BADAK'ALA COMPLETE HAUSA NOVEL

BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL

Ummy ce tace “Gaskiya kam, dan ko ni da na zo daga baya na samu tana shirin tsayar da ruwan miyar, da shigowata kuma yanzu a k’alla na d’auki minti kusan talatin, amma ace bai dahu ba? Abun kam da mamaki.”

“Yanzu ya zamuyi? Wallahi a tsorace nake, Hajia ta turo ni ne dan na kama aiki, kar ta d’ora min laifin.” Cewar Zeituna a matuk’ar razane. Matsawa Ummy tayi ta sake bud’ewa tukunyar wuta tana motsawa ta ga ko ya fara d’aukar hanyar dahuwa, babu wannan alama dan haka ta rufe tukunyar tace “Mu bashi minti biyar d’in shima muga ko zaiyi.”

Baya suka ja wasu daga ciki suka zauna kan kujerun da suka k’awata madafar suka buga tagumi, dan kowa yana da tabbacin ba zai sha ba inhar basu gama kan lokacin da aka basu ba. Lokacin da aka basu na cika Ummy tayi saurin bud’a tukunyar, amma juya iya yau babu abinda ya sauya, abun mamaki ne wannan matuk’a, dukansu babu wacce bata nuna alamar wannan mamakin ba, Ummy ce tace “Anya kuwa? Ko dai…”

Sai kuma tayi shiru sai Soueiba ce tace ” ‘Yan biyu?”

Ba tare data kalleta ba tace “Bani da tabbas, amma kuma ai basu da k’ohi yanzu.”

“Kada muyi saurin yanke hukunci, amma wannan abunda yake faruwa yafi kama da aikin ‘yan biyun gidan nan.” Cewar Soueiba, girgiza kai Ummy tayi tace “Ko hakane ma sai dai aikin Amna, dan tafi ‘yer uwarta mugunta tun suna yara haka nasha wahalarsu.”

Ajiyar zuciya Soueiba ta sauke tace “Sai kiji ki lallab’a mana ita mu samu mu ida girkin nan.”

Murmushi Ummy tayi tace “In dai har Amna ce, to ba zata hak’ura ba sai dai kawai wanda ya rabasu jiya yanzun ma ya bata hak’urin, dan nasan tana fushi ne saboda an kirashi ya tilasta ta ko kuma dai dan tabawa yar uwarta hak’uri.”

Soueiba ce tace “To kiyi magana da Ammar d’in mana shi ya rarrasar mana ita.”

“Ba zan iya ba, ke kije.” Ta fad’a kai tsaye. Kallonta Zeituna tayi sai Soueiba data kalli Nana tace “Kinga Nana, tun kafin Hajia ta dawo ki hanzarta b’angarensu Ammar ki kira shi, dan naga motar shi har yanzu tana nan alamar bai fita ba.”

“To.” Nana ta fad’a tana fita daga madafar, a hankali ta bi ta bayan Hajia ta sulale ta bar d’akin ta je b’angarensu Ammar, babu kowa a falon amma kuma k’ofar bud’e, ita kuma har ga Allah tana shakka da tsoron halin Ammar data shiga dan ta bubbuga k’ofar shi, dan haka ta juyo ta zab’i ta gaya musu su suje da kansu, tana dawowa kuma Ammar ya d’auki makullan mota ya bar gidan wanda yayi daidai da fitowar Soueiba dan ta mishi magana, amma kash har ya fita daga gidan sai komawa tayi.

Sanda Hajia taji meke faruwa da kanta ta samu Amna har d’aki tana gaggawar shiryawa zata tafi makaranta wajen jarabawa, tatas ta mata ta zageta uwa da uba sannan tace in har abincinta bi dahu ba zata kuma ci mata uwa, haka Amna ta fita rai a b’ace akan motonta dan Hamna ta jima da tafiya, amma tayi niyyar yau Hajia ba zata ci abincin ba ko da na rana ma tunda bata iya bayar da hak’uri ba.

A tak’aice dai Hajajju sai yan dubaru tayi, yara ma haka aka musu dubaru aka tura su makaranta, Ummy ma haka dubarar tayi kafin ta wuce asibiti inda ta samu Ammar yau ya rigata zuwa, amarya Zeituna ma a d’akinta ta samu madara da cornflakes ta mishi had’in kauri tasha ta kwanta tana tunanin ahalin gaga. Da rana sam Nana ba tayi tunanin komai ba ta gyara shinkafa ta bayar aka b’arzota ta d’ora tukunyar dambu, ba b’ata lokaci tukunya ta taso aka fara yamutsa dambu, ana gama gyara komai aka d’ora a madambaci aka rufe, nan Nana ta shiga sarrafa mahad’in dambu, ‘yar k’aramar sauce ce mai nik’akk’en nama da albassa mai yawa, saida ta fuskanci yanzu dambunta ya isa ta dubashi ta tunkari tukunyar, tana bud’awa bud’e baki tayi kamar zata k’urma ihu tare da d’ora hannu d’aya bisa kai tace “Na shiga uku, yanzun ma?”

Da sauri Zeinabu data shigo tace “…

*Alhamdulillah*
09/09/2020 à 17:58 – Ummulkhairi: ‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍
*BADAK’ALA*
‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍

*Labarin Gaske*

*NA*

_SAMIRA HAROUNA_

*Litattafan marubuciyar*

*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D’AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD’I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K’ADDARARMU_
*8* _K’ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k’ura)…_
*14* _BADAK’ALA…_

*SADAUKARWA GA*

‍‍‍ _*AHALI NA*_‍‍‍

*TAURARIN NIGER*
“`(Tsintsiya mad’aurinki d’aya)“`

_Bismillahir rahamanir rahim_

_30_

“Mun shiga uku! Kar dai ki ce har yanzu ma ba zamu ci abinci ba?”

Cike da tabbatarwa tace “Ai kuwa dai wallahi da alama.”

Juyawa tayi ta fita tana fad’in “A’a wallahi ba zai yiwu ba, bari na d’auko wayata na kira Sa’ada ta zo ta sa Amna ta sakar mana tukunya, yau ni naga ikon Allah.”

Tana daf da kaiwa d’akinta lieutenant ya shigo, wanda ya kasa zama ya matsu ya ga halin da Zeituna take ciki, sunkuyar da kai tayi tace “Ina wuni Abban Ammar.”

Cikin sakin fuska ya amsa da “Lafiya lau, ya gidan?”

Ba b’ata lokaci tace “To da sauk’i dai gaskiya.” Da mamaki ya kalleta yace “Lafiya dai ko? Ko wani abun ya faru ne?”

Cikin sunkuyar da kai ta fad’a mishi duk abinda ke faruwa, murmushi taga yayi yace “To ku samu ku lallab’a ta mana, kunsan dai fad’a da zagi ba zaisa ta huce ba.”

“Eh hakane, yanzu ma zan d’auko waya ne na kira Sa’ada saita lallasar mana ita.”

Da ‘yar dariya lieutenant yace “To ke ba zaki lallab’ata ba?”

“To ai ni bansan ta inda zan fara bane, ita kuma ta saba da rigimar bibbiyu dama.”

Dariya ya sake yi yace “Da gaskiyarki kuma, tana ina Amnar?”

Nuna sama tayi tace “Tana sama dai a tunani na.”

“Bari na jaraba na gani ko zan iya.” Ya fad’a yana wucewa d’akinsu dake sama, zaune tayi falo ta jira shi ya fito taji ya suka k’are, yana zuwa saida ya k’wank’wasa k’ofar d’akin yayi sallama, kusan a tare Hamna da Amna suka amsa wanda kowace ke kan gadonta babu mai kallon wata, saida kowace ta gyara zaman tufafinta kafin Amna da gadonta ne farko ta taso ta bud’e k’ofar, gaishe shi tayi ya amsa cikin sakin fuska tare da dafa kanta, murmushi yayi kafin yace “Amnata baki jin yunwa ne?”

Da sauri ta d’aga matsakaitan idonta ta kalleshi sai kuma tayi k’asa da su tana jujjuyasu, jin shiru yasa yace ” ‘Yata, yunwa nake ji, kuma na zo gida an fad’a min wai kin rik’e tukunyar girkin, shine nace bara na zo na rok’i alfarma, ko baki saketa dan ni ba ki saki dan k’annanki da kuma angonki Alhaji, wanda kinsan basa juriyar yunwa, da safe ma ance basu ci wani abun kirki ba.”

Ganin tayi shiru yasa ya sake dafa kanta yace “A taimaka mana kinji, kiyi hak’uri komai ya wuce.”

D’agowa tayi ta kalleshi tayi murmushi tace “Ba komai Abbanmu, nima ba’a son raina bane haka ta faru.”

Murmushi ya mata yace “Nagode ‘yata, Allah miki albarka.”

Da murmushi ta masa da “Ameen Abbanmu.”

Juyawa yayi ya samu Zeinabu zaune yace “To ku tashi ku duba tukunyar ku gani.”

Yanda yayi maganar yasa ita ma tayi dariya tace “Yaran nan, mun gode Allah da yasa basu da k’ohi, da ina ga zuwa yanzu duk mun kamu da ciwon yunwa.”

Dariya yayi yace “To wai ya akayi ma haka ta faru bayan kuma basu da k’ohi? Abun da mamaki fa.”

“Wallahi nima ya ban mamaki.” Madafa ta wuce shima ya shige d’akin Zeituna, kwance ya sameta akan sallaya ta idar da sallah, yanzu ma doguwar riga ce jikinta da hijab, sululu ta mik’e zaune cike da kunya tace “Sannu da zuwa, ina wuni.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231 232 233 234 235 236 237 238 239 240 241 242 243 244 245Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected