BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL
Yanda Hamna taji ana fad’in gidan ga wanda suka je saida taje ta ga ba haka bane suna k’wauran fassarashi, ba k’arya fa Ammar yayi gini na kece raini na shiga tsara, babu ce kawai babu a cikin gidan amma hatta kayan d’aki saida ya mata sabi ya zuba, har kayan jiki kallonta kawai yake sanda take kwaso kayan jikinsu, bai hanata bane saboda tunanin tana buk’atarsu ne, amma shi babu abinda baiyi ba har yaran ma ya musu sabin kaya.
Savon gida sabuwar rayuwar ga sabon k’aramin ciki da take dashi had’e da sabbin mutane, nan suka fara rayuwarsu ta d’aukar bakin duniya da sababi, babu abinda ya rage na zamansu sai ma sababin salon shiririta da suka fito dasu.
Idan yaran na gidan kad’ai suke d’an d’aga k’afa suna rage wani abu, amma idan suka fita sai su koma yara sai abinda suka ga dama sukeyi babu mai k’wabarsu.
*Wata shida*
Yau ma ya gama shiryawa zai fita yara sun kwana wajen Ummy saboda weekend ne, tana zaune ta d’ora farantin kankana kan tulelen cikinta tana sha, ko kulata baiyi ba ya d’auki hanyar fita, baki bud’e ta kalleshi da mamakin yanda ya shareta zai fita tace “Toh! Su Ammar kuma ko magana babu shine zaka fita?”
Ba tare daya juyowa ba yace “Bani da lokacinki ne.”
Ido ta zaro ta shiga kiciyar tashi tsaye rik’e da farantin tana fad’in “Wace yar iskar ce?”
Juyowa yayi ya kalleta, a hankali ya shiga takowa da wani irin kallo mai d’auke da salon mugunta, da sauri ta shiga ja baya ta fara zagaya kujerar tana fad’in “Allah karka matso nan Ammar, ka tsaya nan ka fad’a min wace shegiyar ce ta d’auki hankalinka har tasa kake jin baka da lokaci na.”
Cikin dakiya yace “Zan zo ne nan saina fad’a miki yanda zaki fahimta.”
Da sauri tace “Daga nan ma idan ka fad’a zan ji, fad’a min wacece ita?”
Da sauri ya d’ago k’afa da niyyar kamota hakan yasa ta juyawa zata zuba a guje d’aki, cikin d’aga murya yace “Hamna in kika tafi a guje da cikina ban yafe miki ba.”
Da k’arfi ta juyo tana kallonshi tana ja baya da tsoron kar ya tardata, da k’arfi ya rik’o wuyan hannunta yana matsewa cikin k’eta yana fad’in “Ni na fad’a miki ina da yar iska ne a waje? Wai ke me yasa kishi ya miki yawa ne?”
Cikin zabga ihu kai kace idonta yake cirewa ta shiga fad’in “Ammar zaka karya min hannu, sake ni dan Allah sake ni, hannu na fa zai karye.”
Saida ya zaunar da ita kan kujera yayi tsaye k’ik’am a kanta, ko da taga ya fara saita yatsunta tasan me zaiyi, zillewa ta fara yi tana kokawar k’watar hannunta tana fad’in “Na daina na daina, yi hak’uri ba zan sake ba, dan Allah yatsuna fa zasu karye.”
Ai kuwa bai kulata ba ya shiga lank’wasa yatsunta yana tausasu suna k’ara da k’arfin tsiya ba tare da sun shirya ba ji kake k’was k’was k’wask’was, saida ya gama ya saketa ya sunkuya ya kama na k’afa, billi ta shiga yi da k’afafunta tana fad’in “Na tuba Ammar na tuna na tuba wallahi.”
Saida ya gama tas ya mik’e ya gyara zaman rigarshi ya sunkuya ya sumbaci kumcinta yace “Je t’aime.”
Juyawa yayi zai fita ita ma ta mik’e ta nufi d’aki, saida ta kai k’ofar d’akin shima ya kai k’ofar fitar tace “Duk yarinyar daka kalla ko ka bata hannu kuka gaisa ban yafe maka ba Ammar.”
Lumshe ido yayi ya juyo kamar mai jin bacci ya kalleta, gwalo ta masa tace “Naje na fad’a ka zo mana.”
Gyara tsayuwa yayi yace “Ni kuma yau in na fita sai nayi budurwa, kinsan dai ba zan zauna dake kad’ai ba haka kawai, kamar yanda nake canja abinci na haka ma ina buk’atar canja wurin hutuna, dan haka zan samo yar yarinya yar cakwai da zan iya d’auka ba tare da nayi nishi ba, ke kuma a lokacin zaki san girman da nake da shi.”
Hamna da taji kamar ya soketa da mashi da sauri ta manta da wajen b’uya ne ta nufa ta fito ta nufe shi gadan gadan tana shiryin kuka tana fad’in “Ammar Ammar, zo dan Allah muyi magana, zo na baka hak’uri.”
Juyawa yayi cike da jin wata isa da izza wai shima akwai wanda yake wahalarwa akan son shi ya nufi k’ofa, da sauri kamar zatayi gudu ta riskeshi yana shirin shiga gabjejiyar motarshi fara tas, rik’eshi tayi ta baya tana turo baki, juyowa yayi ya kalleta fuska a had’e yace “Ya dai malama? Sake ni sauri nake.”
Ba tare data saki rigarshi ba taja ta har k’asa ta durk’usa gabanshi ba tare da jin nauyin cikinta ta marairaice tace “Ammar karka min kishiya ko ta waje ce dan Allah, ina sonka ba zan iya rabaka da kowace mace ba wallahi, dan Allah kayi hak’uri ka fad’a min duk abinda kake so da wanda baka so zan yi wallahi.”
Saida yayi da gaske ya cije dariyar dake son taho mishi, kallonta yayi yana d’an basarwa yace “Kin tabbatar za kiyi komai nace miki?”
“Allah kuwa zanyi, na rantse maka.”
Kamo hannunta yayi ta mik’e yana kallon fuskarta yace “Da fari ina so ki daina kirana Ammar gatsau babu sayawa, in baki manta nasha fad’a mikibana so, amma dana ga kin k’i dainawa saina zuba miki ido.”
Da tsantsar gaskiyar dake tattare da ita tace “Allah daga yau ba zake sake jin baki na yace hakanen ba, *duniya ta*, nima zanyi kamar yanda yer uwata ke yi.”
Ajiyar zuciya ya sauke cike da k’aunar wacce ta ambata yace “Allah ya gafarta mata.”
Kamar za tayi kuka ita ma tace “Ameen.”
Kallonshi tayi tace “To sai me kuma?”
Kallon fuskarta yayi yace “Ko daina min rashin kunya, bana son ina cutar dake.”
A marairaice tace “Shi ma na daina.”
Murmushi yayi ya shafi fuskarta yace “To shikenan babu ke babu kishiya ko ta cikin gida ce barz ta waje, yanzu kije ki huta abinki kafin na dawo na tayaki hira.”
A sangarce tace “Ka kula min da kanka.”
“Ke ma ki kula min da kanki.” Ya fad’a yana shiga motar, ta cikin gilashi ya bita da kallo har ta shige kafin ya tayar mai gadi ya bud’e masa k’ofa ya fita. Dariya kawai yake shi kad’ai Hamna ce durk’ushe a gabanshi, yana sonta kuma ya yarda ita ma tana son shi, yana jin dad’in zamantakewarsu kuma yana alfahari da hakan, sau da dama sukanyi fad’a har ta kai basa kula juna, amma ko awa basa yi suke shirya kansu cikin sauk’i, wani lokacin ma daga inda aka samu sab’anin ake d’inkewa ya shiga wainata yana rawa da ita ko ya goye har su shirya, hakan ne yasa zaman nasu dad’i da fahimtar juna.
*Kamar* tsautsayi kam akan hanyarshi sai ga d’aya daga cikin mutanen da har yau idan ya tunasu sai yaji kamar yayi kuka, kaf tsawon rayuwarshi babu wanda suka tab’a wulak’antashi sama dasu, ba’a tab’a mishi cin zarafin da suka mishi ba, ba’a tab’a mishi abinda bai rama ba, amma su sun sha daga kalaman mahaifiyarshi, alk’awarin daya mata ya tseratar dasu daga d’aukar fansar shi.
Amma kuma yanzu ga d’aya a cikin jami’an da suka dinga hantararshi da hana shi abincinshi, yana gaba akan mota yana birka gudu sosai da hular kwanon da ba mai rufe kai ba duka, d’an lumshe ido yayi tare da bud’ewa yace “Ummy ki gafarce ni, wallahi zuciyata tsayawa za tayi idan ban d’an tokareshi ba.”
Yana fad’a ya jawo belt d’inshi ya mak’ala sai kawai ya k’ara gudun motar, saida ya daidaici tayar moton kawai ya zungureshi, sai kawai ji akayi gijim ya wuntsile ya fad’i kan moton, da sauri ya taka birki haka mutane dayawa ma duk aka zagaye shi ganin soja ne fan a cikin tenue yake.
Da sauri ya fito daga motar yana réaction irin abun a bazata ne ya zo, ko da ya k’araso wajenshi suka had’a ido sai yace “Yallab’ai, kai ne ashe? Inna lillahi wa’inna ilaihi raju’un, na shiga uku yau, sannu yallab’ai dan Allah kayi hak’uri, wallahi…”