BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL
Komawa tayi ta zauna kan gadon ta kalleshi cike da jin haushi tace “Fitar min a d’aki.”
Mik’ewa yayi ya kalleta yace “Kuyi hakuri Hajia, wannan shine dalilin da yasa duk wanda yayi katob’ararsa yake rufe abarsa, kowa yafi so kiji daga baya yanda zuciyarki zata buga ki mutu kowa ma ya huta.”
Da kallo ta bishi, shima hushi ne yayi shiyasa ya fad’i haka, gajeran tunani tayi sai gata babu buk’atar yin zafi a wannan lokacin, kuma abinda ya fad’a gaskiya ne kawai, cikin taushin murya tace “Dawo nan Ammar.”
Tsayawa yayi daga shirin bud’a d’akin ya dawo ya zauna inda ta nuna masa. Ajiyar zuciya ta sauke mai nauyi ta rik’e hab’a tace “Duk laifina ne da bana iya fahimtar komai, kamata yayi ace na gane yarinyar dake gabana, amma ban gane hakan ba.”
Kallonshi tayi tace “Amma me yasa baka fad’a min har ka bari ka auri yer uwarta kuma? Ai da sai ka auri ita Hamna.”
Kallonta yayi shima yace “Ummy ce matsalar, bata so kowa ya sani sannan ta daina kulani.”
Cikin raha tace “Rabu da ita kawai, yanzu ma karka fad’a mata na sani nasan dai duk nice take jin tsoron kar na sani.”
Rik’o hannayenta yayi yace “Dan Allah Hajia ku gafarce ni ku yafe min, Allah nima ina jin kunyar kaina dan nasan ban aikata daidai ba, ku yanke min duk hukuncin daya dace dani zan d’auka, ba zan ji kunya ko tsoro ba, kuma zan nemi kowa yafiya daga iyayenmu dana zubarwa da mutumci har ita Hamna da kuma Amna.”
Da sauri ta girgiza masa kai tace “A’a Ammar, muyi shiru d’in shi yafi, ka sani a rayuwa akwai abubuwan da ba’a buk’atar su fito fili, yin shirun shine maslaha a yanzu duk da dai nasan akwai ranar da zasu fito, domin kuwa daga yanda yanzu naji sirrin k’uruciyata a wajenka ya tabbatar min babu wani abu fa da za’a b’oye bai fito fili ba, sai dai kafin mu fitar dashi mu fara duba maslahar dake cikin rashin fad’an da kuma fad’an.”
Cikin nutsuwa tace masa “Misali yanzu idan Hazida taji me kake tunanin zatayi?”
Saida ya d’an rarraba ido yace “Ba zata ji dad’i ba Hajia.”
Da hannu ta masa alamar tace “Ba iya rashin jin dad’i kawai ba, hatta zumuncin dake tsakaninta da mahaifiyarku zai lalace, ‘yarta ce fa data haifa kuma su kad’ai gareta, sannan ni kaina zata min alawadai da salon rainon nawa tace shiyasa ban barta da yaranta ba, shin zakaji dad’i idan haka ta faru?”
Girgiza kai yayi a hankali yana d’an shigar da leb’enshi na k’asa cikin baki, d’orawa tayi da ” Sannan ka duba al’amarin ta b’angaren yer uwarta da kake aure, Ammar ya zakayi ka fahimtar da ita sanda taji? Wane irin gamsashen bayani zaka mata?”
Shiru yayi yana d’an girgiza kai, shi fa bai tab’a tunanin yanda Amna zatayi ba idan taji, kawai a yanda ya tsara ko da abin ya fito kowa yaji zai murje ido ne ya tsula tsiyarshi dole kowa ya shafa mishi lafiya, Amna kuma daya bubburma mata ashar tare da mahaukacin mari dole ko mafarkin yi mishi iskanci tayi sai tayi addu’ar tsari ta juya kwancinta, kamar Hajia tasan me yake tunani sai kuwa tace “Kasan adadin kishin matarka? Ammar kasan suffar da mace ke zama yayin data rikid’e sakamakon kishi? To ko da wasa ne ka jaraba ka gani, wannan mai tsoron na ka kamar mutuwarta zata kalleka ido cikin ido, rawar muryar da take sanda take magana da kai zata rera maka b’acin ranta kamar tana rera k’ira’a, shiru da takeyi sanda ka daketa to ba fa lallai ta iya yin shirun ba, Ammar, a wannan fannin ba lallai ka samu girmamawa daga wajen Amna ba, dan haka shirun nan shi yafi kamar yanda mahaifiyarka tayi.”
Cikin marairaicewa yace “Hajia to dan Allah ki yafe min, idan kika yafe min nasan komai zai zo min da sauk’i insha Allahu.”
Murmushi ta masa tace “Ba komai Ammar na yafe maka, nima ku yafe min kaji.”
“Baki mana komai ba Hajiata.” Ya fad’a da murmushi, kallon agogo yayi da sauri ya mik’e tsaye yace “Hajia zan tafi asibiti yanzu, saina dawo.”
Kai ta jinjina alamar to, tana binshi da kallo har ya fita, yana rufe k’ofar d’akin ya sauke wata ajiyar zuciya mai k’arfin gaske yayin da yaji wani sanyi ya ratsa shi, ita kanta yana fita wani sakayau taji kamar ta rage nauyin wasu kaya data jima tana dakonsu a kanta.
A falon dai ya same su dukansu, saida yaje kusanta ya kalli fuskarta, murmushi kawai yayi yana mamakin taya wannan innocent face d’in zata tabka rashin mutumcin da Hajia ta zayyana masa idan idonta suka rufe akan kishi, yo shi kwarjininshi ma zai barta tayi? Ganin ya tsaya kanta yana murmushi yasa tace “Yah Ammar ya dai?”
Kallonta yayi sai kawai ya had’e girar sama da k’asa ya zama boss ya sunkuya yace “Kalli ido na.”
Bud’a matsakaitan idonta tayi ta kalli k’wayar idonshi, Hamna ma dake gefe tana jin ya fad’i haka ta kalle shi duk da ba ita yake kallo ba, tab’e baki tayi ganin sun k’urawa juna ido. Tana kallon idon nashi tayi saurin sunkuyar da na ta tana dariya tace “Ba zan iya ba yah Ammar, mutuwa zanyi da tsoron abinda nake gani.”
Wani shak’iyin murmushi ya mata ya shafa kumatunta yace “Ki ci gaba da kasancewa haka to ko da ranki ya b’ace a kaina.”
Sumbatar bakinta yayi yace “Ina sonki aljannata.”
“Nima haka.” Ta fad’a tana mayar masa da martani, ta gefen ido ta harareshi ko da taji ya fad’i kalmar, tsaki tayi wanda yasa ya kalleta yace “Yarinya kiyi aure ki rage zafin zuciyar nan, kin ganni nan ba zan fasa abinda nayi niyyar yi ba da duniyata, wannan kayan halak d’ina ne kuma malak, naga wanda ya isa ya hanani yin abinda naga dama.”
A hassale ta kalleshi tace “To ina ruwana, dama na fad’a maka zan hanaka wani abu ne? Su dake halak d’in naka dai kaji da su, wasu ai sun maka nisa.”
Cike da rainin wayo yace “To ina ruwana dana wasu dama? Na ga dai duk abinda ke akwai can shine anan, to miye na k’aryar kuma?”
Ita ma murmushi tayi tace “Banyi musu ba cewa akwai hallitu dayawa da suke iri d’aya da na ta ba, amma bai zama lallai komai ya zama d’aya ba, kamar yanda tasirin ma ba d’aya bane.”
Kallonta yayi da wata fassara a fuskarshi kafin ya kalli Amna yace “Duniyata na tambayeki mana? Yanzu dan Allah sai muka je shago tare muka siyo alawa iri d’aya a ledarta, yanzu zaki yarda na ce tawa tafi taki kyau da dad’i ko kuma ni na yarda idan kika fad’a min haka?”
A tare Hamna da Amna suka ce “Ya danganta.”
“Ya danganta.” Kallon kowace yayi sai Hamna data d’ora da cewa “Ya danganta idan ya zamana ita ta fika jin dad’in abu a bakinta, ko kuma ya zamana dama ta fika son alawar ko kuma ta fika sanin dad’inta, sannan zai iya yiwuwa a lokacin bakinta na da d’and’ano kai kuma naka baya da, ko kuma ya zama wunya take ji wanda hakan zaisa duk abinda ya shiga bakinta ta fika jin armashinshi, dole ko iri d’aya ce wani sai yafi wani jin dad’insa a baki, sann…”
“Ke dallah can ya isa.” Ya daka mata tsawa, hararanta yayi yace “Sai wani maganar jin dad’i da d’and’ano kike, amma dai kin yarda alawar d’aya ce ko? To Alhamdulillah daya zamana komai iri d’aya ne babu wata burga da za’a mana.”
Kallon Amna yayi “Yar banza shine kika shigar mata dan tana yer uwarki ko? Ke baki san bayan miji ake shiga ba.”
Lab’e fuska tayi dan haka ya kalli Hamna yace “Ke rumbud’ed’iya biyo ni na baki sak’o ki kawo ma masoyiyata.”
Kallon juna sukayi a tare, dan haka ya kalli Amna yace “Sak’on soyayya ne zan bata ta kawo miki.”