BADAK'ALA COMPLETE HAUSA NOVEL

BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL

Murmushi kawai yayi ya d’an jinjina mata kai ya shige falon, ajiyar zuciya ta sauke dan tasan zaiyi wuya Hajia ta kasa sauraren shalelenta, indai har ya nuna hakan yake so to zata amince ko da ita ba haka ta so ba.

*Fatan nasara Amar*
11/06/2020 à 17:26 – Ummulkhairi: ‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍
*SANIN MASOYI*
_(sai Allah)_
*BAYA DA K’URA*
‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍

*NA*

_SAMIRA HAROUNA_

*Litattafan marubuciyar*

*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D’AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD’I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K’ADDARARMU_
*8* _K’ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k’ura)…_
*14* _BADAK’ALA…_

*SADAUKARWA GA*

_*MASOYA NA*_

_Bismillahir rahamanir rahim_

*TAURARIN NIGER*
“`(Tsintsiya mad’aurinki d’aya)“`

_8_

Bud’ar bakin Raudat cewa tayi “Lahh! Ai Ammien mu tana raye, tare suka tafi basraba basraba amma ita bata dawo ba.”

Cike da makirci tace “Ayya kunji dad’in ku, kuna da iyayenku a raye suna k’aunar ku, sannan Allah ya muku baiwa ta daula babu abinda kuka nema kuka rasa, sannan na tabbata iyayenku suna farin ciki da junansu bare hankalinku ya dinga tashi idan sun samu sab’ani.”

Murmushi Raudat tayi tace “Gaskiya ne aunty, duk da iyayenmu suna yawan fad’a amma dai fad’an nasu na shirme ne, dan duk fad’an su basa awa d’aya basu shirya ba, kuma dama Ammie ita tafi d’aukar zafi.”

Ta gefen ido ta kalleta kafin ta d’an zaro ido tace “Kina nufin yanzu nan iyayenku suna fad’a? To akan me?”

Cike da yarinta Raudat tace “Kamar yanda na fad’a miki fad’an su duk shirme ne, amma mafi aksari sunfi rigima akan kishin Ammien mu, wani lokacin kuma bamu san meke had’a su ba sai dai muga Ammie na b’uya a bayan Ammie, idan ita ta tsokani Dady kenan.”

Saida ta kamo hannunta tace “Kenan Ammienku batayin duk abinda Dadynku baya so?”

Saida ta firfito da manyan idonta masha Allah kafin tace “Ban sani ba gaskiya, mu dai kawai rayuwar iyayenmu tana bamu sha’awa, suna k’aunar junansu sosai, suna raha da wasa a zamantakewarsu, shiyasa muma muke k’aunar su.”

Mik’ewa tayi tace “Aunty bak’uwa saida safe.”

Murmushi tayi tace “Aunty bak’uwa kuma? Ki kira ni da *Nasmat*.”

Murmushi Raudat ta mata tace “Nice name aunty Nasmat, good night.”

Da kallo kawai ta bita harta fita, tana fita ta tab’e baki tana tunano abinda ta fad’a mata, mik’ewa tayi ta cire kayanta ta fad’a toilet, ta jima tana k’arewa toilet d’in kallo ganin kamar ba wajen fitar da datti da k’azanta ba, ko bacci ya kamaka sai kayi a ciki kuma cikin nutsuwa, haka ta fara wanka kafin ta idar ta fito, jakarta da suka taho da ita ta bud’a ta shafa na shafawa ta murza na murzawa sannan ta saka rigar bacci iya gwiwa mai kyau, saida ta zauna kan gadon ta d’auko wasu magungunan mata wanda ta tanadesu dan Abbas kawai tasha sannan ta kwanta.

Suna kammala cin abinci Abbas ya shirya ya tafi taron nan, awa biyu ya d’auke shi kafin ya dawo gida, ya fito a motarshi zai shiga part d’in shi a farfajiyar gidan ya ci karo da mutum, mutum ma mace cikin shirin atamfa tasha ado, wa zai gani inba Harira ba, gidan shiru alamar kowa ya kwanta sai kukan d’awisu da talo-talon dake cikin gidan an ware musu wuri na musamman, tunda ya gane ita ce kawai ya zura kai zai wuce dan haka tayi saurin cewa “Sannu da zuwa yallab’ai.”

Tsayawa yayi kawai ya kalleta kamar mai son gane nufinta, wani farrr ta fara da ido tana takowa cikin girgiza jikinta, tabbas kayan sun amshi jikinta musamman yanzu data yi yar k’iba sun zauna mata a jiki, kwalliyar ma ba laifi sai dai kawai in baka sonta ne zaka kushe ta, mamakin irin salon da take taho dashi yake yi harta tsaya gabanshi k’amshin turarenta da baida maraba da na ‘yan bori ya daki hancinshi, muryarta ce ta dawo dashi daga d’aukaewar da numfashinshi ya kusa yi saboda bai tab’a jin turare irin wannan mai tayar da hankali ba tana fad’in “Yallab’ai, dama na ga baku dawo tare da Sameera bane, shine nace bara na jira ka dawo ko akwai abinda kake so wanda zan iya yi maka?”

Kallon mamaki da kuma yaushe yarinyar nan ta haukace yake mata? Me take nufi? Sameera ce ma take kira haka babu sakayawa? Saida ya d’an ja baya sosai ya k’are mata kallo yace “Ke! Yaushe aka haifeki?”

Sai kuwa Harira ta sake juya ido ba tace komai ba, dan haka yace “To ki koma ki tambaya dan kisan shekarunki da nawa ba d’aya bane, ki shiga hankalinki tun wuri, dan ruwa ba sa’an kwando bane, idan kuma baki ji ba, u wil regret it, that’s my last warning.”

Juyawa yayi a sukwane ya shige part d’in ya barta nan, tab’e baki tayi ta juya tace “Can ka k’arata da turancinka, ni inda zaka dinga min magana ma da turancin da zanfi jin dad’i.”

Raihan na kwance d’aki sun gama waya da mahaifiyarta, har zata kwanta dai kuma saita turawa Abdul sak’o tana tambayar ya hannunshi? Ko ba komai yaji dad’in tambayar dan hakan na nuna ta damu dashi ne, amsa mata yayi da sauk’i, Allah ya k’ara afuwa shine abinda ta fad’a ta aje wayar ta kwanta abinta.

*Washe gari* da sassafe duk yaran sun shirya suna kan dinning suna jiran isowar Dadynsu, Abbas kuma na shiryawa ya fito falonshi da niyyar fita, yanzu ma wa zai gani sai Harira wacce tunda Sameera tace mata duk aikin da zatayi b sai ya kaita ga shiga sashin Abbas ba take jin haushi, wato a lokacin da suna matsayin ma’aikata ai ita ce ma ke kula da sashin shi, kenan ita ma tana tsoron a k’wace mata miji kamar yanda ta k’wace ma Salma, dan haka yau saida ta gama kimtsa yaran da ba zasu iya shirya kansu ba ta shiga falon nashi da k’ofar ke bud’e ta falon Sameera, babu wani abu da d’akin ke buk’ata amma haka ta zage tana goge goge tana karkad’a jikinta sosai cikin doguwar rigar wani tattausan less bayan ta cab’a ado.

Saida Abbas ya rintse idonshi dan yanda k’ugunta ke rausayawa abin tayar da hankali ne, gashi har shatin mazaunin pant d’inta yana hange daga inda yake, haushi da takaici ne suka sashi daka mata tsawa yace “Ke!”

Harira da tuni tasan da fitowarshi shiru kawai tayi a tsora ce ta juyo juyo tana saki wata k’ara duk da muryar ba siririya bace da zatayi dad’in sauraro, ba kwalliyar fuskarta ce ta sake shiga madubin idonshi ba sai k’irjinta da rigar ta matseshi sosai yayi sama kamar zasu fito, tabbas mata bala’i ne, dan k’arfin da yaji lokacin daya mata tsawar nan tana juyowa sai yaji ya rasa kuzarin, wani bala’in sanyi ne yaji hannunshi sun mishi ya kasa d’aga su, da k’yar ya iya tattaro jarumtarshi yace “Lafiya? Meya kawo ki part d’ina?”

Sunkuyawa tayi tace “Ina kwana? Kayi hak’uri yallab’ai, na zo gyara…” Bai bari ta k’arasa ba yace “Kije bana so, kuma daga yau kar na sake ganinki sashi na.”

Sunkuyawa tayi alamar to kafin ta nufo shi, hakan yasa ya bud’e ido yana kallonta ya ga me zatayi, kan k’aramin teburin ne ta aje k’aramar wayarta da man goge madubi, duk’awa tayi zata d’auka ta d’ago kai taga ko yana kallonta, ganin ya kawar da kanshi yasa tace “Yallab’ai na kawo maka abincin ka nan ne?”

Kallonta yayi zaiyi magana kuma sai yayi shiru saboda abinda ya gani, haka dai ta k’arasa kwarkwasarta ta fita ta barshi, tsaki yayi a ranshi yana fad’in “Dole ma ta kori yarinyar nan wallahi, ba zan iya ba haka kawai.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231 232 233 234 235 236 237 238 239 240 241 242 243 244 245Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected