BADAK'ALA COMPLETE HAUSA NOVEL

BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL

Da kallo ta bishi tace “Ita ce lasisin fara zawarci na.”

Duk da bai tsaya ba saida ya juyo ya kalleta ya kuma ci gaba da tafiya, zawarci? Matarshi ta shekara arba’in ba kad’an? Tayi zawarci har ta auri wani? Maganar fa ta soke shi sosai, ba dan baya son kulata ba da saiya buge bakinta, tunda dai har yanzu yana son abarsa kawai kuskurenta ne zai nuna mata, dan har ranshi yayi rantsuwa daya san abinda ya faru a lokacin *wallahi da sai Ammar yaje gidan maza* kan abinda ya aikata, yanzun ma wuri bai k’ure ba sai dai wacce zata zama tsayayyar shaidar ita ce Hamna, kuma yana tsoron shak’uwa ta yan uwantaka da jinin shi dake yawo a jinin jikin d’anta yasa ta basu kunya, shiyasa yayi fatali da maganar Ammar kawai.

Ai kuwa Ummy da gaske take, ko da ta shiga d’aki kayanta ta had’a a jaka ta fita a gidan ko Hajia bata san da fitarta ba.

Lieutenant kuma ya d’an jima d’akin Zeituna hakan ne yasa ko da ya fito ya samu d’an uwanshi ya zo da kuma Hadiza zaune suna gaisawa, Hadiza ce ta kalleshi cikin girmamawa tace “Ban ga Sa’ada ba ni ko har ta tafi aiki ne?”

Juya akalar zancen yayi da cewa “Ina mutumen ne (Ahmad)?”

Da murmushi tace “Ai ina zuwa uwarshi ta karb’eshi, tace ta tafi ta kaisu wajen Abbansu amma yanzu zata dawo.”

Jinjna kai yayi sai Hajia data sake cewa “Babba ina Sa’ada? Yau kamar ba ranar aikinta ba ai?”

“Ta tafi.” Yanda ya fad’a fuska a gimtse yasa Gambo kallonshi yace “Asibiti?”

Shirin daya musu ya tabbatarwa da Hajia ba lafiya ba, dan haka tace “Ina? Tana ina Babba?”

Cikin sanyin murya yace “Hajia ta tafi, nima ban sani ba.”

“Kamar ya baka sani? Babba zauna.”

Zaune yayi ya aje jakarshi gefe ya kalleta, cikin rashin son wasa tace “Fad’a min ina taje da safiyar nan? Ni dai banga sanda ta fita ba.”

Ba tare daya had’a ido da ita ba yace “Hajia ta tafi, akan abinda ya faru ne, ita ce mai laifi ma amma har ta tsaya gabana tana fad’in idan na gaji da ita ta tafiyarta.”

“Sai ka ce mata me?” Cewar Hajia, saida ya waina kanshi yace “Shine ta tafiyarta, tace na aika mata da takardarta.”

Da k’arfi Hajia tace “Babba, kana da hankali kuwa? Yanzu kai baka ji kunyar fad’ar maganar nan ba? Matar ta ka?”

Gambo dake kallonshi da mamaki ne yace “Wai me ya faru ne haka da zafi? d’an uwa a sani na daku baku tab’a samun sab’anin da yasa tayi ko da yaji ba, me yayi zafi haka da girmanku da komai kuna fad’an yara.”

Kallon Hajia yayi ranshi a b’ace yace “Hajia ni zan tafi.”

Mik’ewa yayi zai fita Hajia tace “Ban gama magana da kai ba zaka mik’e min a kai Hassan, zauna min kaji malam.”

Muryar da tayi magana da ita ta waccen Hajiar ce, dole ya dawo ya zauna yana sunkuyar da kai, Hadiza kam mik’ewa tayi ta kalli Hajia tace “Hajia zan jira a waje, akwai buk’atar ku tattauna.”

Cikin mutumtawa Hajia tace “Zauna Hadiza, ai ke ma har yanzu iyalin gidan nan ce.”

Murmushi tayi tace “Ban k’i ta taki ba Hajia, amma duk da haka akwai buk’atar kuyi magana tsakaninku.”

“Hadiza karki manta fa yara biyu ne dake wanda kika samu a gidan nan, sannan abinda ke faruwa yanzun yana da alak’a da d’aya daga cikin ya’yan naki, ki zauna dan Allah sai muyi magana.”

Komawa tayi ta zauna gabanta na fad’uwa kan abinda Hajiar tace, kallon lieutenant tayi tace “Kira min Sa’ada ka ce inji ni duk inda take yanzu ta zo ina nemanta.”

Wallahi wannan Hajiarsu ce ta baya mai magana d’ayan nan, in yayi wasa zai sha ashar yanzu dan haka da sauri yace “To.”

Wayar shi ya fiddo ya shiga neman lambarta, Gambo ta kalla tace “Ka kira min Ammar ka ce ya zo.”

“To.” Ya fad’a yana ciro wayarshi a aljijun balaluwarshi, yana gama magana dashi a lokacin har ya fita da yaran, sake umartarshi tayi daya kira Hamna sannan ta kalli Hadiza tace “Husseina na ciki, ki ce ta fito zamuyi magana.”

“To Hajia.” Ita ma ta fad’a ta nufi d’akin jikinta har rawa rawa yake na tunanin abinda ya faru tsakanin Ammar da Hamna daya har yasa Ummy suke k’ok’arin rabuwa da lieutenant.

Hamna ma ko da kiranshi ya shigo wayarta tana k’ofar gidan, saida hancin motar ta ya shigo sannan ta d’auki wayar, shi kuma yana hangenta ma saiya kashe kawai.

_Kuyi hak’uri da wannan, yau ne sai a slow._

*Alhamdulillah*
04/11/2020 à 14:38 – Ummulkhairi: ‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍
*BADAK’ALA*
‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍

*Labarin Gaske*

*NA*

_SAMIRA HAROUNA_

*Litattafan marubuciyar*

*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D’AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD’I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K’ADDARARMU_
*8* _K’ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k’ura)…_
*14* _BADAK’ALA…_

*SADAUKARWA GA*

‍‍‍ _*AHALI NA*_‍‍‍

✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*
_(Tsintsiya mad’aurinki d’aya)_

☆ *[ T.M.N.A]* ☆ ️

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_

_66_

Husseina ta fito ta samu wuri ta zauna, tunda sauran matan suka fahimci zaman ba dasu bane kowace tayi d’akinta, sai lieutenant dake kiran Ummy, k’in d’aukar kiranshi tayi tunaninta hak’uri zai bata, Hajia ya kalla yace “Hajia ta k’i d’auka fa.”

Wayarta ta lalubo a bayanta tana fad’in “Ban ga laifinta ba mana.”

Kallon Hajiar yayi da mamaki, wai duk abinda tayi bata ganin laifinta? Kiran Hajia kad’ai ta d’auka cikin ladabi tace “Hajia.”

Kai tsaye tace “Kina ina Sa’ada? Maza ki zo gida ina son ganinki.”

Cikin rarrabawa tace “Hajia..ina..kan hanyar…zuwa gida ne.”

“Wane gida? Sa’ada kina da gidan daya wuce nan ne? Kina da hankali kuwa? Ke yanzu dan Allah idan kika je ki ce me? Yaji kikayi? Kiyi sauri ina jiranki yanzu.”

Cikin ladabi tace “Wallahi Hajia da gaske na ke, ina cikin bus d’in da zata tafi *Arlit*, yanzu haka mun wuce *Tessaoua*.”

Shiru Hajia tayi tana kallon lieutenant da shima yake kallonta yana sauraren abinda take fad’a, sunkuyar da kanshi yayi k’asa ita kuma ta harare shi, wata shawarar ta yanke kawai bari ta barta yaje har can ya dawo da ita, kashe wayar tayi cikin fad’a tace masa “Ka shirya tafiya yin bikonta gobe goben nan, babu ruwa na da iskanci kaji na fad’a maka, kai in ba’a hak’uri da ko haihuwarku nayi a gidan ubanku ma.”

K’wafa tayi mai k’arfin gaske dake nuna ranta ya b’ace sosai, kafin wani yayi magana Hamna ta shigo tare da Ahmad, da mamakin ganin mahaifinta taje gabanshi ta zauna tana fad’in “Abba? Yaushe ka zo?”

Kallonta yayi yace “Banjour.”

Lab’e baki tayi tace “Pardon Abba, bonjour.”

Gaisawa sukayi sosai inda take kallon mahaifiyarta da mahaifinta tana jin kamar ace babu aure kan mamanta ta sake had’a aurensu, ba wai sai iyayenka sun mutu ba wani lokacin kake zama maraya, su kansu akwai abubuwa dayawa wanda sukayi musu manqué musamman daga mahaifi, lallai Ummy ta kai su kirata uwa dan ta musu abinda ta cancanci hakan, amma duk da haka uwa uwa ce, ko hakk’in rayuwa a cikinta kad’ai ya ishi d’awainiya dasu.

Sallamarshi tasa ta gyara zamanta ta tank’washe k’afafu ta matsa daf da k’afafun mahaifinta, yaran duk wurin Gambo suka nufa ya sumbaci kowane kafin yace suje sama suyi wasa zai zo ya ba kowa tsarabarsa, saida suka haye sannan Hajia ta kalli kowa tace “Abinda yasa na tara mu anan dama akan maganar yaran nan ne.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231 232 233 234 235 236 237 238 239 240 241 242 243 244 245Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected