BADAK'ALA COMPLETE HAUSA NOVEL

BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL

Kallonshi tayi ta d’an yi shiru kafin tace “Ka fad’a masa ina aiki, i’m busy.”

Wani kallo ya mata yace “Wai ke me kike nufi ne? Haka ma ranar nan yace ki zo kika ce wai kina aiki.”

Cikin taushin murya da sanyin hali tace “To ba aikin nake ba? Dallah malam kaje ka fad’a masa ina aiki.”

Juyawa yayi zai fita yana fad’in “Ni yaronki ne to da zaki aike ni? Ke kije ki fad’a masa.”

Kallonshi tayi tace “Haba yaro ba laifinka bane da ka raina ni, Dady ne yake nuna maka kaine namiji dan haka har ni zaka iya mulka, amma ba komai its not ur fault.”

Khalifa kam da son girma fa bai zo fad’awa Saleem sak’on Raihan ba, sai Raudat dake zaune falo yace ta je ta fad’a masa, tashi tayi tana turo baki dan ita kuma a nata b’angaren gani take mugun raini ne ace Khalifa ke gaba da ita, kasancewar jikin Abbas Abbas ne da ita na girman k’asusuwa yasa har gabanta ya fara tara nonuwa, tana fad’a masa ita ma ta dawo falon ta zauna, Saleem kuma k’wafa yayi yace “Ba zan tab’a barinki ba, dole sai plan d’ina ya kammala a kanki, stupid girl kawai idiot.”

Harya zura k’afafunshi zai rufe motar yaji ance “Idan har kana so ka samu shiga kar ka zama lazy man, confidence kake buk’ata kafin samun zuciyar Raihan.”

Juyowa yayi yana kallon Fadila dake tunkaroshi, ba laifi ita ma kyakyawa ce, bai daina kallonta ba har saida ta k’araso ta tsaya kusa da shi, kafin yace wani abu tace “Tun ranar can na hangi zunzurutun k’aunar da kake mata, amma ita d’in yarinya ce da ba komai ke zama a kanta ba bare tayi tunani a kanshi, amma idan zaka kama k’afa dani burinka zai cika akan Raihan.”

Wani shu’umin kallo ya mata da murmushi a gefen lallab’anshi irin na tarkona ya kama kurciya, ita ma kallonshi take tana ganin nata burin zai cika idan tayi k’ok’ari ta had’a soyayyarsu, cikin kwanciyar hankali yace “Are u sure zaki taimaka min har nayi winnen heart d’in ta?”

Cike da k’warin gwiwa tace “Ina baka tabbacin haka.”

K’aramar yatsarshi ya mik’o mata tare da fad’in “Mun kulla daga yanzu kenan? Mun zama friends.”

Bata bashi yatsanta ba sai kai data jinjina masa alamar eh, fitowar Abdul a sukwane daga part d’in yasa hankalinta komawa can, bata jira ya nemeta ba ta taka da sauri ta tarbeshi tana fad’in “Yah Abdul ina zuwa haka da yammar nan?”

Cikin sakin fuska yace “K’anwata zanje wani wuri ne, ko kina zuwa ne?”

Cikin salo kamar babbar mace tace “Yah Abdul tafiya indai tare da kaine zan yarda na shekara dubu ina yinta ba zan gajiya ba ai.”

Murmushi ya mata yace “To nagode k’anwata, yanzu dai zan tafi saina dawo, ko da wani geft kike so na siya miki?”

Saida ta kashe masa ido tace “Kawai ni ka kular mana da kanka.”

Nan ma murmushi yayi yace “I wil insha Allah, bye bye.”

Yana fad’a ya shiga motarshi ya tayar, da kallo ta bishi harya fita daga gidan kafin ya kula da Saleem wanda shima kallonta yake ya hango soyayyar Abdul a idonta, k’arasowa tayi hakan yasa ya mata dariya yace “Kina ta so ki b’oye, amma kuma zuciyarki da idonki sun k’i lamuntar hakan, meyasa zaki cutar da kanki ta hanyar hana zuciyarki abinda take so?”

Kallonshi tayi sosai tana nazari, ko ba komai yau ta samu wanda ya gano abinda ke zuciyarta, dan haka babu fargaba cikin rufewar ido tace “Saboda ba ni ce na dace da shi ba.”

Da mamaki yace “To wa kenan ta dace da shi?”

Kai tsaye tace “Raihan mana.”

Yanda ta fad’i sunan a take saiya hangi kamar zuciyarta ta fara tafasa, dan ya samu biyan buk’ata sai yace ” Amma ke ma mace ce mai class , kina da kyau ilimi da wayewa, sannan iyayenki babu na yarwa, so meye wata ‘ya mace zata nuna miki har ta hanaki cikar burinki?”

Shaid’an ne ya dinga hura wutar dake zuciyarta harta saki baki tace “Ban sani ba nima, amma ko Ummata sau da dama zaka ga tana nuna banbanci tsakani na da ita, haka ma Abbana yana fifitasu a kanmu, gaba d’aya mun zama kamar wasu bayinsu, mahaifinsu ne ke juya namu iyayen, mahaifiyarsu ma ta mulki iyayenmu, hatta makaranta wannan sai a motarsu ake kaimu alhalin iyayenmu nada halin siyan motan da tafi tasu.”

Harira ce ta fito farfajiyar gidan tana waya da Adamu yayanta, hakan yasa Fadila yamutsa fuska tace “Ina ga zamuyi magana da kai, yan sa ido sun fara fitowa.”

Wayarshi ya mik’o mata yace “Give me ur phone number, i wil call u.”

Karb’a tayi ta saka mishi ta mik’a mishi tayi gaba, shima fita yayi daga gidan, zata shiga part d’in Sameera ta hangi Abbas da fitowarshi kenan daga wanka ya haura sama dan ya ga ko motar da zata kawo mishi matar shi ta si, ganin babu motar yasa shi ciro wayarshi ya dannawa dr Kabir kira, a lokacin kuma Fadila ta zagaya ta haura ta saman dan ta gaishe shi su kuma yi hira kamar yanda suka saba, duk da yanzun tana jin ba zata tsaya yi hirar ba dan Saleem ya tsokano mata wani abu shaid’an kuma ya sake zugata, sam baisan da zuwan mutum ba hasalima baya tsammanin zuwan kowa wurin, tambayar dr Kabir yake yaushe result d’in Abdul zai fito yaje ya karb’a, bayan ya fad’a masa ne Abbas d’in ke cewa “Ina fatan kar a samu kowace cuta a jikinshi, dan in aka samu tofa babu maganar aure tsakaninshi da Raihan, dan su Abba ba zasu bari ba, sanan dan Allah ka k’ara rik’e mana sirrin nan ko Abdul kar yaji an mishi gwajin nan bare kuma wani nashi.”

Alk’awari ya mishi yace ya kwantar da hankalinshi, Fadila na jin haka tayi saurin komawa ta sauka k’asa, ranta ne ya sake b’aci sosai tana ganin kenan shi kanshi Abdul d’in ma basu raga ma ba, ai kuwa shiryawa tayi zata bayyana mishi soyayarta in ya so duk abinda zai faru ya faru.

Ta sauke kenan aka bud’e gate d’in gidan motar Abdul ta shigo tare da Sameera, dama saurin da yake zaije d’aukar ta ne, Abbas na hangensu har Abdul ya shiga da jakarta ita ma ta bi bayanshi, fita yayi daga nan yasa makullinshi ya bud’e d’akin ta ya sake rufe k’ofar da makullin ya zage shi, ya kusan minti talatin a d’akin ko hasken fitila bai kunna ba kafin yaji Sameera ta taho cikin d’aga murya tana fad’in “Ku wa Allah ku wa ubanku ku barni nayi wanka zan fito yanzu.”

Yana jin ta saka makulli ya taso daga kan gadon ya lab’e jikin k’ofar, tana bud’ewa ta mayar ta rufe da niyyar shiga wanka, ta juyo kenan da nufin kunna hasken d’akin taji an cakumeta ta baya tare da rufe mata baki da hanci da tafin hannu lallausa wanda hakan yasa k’arar da tayi bata fito ba, tabbas tasan Abbas ne amma me yake nufi da haka bata sani ba? Take a wurin gyalenta da d’an kwali ya fita ta saki jakar data shigo da ita, ta bayanta ya d’ora hab’arshi a kafad’arta yace “Wato a gabana kike zagar min yara ko? Saboda kina tunanin bana gidan, ashe dama haka kike tsine min bayan ido na? To bari kiga yanda zanyi dake.”

Cillata yayi akan gadon ya kuma bita ya taushe yana fad’in “Jiya nace ki zo, amma ki ka k’i zuwa dan kin raina ni, sannan kika cije ni nace zan rama kika ce na rama d’in, to bari kiga ikon Allah Sameera, ba dai dan kinga ina jin tausayinki ina d’aga miki k’afa ne yasa kika raina ni ba.”

K’wafa yayi yasa k’arfi ya cire zip d’in rigarta da k’arfi, bata fara jin tsoro ba har saida taji ya rabata da komai na jikinta, da k’arfi ta k’walla kiran “Ammieeeee!”

D’aga hannu yayi kamar zai mareta yace “Wallahi kika k’ara d’aga min murya saina zabgeki da mari, fitsararriya kawai.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231 232 233 234 235 236 237 238 239 240 241 242 243 244 245Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected