BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL
Kasancewar yara duk na islamiyya manya kuma basu cika shiga b’angarensu ba yasa ta kwashi tsawon awa uku da rabi a wurin babu wanda ya sani, sai tasowar yara ne daga islamiyya, su Abba da Ameer b’angarensu Ummy ma suka nufa dan can ake basu biscuit da chocolat, Ameera da tafi sarkawhar mahaifiyarta kai tsaye can ta nufa ita ma, ko da taga d’aki rufe ma ta d’auki hanyar da zata sadata da bayan gidan inda suke wanki wani lokacin har su zauna shan iska, ko da ta zagaya ta ganta kwance ta k’arasa, ita dai tasan kwancin nan bana lafiya bane, sai kawai tayi zaune kusanta tana daddab’ata tana kiran “Ummy, Ummy ki tashi k’aca ne fa kika kwanta.”
Jin shiru yasa ta k’ara girgizata tana fad’in “Ummy bake ke ana mu wacan k’aca ba? Shine kuma kika b’ata jikinki kema, saina fad’awa Papa.”
Tun Ameera na magana har ta gaji ta d’ora kanta akan cinyarta ta kwanta ita ma ta fara kuka.
Shi kanshi Ammar gabanshi yaji kawai yana ta fad’uwa, ya rasa me ke mishi dad’i a duniyar, wayarshi ya d’auka ya kirata da nufin tambayarta yara sun dawo daga islamiyya, saida yayi kira takwas ba’a d’auka ba sai kawai ya d’auki makullin mota ya fito, bai tsaya ko ina ba
sai gidan, shi ma yana ganin k’ofar rufe saiya juya ya shiga wajensu Ummy, yana ganin Ameer sun shiga wasa da uniforme d’in su yace “Sarkin k’iriniya ina uwarka take?”
Saida ya nuna mishi b’angarensu yace “Tana can.”
“Ameera fa?” Ya fad’a yana kallon sauran yaran, nan ma nuna masa yayi yace “Tana can.”
Juyawa kawai yayi ya sake komawa, wannan karan kai tsaye bayan gidan ya nufa, yana dosa ya hangin tashin hankalin da ko a mafarki baiyi tsammanin riskarshi ba, Ameera dake kuka har ta daina saboda baccin daya d’auketa sai ajiyar zuciya take, da gudun bala’i ya k’arasa yana kiran sunan “Amna, Amna, lafiya?”
Durk’ushewa yayi ya tallabo kanta, luuuuu kanta yayi yana ta langab’ewa, cikin kid’ima ya kamo wuyan hannunta yayi shiru, da sauri ya d’ora yatsunshi biyu kan wuyanta yana saurare, jin akwai alamar harbawar jijiya yasa shi saurin mik’ewa tsaye, janyo Ameera yayi daga jikinta baiwar Allah a cikin bacci ta firgita ta tashi, bai kula yarinyar ba ya tattaro Amna ya rumgume kamar yar beby yayi waje da ita.
Yaran ne suka sanar da fitarshi da Amna, ko da suka fito har ya figi motar sun bar gidan, a tsiyace yake gudu yana juyawa yana kallonta, da hannu d’aya yake tuk’i d’aya hannun kuma ya rik’e nata gam, Allah, Allah, Allah, kawai yake maimaitawa shima a zuciya, komai ya tsaya masa cak ya rasa me zaiyi tunani akai, yana isa bai bari mai gadi ya bud’e masa ba ya fito, mai gadi na shirin bud’e k’ofar yaga mai gidanshi a gigice ya bud’e gidan baya yana k’ok’arin d’auko mutum, da gudu ya shiga asibiti inda ya sanar dasu aka fito da gadon d’ora marar lafiya, yana daf da shiga suka had’e nan ya d’orata suka jata da gudu, ana turata d’akin da za’a dubata sai kawai ya ja ya tsaya, gashi yau asabar Ummy na gida, hannu biyu yasa ya shafi kansa tare da tsayar da hannayen saman kai, likitoci biyu mata ne suka shiga sai d’aya likitan wanda zai shiga ya ga Ammar ya tsaya shima saiya tsaya ya kalleshi, dafa kafad’arshi yayi yace “Muje mana, zamu buk’ace ka a ciki.”
D’ago duka idonshi yayi ya sauke mishi su, kallo ya bishi da shi kamar bai gane yarenshi ko kuma yau ya fara ganinshi, ya jima yana masa wannan kallon kafin ya bud’e baki yana son magana sai kuma ya kalli gefe, idonshi yaji sun cika da k’walla sai yayi saurin tsayar dasu ya kalleshi, girgiza masa kai yayi yaja baya baya ya zauna dab’as kan dogon bencin k’arfe dake bayanshi, duk’e kanshi yayi ya tangaleshi da tafin hannayenta, ganin haka sai kawai likitan ya juya zai shiga ciki, da sauri ya mik’e ya rik’o rigarshi, juyowa yayi yana kallon sai kuma ya sunkuyar da kai, dafa kafad’arshi yayi yace “Ammar, ka kwantar da hankalinka mana, kai ma fa likita ne, k’warin gwiwa kake buk’ata.”
Iska ya furzar ya d’ago ya kalleshi idonshi sun rine sosai, cikin amon muryar kuka yace “Dan Allah, dan Allah ka ceci rayuwarta.”
Jinjina masa kai kawai yayi ya juya ya shige, komawa yayi ya zauna ya dafe kanshi, a hankali yace “Me ya sameta? Me zai faru yanzu?”
D’ago kanshi yayi yana dafe da goshinshi yace “Cikin nan karka zamar mana matsala, ta min k’orafi akan shi amma ban ji ba, idan da nasan haka zata faru da tun farko na saurareta mun samu mafita.”
Kafad’arshi da yaji an dafa yasa shi juyawa ya kalli wanda ke bayanshi, Ummy ce tsaye tare da su Hajia Zeituna Zeinabu da sauransu, da sauri ya rik’e hannun Ummy yace “Ummy tana ciki, bansan me zai faru ba.”
Kallonshi tayi tace “Me ya same ta?”
Kai kawai ya girgiza bai ce komai ba, shiru sukayi kowa na addu’a a zuciyarshi, likitan ne ya fito da sauri da takardu a hannunshi ya zo ya tsaya gabansu, da sauri ya tashi tsaye yana tambayarshi lafiya? Saida ya kalli Ummy sannan ya bashi takardun yace “Muna buk’atar sa hannunka za’a mata aiki dan a ceto abinda ke cikinta.”
Fad’uwar da gabansa yayi yasa shi dafe k’irjinshi, rik’e hannunshi yayi yace “To ita fa?”
Kallonshi yayi zaiyi magana sai Ummy tayi saurin karb’ar takardun tace “Dukansu za’a fito dasu lafiya, saka hannun anan.”
Kallon Ummy yayi sai yayi murmushi yace “Yawwa Ummy na.”
Da sauri ya saka hannun likitan ya kalleshi yace “Muna buk’atarka a ciki Ammar, da alama ta d’auki kusan awa hud’u ko uku da rabi a sume, hakan ya jawo tsayawar…”
Da sauri yace “Zuciyarta na bugawa?”
Kallonshi yayi yace “Shiyasa nake so ka shiga ciki, zuciyarta na bugawa amma ba daidai ba.”
Da saurin bala’i ya tunkari d’akin ya shige ciki, saida ya shiga ya saka rigar aiki da hula da safar hannaye, rintse ido yayi ya bud’e akan ta, an saka mata oxygène tana kwance kamar gawa, saida ya kalli n’aurar dake nuna bugun zuciyarta da numfashi, nan ya shiga had’a allurai da abubuwan da suka dace, inda d’aya likitan kuma yasa aka mata allurar kashe zafi, nan da nan cikin k’warewa ya farkata inda Ammar ya kasa kallonta a wannan halin, bugun zuciyarta kawai yake dubawa yana fad’awa likitan yayi sauri dan ya samu damar yin nashi aikin shima, ana ciro santalelen yaron ya fashe da kuka, da sauri ya juyo yayi saurin karb’arshi, kallon fuskar yaron yayi sai yaji hawayen da yake ta k’ok’arin b’oyewa sun zubo masa, d’aya daga cikin likitocin ne ta amshe shi ta shiga kula da yaron dake ta tsanyara kuka.
Yana gama mata d’inki shima ya shiga dubata, bai tab’a tunanin zai iya nuna k’warewarshi kan wani na shi ba, gashi yana aiki akan matarshi data fara rikid’ewa ta zama jinin jikinshi, yana aiki akan ta cike da son ya ceci rayuwarta ta rayu, yana aiki akanta da niyyar ko tashi zuciyar ce ya cire ya dasa mata, amma kuma hannayenshi rawa suke, tausayinta da k’aunarta sai wahalar dashi suke a lokacin, sai gashi ya kai matakin da ma baisan me yake mata ba, likitan ne ya kula da hannunshi sai rawa suke kamar yau ne ya fara aikin, likitan na shirin dafa shi sai gani yayi ya saki wani d’an tsinken dake hannunshi ya juya baya yana rufe fuskarshi da hannu, da sauri ya matsa kusa dashi da nufin ya mishi magana, ikon Allah sai kawai suka ji n’aurar na kukan dake nuna bugun zuciyar ya fara tafiya daidai.