BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL
Tsayawa yayi kamar an taka masa birki ya d’an juya ya kalli su Amar dake zaune suna kallon ikon Allah, d’orawa yayi da “Hajia kin manta da wani abu, tun ranar da aka haifeni k’wank’wanmanki suka dawo kaina.”
Ciro gilashin shi yayi gaban aljihun rigarshi ya manna a idonshi ya juya, lieutenant ne ya mik’e ya fizgo rigarshi, hannu ya d’aga da niyyar marinshi sai Hajia ta dakatar da shi ta hanyar fad’in “Barshi.”
Kallon Hajia yayi ya saki rigar Ammar shi kuma saida ya gyara rigar ya wuce yana fad’in “Babu abinda dukanku zaiyi min da baiyi min shi ba a baya.”
Hajia kuma kallon Sa’ada tayi wacce ita fa take ganin duk rashin mutumcin da Ammar keyi ita ke d’aure mishi gindi, k’wafa tayi ta harareta ta wuce d’akin ta da tunanin koyawa uwar tashi hankali sai taga ta tsiyarshi ai.
Alhaji na d’an tattaki a gaba d’aya gidan harya isa bayan gidan, tsayawa yayi ganin Zeituna wacce abun duniya ya isheta tana kuka, girgiza kai yayi dan yasan matsalar ba zata wuce Hajiar shi ce ta mata wulak’ancin data saba, takawa ya fara yi da niyyar zuwa ya bata hak’uri, sai kuma ga Iya ta fito daga d’aya hanyar dake sadaka da bayan gidan da mamakin ganin Zeituna tana fad’in “Subhanallahi! Zeituna dama nan kika zo kika zauna? Ina can ina nemanki ki ka ma min d’auke kujerun wurin nan mu share wurin, amma kuma…”
Shiru tayi ganin Zeituna na kuka, da sauri ta k’araso Alhaji kuma ya tsaya, kusanta ta zauna ta dafata tace “Zeituna lafiya? Me akai miki kike kuka?”
D’agowa Zeituna tayi ta kalleta cikin goge hawaye tace “Iya, kamar mahaifiya na d’auke ki, bayan iyaye na babu wanda ke nuna min kulawa kamar ke, Iya wani abu yana damuwa na sosai a zuciyata, na b’oye nayi addua’r Allah ya cire min amma har yanzu babu sauk’i, yanzu gashi wata masifar na neman kunno min kai, Iya zan fad’a miki matsala ta watak’ila na samu sauk’in abinda ke damuna, amma Iya dan Allah ya zama sirri tsakani na dake, kuma bana so kiga wautata ko shirme na da haukana, shawara kawai nake so ki bani Iya.”
Ajiyar zuciya Iya ta sauke cike da dattako ta dafa kafad’ar ta tace “Nima kamar ‘ya na d’auke ki Zeituna, ki fad’a min matsalarki insha Allah zamu samu mafita, kuma zan fahimce ki da yardar Allah, sannan babu wanda zaiji maganar nan.”
Gyara zama Zeituna tayi ta fuskanci Iya da kyau ta kalleta da idon basira tace “…
_Duk wanda yasan zaiyi comment zai iya kasancewa grp d’ina ta hanyar neman wannan lambar *88-35-50-01*, ko kuma wannan *+213-65-81-91-316*, ko kuma wannan *99-32-99-10*, kuji da kyau wanda yasan zaiyi comment kawai._
16/06/2020 à 13:21 – Ummulkhairi: ❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️
*BADAK’ALA*
❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️
*Labarin Gaske*
*NA*
_SAMIRA HAROUNA_
*Litattafan marubuciyar*
*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D’AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD’I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K’ADDARARMU_
*8* _K’ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k’ura)…_
*14* _BADAK’ALA…_
*SADAUKARWA GA*
_*AHALI NA*_
*TAURARIN NIGER*
“`(Tsintsiya mad’aurinki d’aya)“`
_Bismillahir rahamanir rahim_
_17_
Tunda Junaid ya samu labarin gobe za’a je neman auren Maryama hankalinshi ya tashi , sam bai d’auka abin zai zo da wuri haka ba, duk da shi ba matse yake da yayi aure ba, amma tunda wacce zata aurar dashi d’in ta amince dole ya gaggauta, kiran Iklima yayi yace ta dubi Allah ta dubi annabi ta had’a shi da Maryama yana so suyi magana mai mahimmanci, magiyar da yayi mata tasa tace ba damuwa ya zo gida suna nan, saida ya d’auki wanka cikin k’ananan kaya yayi kyau sosai sannan ya fito, har zai shiga motar shi saiga Jibril ya shigo, takowa yayi wajenshi yana fad’in “Yawwa d’an uwa, gwara da Allah ya kawo ka, wani taimako zaka min dan Allah.”
Cikin sakin fuska Jibril yace “To wane irin taimako kuma malam?”
Tsaye yayi ya bashi hannu suka gaisa yace “Yanzu haka wajen Maryma na nufa, Iklima ta min alk’awarin ganinta idan naje, sai dai Maryama tana da taurin kai sosai, ina so ne muje ka rakani dan Allah wala’allah ko in ta ganka zata saurare ni, dan ya kamata ace yau ta koma gida saboda gobe su Abba zasu je garinsu nema min aurenta.”
Ido Jibril ya fiddo yace “Toh, da wuri haka? Amma ni…”
Katse shi yayi da cewa “Amma kai me? Dan Allah d’an uwa karka ce a’a, ka taimaka min muje, in kuma ba zaka je ba saina je na d’auko Ammar duk inda yake.”
K’ara zaro ido yayi yace “Ammar fa kace? Kai yanzu zaka yarda kaje wurin matar da kake son aura da Ammar? Lallai.”
Dariya Junaid yayi yace “To miye a ciki? Shi ba mutum bane?”
“Mutum ne, amma kasan danya d’udd’ura mata ashar k’aramin aikishi ne ko.”
Kafin Junaid yace wani abu Jibril yace “Jirani kawai na zo mu tafi, amma sai nayi wanka nima.”
Cikin gidan ya nufa Junaid na fad’in “Sai ka ce wanda zaije neman kasuwa, ko ka manta kai kana da matarka?”
Bai wani jima sosai ba ya shirya ya fito ya shiga b’angaren iyayen ya gaishe su sannan ya fito, ya fito kenan a farfajiyar suka had’e da Jamila zata shiga falon, k’asa tayi da kanta tace “Ina wuni.”
Cikin dakakkiyar murya ya amsa da “Lafiya lau, me kike a waje?”
Sororo ta kalleshi a ranta tace “Tofa! Wai kowa daya samu dama saiya dama tsiyarshi.”
Saida ta kalli k’wayar idonshi tace “Ba daga waje nake ba, daga bayan gida nake.”
Baice komai ba yasa kai ya wuce saida ta juyo ta kalleshi, yana samun Junaid suka fita daga gidan suka d’auki hanya sai gidansu Maryama, suna zuwa Iklima ya kira yace gashi waje, sosai Iklima tasha daga da Maryama kafin ta fito daga d’akin suna fad’a, a k’ofar gidan ta samu Huda tare da yara suna wasa, hannunta ta kama da tunanin idan sunje ya ga Huda ba zai mata wannan maganganun nashi ba da ba zasu anfaneta ba, daga cikin kwana inda suka paka mota ta shigo, tana zuwa taja ta tsaya ta jingina a motar a b’angaren da take tunanin babu kowa dan bai tab’a zuwa mata da kowa ba, ta k’ofar da yake tuk’i ya fito ya zagayo wurinta yana doka murmushi da fad’in “Gimbiya sarautar mata, Maryama kina lokaci fa, gani na ma sai kin so.”
Cike da jan aji tace “Hakan yafi ko? Asha wuya kafin a ganka.”
Murmushi yayi ya dafa kan Huda yana kallonta yace “Huda ya kike? Ya karatu kuma?”
Da murmushi yarinyar ta amsa da “Lafiya lau, ina wuni.”
“Lafiya lau Huda, ke ba kya baccin rana kenan?” Ya fad’a yana kallon Maryama, shiru Huda tayi dan kallon da Maryama ta mata bata fahimci me yake nufi ba, kallon Maryama yayi yace “Mari magana na zo muyi dake mai mahimmanci, amma kafin nan zan so ku fara gaisawa da d’an uwa na Jibril.”
K’ofar daya nuna mata yasa tayi saurin tasowa daga jinginar da tayi ta juyo tana kallon k’ofar, bud’e k’ofar Junaid yayi yace “Malam saika fito ko.”
Zuro k’afa yayi ya fito sannan ya fito da d’aya k’afar yana murmushi da kallon Junaid yace “Ai na d’auka ka manta da ni zakin soyayya.”
Kai tsaye kuma ya kalli Huda dake kallonshi ita ma tana murmushi, murmushi ya mata yace “Sannu bebbbbbbbbb.”
Cak ya rasa maganarshi saboda kallonshi da ya kai kan fuskar da duk da akwai canji amma ba zai tab’a mantawa da ita ba har abada, dakan uku uku k’irjin shi ya shiga yi a lokaci d’aya kuma ya ji komai na jikinshi ya tsaya daga gudanar ruwa da jini har zuwa numfashinshi ma neman gagararshi yake so yayi, ba zaka ce yana da rai ba inba dan zufar dake tsatsafowa daga kowace k’ofa ta jikinshi ba.