BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL
Bud’ar bakin tsohon sarki cewa yayi “…
*Mu tara a shafi na gaba insha Allah, shin zai ce yayi aure ne ko kuma a’a? Wa ma za’a aura masa ne? Ya kuma zaman zai kasance?.*
✋
29/05/2020 à 11:19 – Ummulkhairi: ❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️
*BADAK’ALA*
❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️
*Labarin Gaske*
*NA*
_SAMIRA HAROUNA_
*Litattafan marubuciyar*
*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D’AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD’I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K’ADDARARMU_
*8* _K’ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k’ura)…_
*14* _BADAK’ALA…_
*SADAUKARWA GA*
_*AHALI NA*_
*TAURARIN NIGER*
“`(Tsintsiya mad’aurinki d’aya)“`
_Bismillahir rahamanir rahim_
_6_
Kallonshi yayi yace “To, ban gane me kake nufi ba?”
“Yanzu zan fahimtar da kai Baba.” Ya fad’a yana gyara zama sosai, ba tare da tsoron komai ba ko fargaba yace “Ni mutum ne daya yarda da tsafi, ina da wanda yake jib’antar al’amuran rayuwata (boka fa yake nufi), akwai wata babbar harka dana saka a gaba nake son ganin na cimma burina a kai, amma ya fad’a min komai zai tafi daidai da zaran na samu budurwa ina nemanta ta duburarta, ya kwatanta min kalar yarinyar dama fallasa min kamaninta, ina ganin yarinyar nan kuma na tabbatar ita ce, na fad’awa boka na kuma ya tabbatar min ita ce silar k’ara bunk’asar arzik’i na, amma komai zai tafi yanda ake so ne idan na fad’awa iyayenta komai da ita kanta yarinyar, dan ana buk’atar ku sani sannan ku amince d’ari bisa d’ari, wannan shine ya kawoni gareku, idan baku amince ba to ku sani kunyi asarar babbar dama, dan akan harkar nan a shirye nake dana kashe kud’i daga million d’aya har million hamsin, indai buk’ata zata biya.”
Kawu Mamu da yana saurarenshi gumi ne ke keto mishi, a zuciyarshi addu’a yake su rabu lafiya dan ya fahimci k’aton matsafi ne, amma yana jin million ta fara magana saiya kalleshi da sauri ya goge zufar yace “Million hamsin fa kace d’an nan? Kuma zaka iya bada su?”
Wani shak’iyin murmushi yayi yace “Sosai ma, zan iya yin komai domin ganin na samu abinda nake so.”
*Allah ka mana tsari da irin mutanen nan, kawu Mamu ma ba iyaye ne da zakayi alfahari dasu ba, ko ba ‘yar daka haifa ba ace mutum ya fito gwaro gwaro ya fad’a maka k’udirinshi akan wani naka, ina ga sai inda k’arfin ka ya k’are, abun kamar a almara amma kuma ya faru, ana irin wannan tab’argaza me zai hana ubangiji yayi fushi damu har ya dinga jarabtarmu da masifu iri-iri, Allah mun tuba ba dan hallayenmu ba ka mana gafara, domin kuwa kai mai gafara da kuma jin-k’ai.*
Cikin jin dad’i kawu Mamu yace “Wannan ai ba komai bane, dama ba ni na haifeta ba ‘yar d’an uwa na ce, dan haka indai har zaka bayar da wannan kud’in to a shirye nake dana saka ta tayi maka duk abinda kake so, kuma dama ai yarinyar tana ‘yan yawace yawacenta, kaga kuwa abun ba zai bata wahala ba.”
Duk da hausar tashi da k’yar yake ganeta amma dai ya fuskanci abinda yake nufi, dan haka ya kalleshi yace “Ka amince kenan?”
Cikin sautinshi na fulatanci yace “K’warai kuwa Alhaji.”
Jinjina kai yayi alamar gamsuwa tare da saka hannu cikin aljihu, wasu sababbin kud’i ya fito da su yan jaka goma goma ya dire mishi gabanshi yana fad’in “Ga wannan naka ne, ka fara rik’ewa kafin na sake dawowa.”
Sake zura hannu yayi wani aljihun ya zaro wanda suka ninka waccen ya aje mishi yace “Wannan kuma a bawa yarinyar tayi buk’atunka, ta kuma tabbatar duk abinda zatayi zatayi shine dan gyaran jikinta saboda anfani na, ni zan tafi yanzu, zan dawo nan da sati d’aya lokacin nasan ta gama gyaran kanta.”
Yana fad’a ya mik’e ya saka takalminshi, kawu Mamu da tuni hankalinshi ya tashi kud’in ya d’auka yana waiwayen bayanshi yana zubawa aljihu, ganin bai ma san me yake ciki ba yasa ya wuce kawai ya barshi, saida ya bud’e murfin motar ya juyo yace “Sunan yarinyar Zeituna ko(dan bokanshi ya fad’a mishi a daren jiya)?”
Cikin kid’imewa kawu Mamu yace “Eh Eh, sunanta kenan, Zeitu ba.”
Shiga kawai yayi ya tayar ya wuce, kawu kuma cikin gidan ya shiga Jumma na ganinshi tace “Yanzu Baban *Jumare* a waje ka baro mana tabarmar salan wani ya d’auke?”
Da yatsa ya mata alama tayi shiru sannan ta biyoshi, bukkarshi suka shiga har saida ya sake labule kafin ya kalleta kamar marar gaskiya yace “Ke ba tabarma ba ki fad’i abinda kike so ma zan miki, zauna ki saurare ni kiji.”
Zaunen tayi tana kallonshi da tambayoyi pal a ranta, nan fa ya kwashe komai ya fad’a, al’ajabi tare da jinjina rashin imanin mijinta ne suka rufeta, da mamaki ta kalleshi tace “Baban Jumare, yanzu kuma kai ka amince da nufin mutumin nan a kan ‘yar d’an uwanka? Baka tsoron abinda mutane zasu fad’a? Sannan ba ka tunanin ma ko kasheta zasuyi? Haba ka duba lamarin nan mana.”
Rufe ido yayi ya fara zazzaga mata bala’i wai ‘yar d’an uwanshi ce ai, sannan kullum ita ke fad’a mishi Zeituna karuwanci take, to meye yanzu dan anzo har gida an nemi izininshi, ita dai hankalinta bai kwanta ba har saida yace “To wallahi idan ba zaki bani goyon baya ba sakinki zanyi, kinga dai yanzu ina da kud’i? Dan haka k’ara aure ba zai min wahala ba.”
Sai lokacin kad’ai ta wayance ta nuna mishi ba komai kawai, kud’i ya tsakuro ya bata yace “Wannan kuje kusuwa ke da ita idan ta dawo ki siyo mata kaya masu kyau na kwalliya da ado, wannan kuma kema kya fara tab’awa.” Ya fad’a yana d’auko jaka goma ya bata, ai sai taji kamar ya bata duniya, nan fa suka shiga bushasha da kud’i anata farin ciki.
*Misalin 08:07 na dare*
Tunda Hajia na gidan shiyasa yau Zeituna bata tsaya cikin gidan ba, tare da Iya suka fito kowa yayi hanyarshi, amma tana ganin Iya ta b’ace ma ganinta saita lab’e a cikin kwanar ta zauna anan, lieutenant kawai take so ta gani sannan ta wuce gida, duk motar da taji tayi oda a k’ofar gidan saita lek’o da sauri, amma sai taga wani ne daban ba shi ba, a k’alla ta d’auki minti kusan ashirin bai dawowa sai kawai ta yanke shawarar tafiya, dan bata so tayi dare irin na jiya na jawa kanta masifa, mik’ewa tayi jiki a sanyaye ta kama hanya duk zuciyarta babu dad’i, da haka ta isa gida tana zuwa kuma mamaki kuma ya nemi halakata saboda Inna Jumma ce da kanta ta bata tuwo, inda kawu kuma har yake tambayarta ta k’oshi? Jumma ce tace “Tashi ki d’ibi ruwa kiyi wanka ki zo zaki rakani unguwa.”
Da mamaki ta kalleta tace “Unguwa kuma Inna?”
“Eh.” Tashi tayi tana mamakin canzawar mutanen, ta zauna tare da su na tsawon shekara goma sha biyu, amma abu makamancin wannan bai tab’a faruwa ba sai yau, to me suke nufi? Ta tambayi kanta, kar azo ko salwantar dake zasuyi ma dan su huta, wata zuciyar ta fad’a mata haka, da wannan wasi-wasi ta samu tayi wanka sai dai babu wani sabulu mai kyau, haka ta fito suka shirya suka fito, adaidaita suka samu ta kaisu kasuwa ta aje, kayan kanti ta siya mata saidai ba masu yawa ba, saboda tsadarsu yasa basu iya d’aukar dayawa ba, daga doguwar riga uku sai riga da siket biyu, kayan kwalliya ta siya mata aka had’a da sabulu da man goge baki da sabi takalma masu tsini, daga nan suka wuce gida Jumma na ji a ranta ita ma fa ta waye, alhalin duk kayan da ake siye babu wanda ake yayinshi yanzu duk tsofaffin yayi ne, amma a haka take ganin ita ma ta zama cikakkiyar yar birni.