BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL
Tsaki yayi yace “Ke dan Allah kiyi duk iskancin da zakiyi zuwa jibi ki bar garin nan, na k’osa kud’in nan si shigo wallahi harka ta bud’e, dubi shegiyar katifar da nake kwana akai.”
Sai lokacin ta kalleshi tace “Wai kai yanzu ko kunya baka ji? Kana kwance gida ni ce zanje na nemo maka kud’in da zaka ji dad’in rayuwarka da su.”
Ba tare da damuwa ba yace “To meye a ciki? Ke ma sau nawa ina miki anfani? Yanzu lokacinki ne yayi.”
Tsaki taja ta mayar da kallonta kan wayarta tace “K’aton banza kawai.”
Kallonta yayi amma bai biye mata ba saboda yana wata hira data d’auke mishi hankali, wata budurwarshi ce mai sunan *Meena* ke ikrarin daina harka dashi tunda baya sonta baya kashe mata kud’i, maida mata sak’on yayi da “Rabuwa dani a daidai wannan gab’ar na nufin ke asararriya ce.”
Maido masa tayi da “Sai dai in kaine asararren, shege d’an iska wace tsiyar kake tsinana min?”
Shima mayar mata yayi da “Ke haba matsalata dake banza ce, kanki baya kawo wuta ko kad’an, ina nufin idan kika barni a wannan lokacin to zakiyi asarar wata opportunity da muka samu.”
“Ban gane ba d’an rainin hankali, fahimtar dani?”
Nan ya fad’a mata wai sun samu wani Alhaji gara zasu wanke shi, kuma k’ashin bayan tafiyar abokiyarshi ce Ma’arufa, dan haka karta bari damar nan ta wuce ta, nan dai suka sulhunta komai ya wuce.
♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡
Yanda Abbas yayi tunanin aikin zai kaishi kwana uku sai ya zo da sauk’i, dan haka ya shirya ya taho ba tare daya fad’awa madame ba, su a lokacinsu dare ne dan har sun shiga bacci, saida ya fara shiga wajensu Ammie da suma har sun kwanta ya gaishe su, daga nan kuma part d’in shi ya wuce ya aje jakarshi yayi wanka, kayan bacci ya saka ya feshe jikinshi da turare mai sanyin gaske kafin ya d’auki makullin k’ofar da zata sada shi da falon Sameera ba sai ya fito ta farfajiyar gidan ba, yana shiga ya tabbatar sun jima da kwantawa, d’akin Raihan ya fara bud’a k’ofar a hankali ya lek’a, saida ya sauke ajiyar zuciya sabida ganin tana bacci hankali kwance, duk da har yanzu bai siya mata waya ba amma dai yana tsoron sharrin zamani da dubarar ‘ya’yan yanzu, rufewa yayi ya lek’a d’akin Rauda, Khalifa da sauran yaran, amma yana ganin Abdul raheem shi kad’ai kwance a gadonshi babu Ameer ya tabbatar yana wurin mamanshi, a hankali ya shiga can cak ya tsaya, rarraba ido yakeyi tare da shafar kai, a hankali ya fara takowa har ya zo kusa da ita ya tsaya, jefar da makullayen yayi kan gado ya bud’e mata hannayenshi yace “Come on my angel, i miss u.”
Sameera da tunda mota ta shigo gidan ta farka a hankali cikin turo baki ta bud’e hannayenta ta kwanta luf a k’irjin shi, lumshe ido yayi ya sauke wata ajiyar zuciya mai d’an k’arfi wacce iska da gumin bakinshi har suka sauka kan fuskarta, k’ara shiga jikinshi tayi tana sake matseshi sosai saboda k’aunar mijin nata, ido rufe take sauke ajiyar zuciya tana shak’ar turarenshi dake son mayar da ita bacci, cikin muryar shagwab’a tace “Me yasa baka fad’a min zaka zo ba?”
Saida ya fara yawo da hannayenshi a gadon bayanta yana latsawa saboda taushi da laushi ba tare daya bud’a ido ba yace “I’m sorry, nima bansan aikin zai sakeni yau ba, ina k’arasawa kuma naji ba zan iya kwana nesa da ke ba, shiyasa na garzayo na zo gareki.”
K’ara daidaita zamanta tayi cikin k’irjinshi shi kuma yana sake matseta yana shafata, cikin wata murya mai kama data bacci yace “Meerata.”
“Uhmmm.” Ta fad’a ba tare data kalleshi ba, d’orawa yayi da “Zan samu kulawarki a wannan daren kuwa? Naga baba na yayi kane-kane a kan gadon.”
D’agowa tayi ta kalleshi ta juya ta kalli Ameer dake ta baccinshi, sake kallonshi tayi tace “Ka d’auke shi mana saika kaishi d’akin su.”
Kallon Ameer yayi shi ma ya zagaya zai d’auke shi yace “Allah kasa kar yaron nan ya hanani sakewa.”
Murmushi tayi wanda harya fitar da sauti, kallonta yayi yace “Wallahi yaron nan rigimarki ce ya koya, ko da yana jariri bai hanani yin rayuwa da ke ba kamar yanda yanzun yake hana ni.”
Zaune tayi bakin gadon tace “Watak’ila yana tsanani buk’atar a kasance auta ne shiyasa, yasan idan ya baka fili saika masa k’ane.”
Harara ya cillo mata yace “Idan na tashi yi a hanani na gani, kinsan dai ko gabanshi na so zanyi yanda nake so ko?”
Dariya tayi tace “To ka barshi yanzu saimu jaraba mu gani.”
A lokacin daya d’auki Ameer ne yace “Bana so na jefo shi k’asa ai.”
K’arar bud’a k’ofa yasa Ameer bud’a ido tare da zabura ya kalli wanda ya d’auke shi dan ya hango mamanshi zaune, rintse ido Abbas yayi wanda yasa Ameer cikin muryar bacci cewa “Yeee! Dady na ganka bud’e idon.”
Kafin ya bud’e idon ido ya sake cewa “Dady yaushe ka dawo? Ka kawo min computer ta?”
D’ago shi yayi suka kalli juna yace “Muje na kaika d’akinka ka kwanta da safe zan nuna maka wacce na siyo maka, ko Khalifa baya da irinta.”
Ai sai Ameer ya dirko daga kafad’ar Abbas yace “Um um Dady, ni tare da Ammie na zan kwana, abinda ma tunda ka tafi tare muke kwana, kai kaje d’akin ka.”
Da gudu ya yo kan Sameera ya kwanta kan cinyoyinta yana kallon Abbas, ganin yana nufoshi yana fad’in “In dai kana son na baka computer sai ka zo mun tafi, idan ba haka ba kuma sai dai na bawa *Amjad* (d’an Naseer) ita.”
Zagaya hannayenshi yayi ta kunkumin Sameera ya mak’aleta sosai yace “Um um, bana so ni dai.”
Dariya Sameera tayi rumgume shi tace “Babana kenan, yaro kwana a gado d’aya tare da mahaifiyarshi yafi mishi komai na duniya ko?”
“Eh Ammie.” Kwance Abbas yayi kan gadon dan ko yace ya zare mishi ido kuka ne zai saka musu a daren nan, kallonshi yayi yace “Zo nan baba na nayi kewarka sosai.”
Rarrafawa yayi ya kwanta kan k’irjin shi ya rumgume shi, Sameera ma kwance tayi ta d’ora kanta a kafad’ar shi tace “Ka ci abinci kuwa?”
Ido lumshe yace “Um.” Tsautsayi yasa Sameera cewa “Auta na kayi abinci kaji, kasan…”
Wata k’ara ta saki saboda mintsinin da Abbas ya mata a mazaunai, zaune ta tashi idonta har sun fara ja saboda zafi, kallonshi tayi shi kuma ba tare daya kalleta ba yace “Gobe ma na sake jin kin kira shi auta kiga yanda zanyi da ke.”
Kamar zata fashe da kuka tace “To meye a ciki dan na kira shi da auta dan Allah?”
Ido rufe kamar wanda zaiyi bacci yana ci gaba da shafa bayan Ameer yace “Saboda yawon kiran na shi da auta zaisa wata rana ki fad’a lokacin amsar addu’a, ni kuma so nake sai kin dire min sha biyu insha Allahu.” Shiru ta mishi ta kwanta, gashinta yake shafawa da d’aya hannun a haka har bacci ya d’auke su.
*BASRABA*
Tunda garin Allah ya waye Takawa yake jin kamar ba shi ba, a haka har akayi sallah la’asar ya dawo b’angaren shi kan kilisarshi ya kishigid’a, haka kawai yaji yana buk’atar ganin liman, dan haka yasa d’aya daga cikin masu tsaron k’ofar shi ya nemo mishi liman, kusan dama unguwar duk duk fadawan fada ne a ciki, dan haka ba jimawa sai gashi ya dawo tare da liman, jakadiyar uwar d’aki na ganin haka ta garzaya ta fad’awa uwar d’aki, cikin tashin hankali tace “Kin tabbatar liman ne ya shiga wajenshi?”
Cikin girmamawa tace “Ko zanyi k’arya uwar d’aki harshena yayi kad’an daya furta miki k’arya, yanda na ga liman tare da bafaden nan ina fatan ganin annabi haka.”
Wata ajiyar zuciya ta sauke marar dad’in sauti tace “Tashi kije, amma kar kiyi nisa dan zan buk’ace ki.”