BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL
Ma’arufa kuma shiru tayi dan tunanin halin da mutumin kirkin zai shiga ya d’an fara damunta, gashi basuyi anfani da kororon robar da take anfani dashi ba idan za’a kusanceta, duk yanayin saiya mata babu dad’i da haka suka isa masaukinsu.
Har Sameera tayi sallah amma ba taji motsinshi ba, dan haka ta fito cikin rantsatsen less d’inta ta shiga d’akinshi, tana ganinshi kwance ruf da ciki dafe da bayan kanshi ta k’arasa da sauri ta zaune kan gadon ta tallabo shi cike da damuwa tana fad’in “Subhanallah, Abban Ameer lafiya? Meya sameka? Zazzab’i ne ma jikinka.”
Abbas da tunda ta shigo yaji tahowarta tana haurawa kan gadon ya ji wata tsanarshi ta k’ara zuwa mishi, k’in yarda su had’a ido yayi bai kuma bata amsa ba, shafa fuskarshi take cike da tausayi tana fad’in ” *Rabin raina* dan Allah ka min magana, meya sameka haka? Mun rabu da kai lafiya fa.”
Tureta yayi daga jikinshi ya sake mayar da kanshi kan pillow, ba tare da damuwa ba ta sake d’auko kanshi ta rumgume tsakanin k’irjin ta tana fad’in “Na kira maka dr Kabir ne ya duba ka?”
D’an k’aramin tsaki yayi ya sake d’auke kanshi yana fad’in “Mtsss, leave me alone.”
Gyara mishi kwanciya tayi tace “Ina zuwa, bara na d’auko wayata saina kira shi.”
Ta juya kenan taji muryarshi yace “Bana so, karki kira min kowa, kema dan Allah ki barni ni kad’ai, please and please.”
Mamaki ne ya sakata dawowa kan gadon ta juyo dashi tace “Abban Ameer, lafiya? What it’s problèm?”
Ba tare daya bud’a idonshi ba cikin wata irin muryar data kasa fahimta yace “Na ce ki fita kema, bana so kowa ya dame ni dan Allah.”
Cikin d’an daga murya tace “Ban gane baka san kowa ya dameka ba? Meya faru ne? Me akayi maka a gidan ko a waje? Matsalarka har ta kai k’adamin da ba zaka iya fad’a min ba? Ni fa mata….”
A hassale ya mik’e ya sauka daga kan gadon ya fizgi hannunta yayin da hawaye ke zubo mishi a idonshi na k’una zuci ya nufi k’ofa da ita, kallon fuskarshi take da mamaki tana ganin hawayen dake zuba, tabbas tasan yana kuka kuma yana son zama shi kad’ai idan ya tuna da yanda mahaifinshi ya rasu, amma ganin wannan zunzurutun damuwar kam ita dai bata tab’a gani ba, yana shirin fitar da ita daga d’akin ta cije ta fincike hannunta tace “Wai meye matsalar, dan Allah Abban Ameer ka fad’a min, kasan hankalina ba zai kwanta ba idan har baka fad’a min ba? Ni dai a sani na ban aikata maka wani laifin ba, amma…”
Zafin zuciya da halin da yake ciki na tashin hankali da jin zai iya dukan koma waye ya d’auke ta da mari, bai bari ta gama fahimtar meya faru ba ya jata zuwa waje yana fad’in “Ke har abada ba kya fahimar halin da mutum ke ciki.”
Yana jefata waje ya mayar da k’ofar ya rufe da makulli, Sameera dake dafe da kunci tsananin mamaki take, toh! Me yayi zafi haka? Laifin waye ya shafeta da har Abbas zai iya marinta? Meye damuwarshi? Rashin sanin wannan amsoshin yasa taja k’afa jiki a sanyaye ta bar wurin ta koma d’akin ta, ita ma bata sake fitowa ba saboda tunanin damuwar dake damun mijinta, Ammie ma da taga shiru ta d’an damu, kuma ga duka motocin gidan bare ta d’auka sun fita, amma haka ta daure saboda tunanin kusanci na mata da miji.
*A kwana biyun nan* sosai Fadila ke sakewa suna hira ta waya da Saleem, inda yake rubtata ita kuma tana fad’a mishi komai daya shafesu, a haka ya zurmata har ya fahimci tana kishi da Raihan wacce ita bata ma damu da abinda ita Fadilar ta damu da shi ba, nan fa ya nuna mata zai mata maganin matsalarta ta yanda shi zai samu Raihan, dan shi yana nuna mata yana son Raihan ne har zuciyarshi, ita kuma zata samu Abdul ita kad’ai, abinda yace tayi ne ya d’an sata jin wani iri haka, amma daya k’arfafa mata gwiwa ya nuna mata ta haka kawai zata samu soyayyar Abdul, sai kawai tace zata k’ok’arta ta gani, amma fa dan Allah karya cutar da Raihan d’in, murmushin jin dad’in samun nasara yayi yace karta damu, shi fa sonta yake kuma zai iya komai danya sameta.
To fa a hakane yanzu Fadila take sakawa Raihan d’in ido duk wani motsinta, yau ma dawowarsu kenan tare da amarya daga wurin gyaren jiki, d’akin uwar amarya *Kubra* suka shiga kowace ta fara k’ok’arin wanka, dayake babban gida ne kuma da ban d’aki dayawa sai kowa bai tsaya jiran d’an uwansa saiya fito ba, Raihan ce tayi nasarar shiga toilet d’in aunty Kubra, babu kowa a d’akin dan haka tana shiga Fadila ta dawo d’akin, tana ganin ta shiga tayi sauri ta fita ta zagaya bayan d’akin, doguwar kujera ta samu ta taka ta lek’a ta window, ai kuwa saiga Raihan ta bayyana tana cire kayanta, sabuwar wayarsu ta d’auka ta danna camera ta fara d’aukar ta hoto, Raihan dake wanka tana jin dad’in saukar ruwan daga sama idonta rufe, saida ta d’auki tsiraicinta kad’ai ta sauko ta dawo d’akin ta aje wayar ta shiga wanka ita ma.
Saida suka ci abinci suna zaune ta shiga WhatsApp ta tura ma Saleem wannan hotunan, yana ganin hotunan saida yaji wata sha’awar yarinyar, amma haka ya daure yana ta kallo har saida ya samu nutsuwa.
*Washe gari* abun alajabi suka tashi da shi, bak’uwar gidansu babu ita babu labarinta, kuma babu wani abu data bari da zai nuna taji dad’in zaman gidan ko tayi godiya kan abubuwan da aka mata, haka Ammie ta dinga mita akan tafiyar ta ta tunda babu kayanta, da safe ma haka Abbas ya tashi babu k’warin jiki, wanka yayi ya shirya cikin manyan kaya, maimakon ya fita saiya koma ya zauna yana jin kunyar fita, Sameera ma data ga har yara sun tafi makaranta amma bai fito ya karya ba yasa ta d’auki abun karin na shi ta shida part d’in shi, a falo ta ajiye a k’aramin center table ta nufi bed d’in shi, a hankali ta bubbuga amma shiru, sake bubbugawa tayi daga ciki yace “Please Sam ki barni dan Allah, na fad’a miki bana son takura.”
Cikin muryar rarrashi tace “Dan Allah Abban Ameer ka bud’e min k’ofar nan, ka sani fa baka da wanda zaka fad’awa damuwarka sama dani, idan kuma ba zaka iya fad’a min ba to ka fad’awa Abba ko Ammie mana, amma kana gani gaba d’aya ka saka kowa damuwa, yara sun tafi islamiyya babu farin ciki saboda basu ga Dadynsu ba, Ammie tana tambaya ta lafiyarka k’alau? Bansan me zan ce musu ba.”
Daga ciki ya amsa da “Ki fad’a musu bana jin dad’i ne kawai.”
Sanin ba zai bud’e ba yasa tace “Shikenan, zanje na fad’awa Ammie komai ita idan ta zo nasan zaka bud’e, ba zan fad’awa Abba bane dan nasan idan ya zo zai karya k’ofar ne.”
Da sauri ya taso yana fad’in “No Sam, please.”
Jin yana bud’ewa yasa ta tsaya tana kallon k’ofar, yana bud’ewa sukayi ido hud’u da shi, damuwa ce karara kan fuskarshi, saidai ya k’i kallon fuskarta har yanzu, ajiyar zuciya ta sauke tace ” Muje ka ci abinci gaya nan falo.”
Juyawa yayi ya d’auko wayarshi da makullin mota sannan ya dawo, wucewa yayi kamar wani gunki harya zauna kan kujera, durk’usawa tayi gabanshi ta fara zuba mishi abincin, harta gama bai kalleta ba saida ta ajiye mishi gabanshi, cokalin ya d’auka zai fara ci amma sam baya da appétit, da k’yar ya daure ya rufe ido zai kai loma bakinshi wayarshi tayi k’ara, cike da rashin kuzari ya d’auki wayar ya duba, bak’uwar lamba ce dan haka ya k’i d’auka saida aka sake kira na biyu shi ma bai d’auka ba, amma dake Salma ta fad’awa Ma’arufa komai game da shi saita turo mishi text kamar haka _”Ka d’auki waya zamuyi magana ne, very importante.”_