BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL
Sakinta yayi ya juya ya bar d’akin Ummy ta bishi da bala’i amma ko a jikinshi, da fitarshi kuma sai ga colonel ya iso har cikin gidan yan rakiyarshi suka shiga, saida zai shiga d’aki ya dakatar da su ya shigo ciki, saida ya gaisa da mutane sosai da yara kafin ya shiga dan yin wanka.
Ya gama wanka ya saka dogon wando da singlet zai saka riga Zeinabu sarkin tsegumi tace “Amma dai kasan duk cikin sabgar nan da za ayi mu akafi cuta ko?”
Da mamaki ya juyo ya kalleta ya dakata da saka rigar yace “Me? Cuta fa kika ce? Cutar me aka mana?”
Zaune tayi bakin gado tana fad’in “To kayi tunani mana ka gani, mu fa yara uku zamu aurar lokaci d’aya, kuma biyu daga ciki mata ne, ka kuma san auren mata yafi na maza kashin kud’i, kaga kywa ai zamu shiga uku.”
Kallon anya kuwa matar nan nada hankali ya mata? Dan shi dai inba hauka ke damunta ba baiga abun mita ba anan, da mamaki yace “Zeinabu yaushe kuma gidan nan muka fara rayuwar tsiya da talauci? Yanzu ke duk a lamarin nan kud’in da zaki kashe ne matsalarki? Ba wai farin ciki da ‘ya’yanki zasuyi aure ba, meyasa kike hakane? Ke nama ji zamu kashe kud’in, babu kud’in ne na kashewa? Ko kuma ke aka ce ki fito dasu ki kashe bare ki wa mutane iya shege, sannan meyasa bakiyi tunanin d’an uwana ba da kuma matarshi Sa’ada? Su fa duka yayansu maza ne wanda su zasu kai, ke kuma d’an ki d’aya ne zai kai biyu kuma mata zasu kawo miki abun arzik’i, mtssss, wallahi Zeinabu matsalarki tayi yawa.”
Mik’ewa tayi jin k’orafinta yau ma bai karb’u ba ta nufi k’ofar fita tana magana k’asa k’asa da fad’in “Aikin banza, ai nasan dama ba tunani gareka ba bare ka hango abinda na hango mana, indai har zamuyi yanda akeyi ne ai mazan idan sun kawo mana sai mun kusa ninka musu abinda suka kawo a cikin gara.”
Tana daf da kaiwa k’ofar taja tsaki tare da murgud’a mishi baki, da k’arfi ya juyo dan tabbatar da gaske ne abinda yaji wai, ita ma sai bayan tsakin ya fito ta fahimci bala’in data jawowa kanta, ai da wani irin k’arfi yayo kanta zai cabkota amma hukuncin ubanjigi saita zame ta juya da gudu ta fad’a ban d’aki duk da k’ok’arin shi na son cabkota, tana shiga da iya k’arfinta ta maido k’ofar ta rufe daidai yana kawowa, kile tasa ta rufe gam shi kuma ya shiga bubbuga k’ofar yana fad’in “Zeinabu ni? Ni kike wa tsaki! Zeinabu yaushe kika raina ni haka? Allah ki bud’e k’ofar nan ko na karyata.”
Wata irin jijjiga ya wa k’ofar da yasa ta fara motsi da k’arfi kamar zata karye, Zeinabu kam ciki ya d’uri ruwa sosai, tasan inhar ya bud’e to saiya karyata kam, yana cikin jijjiga k’ofar da k’arfi Sa’ada da tun farkon fara bubbuga k’ofar shi taji dan tana falon zaune ta kira Junaid tace ya zo, yana zuwa d’akin ya bud’a ya shigo da sauri ya tunkaroshi ya rik’e shi yana fad’in “Yi hak’uri dan Allah Abba, kayi hak’uri, muje ka rabu da ita.”
Wani kallo ya ma Junaid ido jawur ya fizge ya shak’i wuyan rigarshi yana fad’in “Dan ubanka waya kawo ka? Me ma ya shigo da kai? Ka zo ne ka shigar ma uwarka? To yau saina kasheta a gidan nan, nace saina kasheta idan ya so nima a kashe ni.”
Yanzu kam Junaid ya fahimci uwar tashi ta kwanto musu kura, turashi yayi ya kaiwa bango karo ya sake kama murfin k’ofar ya jijjiga da k’arfi, cikin d’aga murya yace “Shikenan, ai kin k’i bud’ewa ko, to bari kiga yanda zanyi da k’ofar.”
Da sauri ya juya kayanshi daya shigo dasu ya fitar ‘yar k’aramar bindigar dake jikin kayan ya zaro ya nufo k’ofar, Junaid na ganin haka ya shiga gaban k’ofar yana sake bashi hak’uri amma saiya ture shi gefe, ganin abun yafi k’arfin shi yasa shi fitowa yayi daidai da fitowar Hajia, da sauri yace “Hajia dan Allah ki zo kafin Abba ya kashe Umma, wallahi ranshi ya b’ace.”
Da azama ta tako ta shigo d’akin tana fad’in “Kisan kai? Karfa yaran nan ya ja mana masifa a gida.”
Tana shigowa daidai colonel yasa k’afa da k’arfi ya bangaje k’ofar, Zeinabu na jin ya bud’e ta dafe kanta da hannaye ta k’ame wuri d’aya ta rintse ido jin fitsari na zubo mata daga tsaye, shi ma kuma yana ganinta gabanshi ya saita bindigarshi ya nuna mata yana fad’in “Me na fad’a miki? Bance miki ki bud’e ba kafin na shigo da kaina, to yau zzzz…” Bai k’arasa ba Hajia ta shiga tsakaninsu tace “Ka kashe ni Hussein kafin ka kasheta, tunda so kake ka jawo mana abun kunya.”
Ganin Hajia gabanshi ya sa shi kaucewa cikin hassala ya buga bindigar a bango ya saketa ta fad’i shi ma kuma ya kaiwa bangon duka da hannunshi, a hankali Hajia ta dafa kafad’ar shi ta shafa, shiru yayi bai juyo ba hakan yasa ta kama hannunshi suka fita zuwa falo, Junaid kuma kallon mahaifiyarshi yayi cikin ladabi yace “Umma dan Allah ki rage duk wani abunda kika san Abba baya so, duk zafin zuciyar Abba kana iya zama kayi hira da shi ku fahimci junanku, amma ko yau Abba zai shigo gari sai kaji hayanuyarshi kin b’ata masa rai.”
Haushi ne yasa Zeinabu cewa “Kai ni fita ka bani wuri, tunda kana bayan uban naka saika zo ka bashi kashi.”
Tsaki tayi ta mayar da k’ofar ta rufe duk da bata rufu da kyau ba dan ya riga ya b’allata, shi kuma fita yayi ya samu mahaifin nashi zaune ya tangale gwiwoyin hannunshi kan cinyoyinshi ya dunk’ule hannunshi yana dukan d’aya hannun, Hajia ce kawai zaune tana kallon tv da tunanin idan ya sauko sunyi maganar da zasuyi akan tafiyarsu ta gobe, suna haka su Alhaji suka shigo tare da lieutenant, bai ma kowa magana ba kuma suma basu damu ba sun san kayan ne suka motsa, zaune sukayi sai Alhaji daya kalli Junaid yace “Ka kira min uwar ‘yan biyu, idan ka dawo ka kira min su kansu yan biyun.”
Sama ya haura ya samu Sa’ada can ya kirata ya dawo, b’angaren su ya nufa ya kira Ammar da Amar suma suka zo, Alhaji da kanshi ya kira Husseina da Labaran da suke tattaunawa suma kan auren Jibril da Jamila, saida suka had’u ya kalli kowa da kyau kafin yace “…
17/06/2020 à 22:08 – Ummulkhairi: ❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️
*BADAK’ALA*
❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️
*Labarin Gaske*
*NA*
_SAMIRA HAROUNA_
*Litattafan marubuciyar*
*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D’AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD’I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K’ADDARARMU_
*8* _K’ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k’ura)…_
*14* _BADAK’ALA…_
*SADAUKARWA GA*
_*AHALI NA*_
*TAURARIN NIGER*
“`(Tsintsiya mad’aurinki d’aya)“`
_Bismillahir rahamanir rahim_
_19_
“Abinda yasa na taraku dama dan na fad’a muku wani abun alkairi ne daya tunkaro mu, insha Allah nan da kwana uku zamu sake yawa a gidan nan.”
Shiru kowa yayi sai kallonshi da suke babu wanda yace wani abu, Husseina ce tace “Masha Allah, ah lallai abun farin ciki tunda zamu k’aru ne, amma ta ina?”
Kallon Hajia yayi data tsura mishi ido tana jiran tajiba daidai ba ta fara masifa, had’e rai yayi sosai dan karta kawo mishi wasa kafin ya kalli Sa’ada yace “Sa’ada, kiyi hak’uri abisa abinda ya faru, laifina ne bana mijinki ba, kamar yanda zaki ji yanzu shima haka kawai yaji na yanke hukuncin, amma na tabbata idan kuka ji dalili na zaku fahimce ni, nasan kina da ilimi kuma ba yarinya bace ke, idan har kin kama girmanki hak’ik’a zakiji dad’i sosai anan gaba, ‘ya na d’auke ki kamar yanda babba yake d’ana, ina fatan kema zaki min biyayya.”