI NA*_
*TAURARIN NIGER*
“`(Tsintsiya mad’aurinki d’aya)“`
_Bismillahir rahamanir rahim_
_16_
“Iya wani zunubi zuciyata ta aikata wanda ko a mafarki bai dace ace nayi ba bare kuma a zahiri.”
Dafe k’irji Iya tayi tace “Ke ‘yar nan! Me kika aikata haka? Allah yasa dai ba wani mummunan bai abu kikayi ba.”
Alhaji da farko juyawa yayi tunda yaji tace sirri ne kuma bai kamata ace yaji ba, amma jin tace zunubi kuma saiya dakatar da shi, *zuciya* kuma *zunubi* murmushi yayi ya tsaya dan yasan duk inda zancen zaije ba zai wuce maganar soyayya ba, sai dai yana so yaji meyasa matashiyar ke tunanin zunubi zuciyarta ta aikata? Ko dai irin *wahalalliyar soyayyar* take? Soyayyar da babu sakamako mai kyau a cikinta saina wahala da dakon abinda baya anfanar da gangar jiki bare ita kanta zuciyar, dan haka ya tsaya dan jin matsalarta.
Kallonta tayi a marairaice tace “Iya mummunan abu ne kam, dan idan akaji zata min alawadai, wasu kuma zasu min dariya saboda ganin matsayina bai kai can ba, kuma nima nasan da haka Iya, jarabawa ce kawai wacce take neman tafi k’arfi na.”
Cike da tsoro Iya ta dafata tace “Zeituna, a sanin dana miki ba kya da wasu miyagun halaye, amma maganganunki sun d’ugunzuma tunani na zuwa kwokwonto da son jin zunubin da kika aikata, fad’a min wane irin zunubi ne wannan.”
Cikin zubo da hawaye tace “Iya na kamu da so, son wanda bai kamata ace na kamu da son shi ba, son mutumin da ba zai tab’a kallon ko da fuskata ba bare ya ji wani abu mai kama da so a zuciyarsa a game da ni, son mutumin da ko da ace ‘ya ce ni mai gata yafi k’arfi na saboda wasu dalilai, Iya bansan ya zanyi ba dan Allah ki bani shawara?”
Cike da kulawa ta kalleta tace “Zeituna har yanzu a duhu kike saka ni, ki fito ki fad’a min matsalarki, kin manta na fad’a miki ke kamar ‘ya ce a gurina?”
Gyad’a kai tayi alamar eh kafin Iya tace “Dan haka Zeituna karki sare, ke fa ‘ya mace ce, kina da damar da zaki so kowa kuma kowa ma ya so ki, karki k’ask’antar da kanki har ki dinga ganin baki dace da samun soyayyar wani d’a namiji ba, ke nifa na yarda da yata wallahi, tsaye da kyau haka zaune da kyau, har waye zai ce ma baya sonki? Ai ki k’addara koma waye to shi yayi babban dace da har samu nasarar samun soyayyar ki, dan haka fad’a min naji waye shi?”
Cikin murmushin jin dad’i na yabon da Iya tayi mata ta kalleta sororo tace “Iya Abban Ammar ne, mijin aunty Sa’ada, lieutenant Hassan Gaga.”
Har gaban Iya saida ya fad’i a wurin, zaro ido tayi lokaci d’aya kuma dan karta sanyaya mata gwiwa taji ba dad’i sai kuma ta wayance tace “Haba dai? Dama ai na fad’a miki koma wanene shi yayi dace ba ke ba, ke baki ga banbancin dake tsakaninku da shi bane?”
Da mamaki Zeituna ta kalleta tace “Wane irin banbanci Iya? Lieutenant fa nace miki na gidan nan, mahaifinsu Ammar.”
Da yar harara ta bita irin ta yo shi d’in fa kafin tace “To sai me? Tabbas yana da kud’i da kuma ilimi, amma duk da haka akwai abinda ke ma kika fishi.”
“Me kenan Iya? Cewar Zeituna da har yanzu take mamaki.
Murmushi Iya tayi tace “Kin fishi k’urucuya, Zeituna ke yarinya ce shi kuma tsoho, hakan zaisa ba zai iya juyawa soyayyarki baya ba.”
Rufe ido Zeituna tayi irin wai kunyar nan tana fad’in “Kai Iya, Allah ba tsoho bane.”
Waro ido Iya tayi tace “Iyeeh! Kaji min yarinyar zamani ko, to zan gani idan ba tsohon bane.”
Had’e murmushin kan fuskarta tayi tace “Iya zan bar garin nan.”
“Me? Barin gari? Meyayi zafi? Ke duk zafin soyayyar ne? Zeituna karki halaka kanki mana, ki bi komai a sannu kina kai kukanki wajen ubangiji, nima zan tayaki da addu’a.” Duk iya tayi maganar ne tana kallonta.
Girgiza kai tayi tace “Iya ba wannan bane matsalar, matsalar kawu Mamu ce.”
Nan ta kwashe komai ta fad’awa Iya wanda taji suna tattaunawa, kuka take sosai Iya na rarrashinta da cewa tayi hak’uri kar tayi saurin barin gari tunda babu inda zata je, sun jima nan zaune suna tattaunawa har Alhaji ya bar wurin cikin matuk’ar sanyin jiki, d’akin baccinshi ya shiga ya zauna kan kujerar da bata da maraba da gado yana tunani, hak’ik’a *so* wani abu da babu wanda ya bari, babu ruwanshi saiya shiga zuciyar babba komai girmansa ya kuma gaura shi a k’asa, haka kuma ya shiga zuciyar matashi komai k’uruciyarshi yayi maganin wautarshi da rashin hankalinshi, tunanin Zeituna da halin da take ciki ne ya tsaya masa a rai, kawun ta? Amma baya tsoron mahallicinsa? ‘Yar d’an uwanka zaka nemi ka jefa rayuwata a harkar karuwanci? Da wannan tunanin Alhaji ya jima zaune ya kasa yin komai har saida ya samu tsayayya kuma gamsashiyar shawara sannan ya mik’e ya shiga wasu harkokin.
Da safe bayan sun karya Hajia tace lieutenant ya kira colonel ya sanar da shi gobe zasu je Goure neman auren Maryama, haka kuma ya kira gwamna ya sanar dashi an tsayar da auren ‘yarsa Amna, yanda tace haka yayi hakan yasa colonel daya samu sararin aikin kiran da aka mishi ya d’auko mota ya kamo hanya tare da masu tsaronsa a biye da shi.
♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡
Tunda suka je asibiti ko aiki ya had’a su Ummy ta k’i yarda ko ido su had’a, ya fahimci hushi take dashi abinda ya tsana kenan a duniya, yawan sakawa Ummy na fushi dashi yasa yake k’ara jin haushin Hajia shima, har lokacin tashin shi yayi ya shirya ya fito, har zai wuce ta gaban d’akin inda ake kwantar majinyata saiya hangeta tana cirewa tsohuwar da yasa a kwantar da ita saboda tana neman agajin gaggawa, turo k’ofar yayi ya shiga babu sallama, juyowa Ummy tayi tana ganinshi ta d’auke kai, amma saboda dokar aiki da kuma ba kowa yasan d’a da uwa bane yasa cikin dakakkiyar murya a harshen fransanci tace “Docteur har ka fito? Na ga lokaci ya d’an ja kuwa.”
Saida ya kalli robar ruwan ya kalli tsohuwar ya zauna bakin gadon kusa da tsohuwar yana kallon fuskarta yace “Kaka ya jikin naki?”
Kallonshi Ummy tayi, wato ba zai kulata ba dan ma ya samu ta mishi magana? K’wafa tayi a cikin zuciyarta ta juya da wani d’an kwano kwano kuma shi ba faranti ba a hannunta wanda ake zuba ‘yan magunguna da allurai zata fita, ji tayi yace “Madame jira.”
Tsayawa tayi ta had’e wani abu a mak’oshinta kafin ta juyo da fara’a a fuskarta, a lokacin kuma tsohuwar ta amsa mishi da “Jiki da sauk’i likita.”
Fuskar dai a yabo ba fallasa yace “Ina fatan dai baki manta duk abubuwan dana fad’a miki ki kiyaye ba ko?”
Cikin murmushi tace “Ban mance ba likita.”
Mik’ewa yayi ya dauk’i abun sauraron bugun numfashi ya dinga d’ora mata a k’irji, ajewa yayi akan farantin dake hannun Ummy ya d’auki abun awon hawan jini ya zura mata a hannu ya d’aure mata ya danna wani madanni, nan ma saida ya samu sakamakon da yake buk’ata kafin ya d’an duba idonta, katinta dake aje kusan kanta ya d’auka ya duba tare da wasu yan rubuce rubuce, takardar maganin daya bata tun farko ya sake nuna mata yace “Kaka ki tabbatar an siyo wannan magungunan fa.”