BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL
*SADAUKARWA GA*
_*AHALI NA*_
*TAURARIN NIGER*
“`(Tsintsiya mad’aurinki d’aya)“`
_Bismillahir rahamanir rahim_
_14_
Tunda Hadiza ta tare gidan ta fahimci sauran matan da ma mutanen gidan baki d’aya hak’uri suke da tsohuwar gidan, ita kuma sai take ganin ba zata iya ba gaskiya, domin kuwa ba zatayi hak’uri da tilasta mata da akayi ba ta auri d’an ta, sannan kuma tayi hak’uri da rashin mutumcin da uwarshi ke darzawa a gidan, duk da bata nuna mishi k’iyayya a zahiri amma dai da gani kasan ba wai dan tana so bane take zaune da shi, dan ko mu’amuma ta aure ya nemeta zakaga tana irin gani kayi yanda zakayi kawai na kama gabana take mishi, haka zaka ga tana wani kakkawar da kai tana gunguni da k’ananun tsaki da baya fitowa fili, ya jima da fahimtar hakan, shi kuma Allah ya san zuciyarshi baisan lokacin data shiga ta shi zuciyar ba, dan haka yake k’ok’ari sosai wajen faranta mata rai duk da bai cika zama tare da su ba, kulawar da yake nuna mata da kaffa-kaffa da rashin son b’acin ranta yasa Hajia lura da hakan, nan ita ma saita fara kafa mata k’ahon zuk’a ta hanyar nuna mata tsana a fili da cewa bata isa ta rabata da d’an ta ba ko da me ta shigo, sam bata kula ta saboda ko ba komai babba ce ita kuma ta haifi mijinta, sai dai ita kuma bata cika yin irin bautar da take saka Zeinabu da Soueiba ba da Sa’ada, ko sun fara aikin tare zata zame ta kawo na ta fi’ilin, a lokacin Sa’ada ita ma hak’uri take sosai, badan ma karatun ta data saka gaba ba wanda Hajiar ta so datseshi, amma da k’yar Hassan ya fad’awa Suley daya fahimci tana son karatun sannan suka shawo kan matsalar, duk da jimawar da tayi bata samu ciki ba hakan bai damu Hajia ba, dan ita a ganinta ma hakan daidai ne, dan yanda ita kad’ai ma ta mallake mata d’a ina ga ta haihu, saidai bata d’aga musu k’afa har zuwa lokacin, duk wata hidima ta gidan sune har da hidimar ita kanta, idan ka same su da rana zaka rantse masu aiki ne ba matan gidan ba, gashi kuma a lokacin Allah yasa duk mazajen nasu babu wanda bai samu k’arin matsayi ba, amma haka suke rayuwar k’ask’anci kamar bayi, ko fita zasuyi sai Hajia ta bada izini, dan haka tun kana jibi zaka fita kake sanar da ita dan ta baka lokacin data ke so, girman ciki ko tsufanshi baya sa ta sarara maka da aikin gida, saika haihu kawai kake da damar yin jego na sati d’aya shima saboda idon mutane, wani ikon Allah kuma har saida Hadiza ta shekara *shida* a gidan kafin Allah ya bata cikin su Hamna, ciki ne daya bata wahala sosai, hakan yasa fa Gambo ya rufe ido ya shirya sai kawai Hajia ganinshi tayi da kaya yace zai tafi da matarshi can ya samu k’wararrin likitoci da zasu dinga dubata, a lokacin Hajia bata iya cewa komai ba saboda Suley dake wurin kuma yace ba komai su tafi Allah ya tsare, daga lokacin ta sa k’afar wando d’aya da su dukansu, ko kiranta sukayi a waya dan su gaisheta sai dai ta kashe kiran, sam ta fita a lamarinsu ta zura musu ido, shi kuma yana can duk da yana damuwa sosai da hushin da Hajiar keyi amma baya hana shi kulawa da ita, sosai yake nuna mata soyayya, amma zuciyarta kamar ta shed’an sam ta k’i saduda ta so shi daidai da k’wayar zarra, suna haka har ta haihu ta samu *Hamna* da *Amna*, yara ne da za ace basuyi goshi ba a wajen Hajia, dan da suka dawo ma dan ayi suna anan ko kallon yaran batayi ba, hakan baya musu dad’i amma ya zasuyi daya wuce rarrashi harta yafe musu, abu ya k’i ci ya k’i cinyewa, sai Hadiza tayi anfani da wannan dama ta hanyar nuna mishi gwara ya rabu da ita danya shirya da mahaifiyarshi, tambayar daya jefa mata a lokacin tasa t saurin kallonshi, domin kuwa cewa yayi “Har yanzu na kasa samun shiga zuciyarki ko?”
Kame kame kawai ta dinga yi masa har yace ta fad’a mishi gaskiya tsakaninta da Allah tana son zama da shi ko bata so, ganin ba zata iya tauye kanta ba yasa ta fad’a mishi gaskiya hak’uri take amma bata sonshi har yanzu, duk da hakan bai mishi dad’i ba amma ba zai iya tauyeta ba, dan inhar zai kasa samun zuciyarta a shekara shida duk da kyautata mata da yake, to fa baiga ranar da zata so shi ba, a wannan lokaci ne ya saketa saki d’aya yace zata iya aure idan ta samu miji, su Hamna kuma da ko arba’in d’in su ba ayi ba yace ta shayar dasu idan ta yayesu zai d’auko yaranshi, gaba d’aya kuma sai hakan bai mata dad’i ba taji jikinta yayi sanyi, amma aikin gama ya riga daya gama kuma, jin wannan labari yasa Hajia shiryawa da shi, rufe ido tayi tace ai dole sai dai ta bar su Hamna ita ta tafi saboda ta nuna mata basa buk’atar ta suma tunda ta nuna bata buk’atar su, irin tarzomar da akayi ba k’arama bace akan yaran, dan ita ma Hadiza zuciya tayi ta aje yaran tace gasu nan ta shayar dasu idan zata iya, Suley kuma da Gambo suna rarrashinta amma ido sun rufe, haka ta fita a gidan daga ita sai kayan da aka kawota da su, tace yara Allah ya raya mata su idan sun girma zasu nemeta, Hajia kuma tace ba zata hana su nemeta ba amma dai ba zata tab’a cin moriyarsu ba, bayan ta barsu da fari Sa’ada tace wai dole ta sha maganin da zai dawo mata da ruwan nono dan lokacin ita ma shiru tun su Ammar saboda ta shayar dasu Hamna, Alhaji ne yace ba zai tab’a faruwa ba, idan kuma yaran suka tasa suka zo junansu fa, kuma ko ba komai ma zasu iya had’a su auren zumunci, dan haka sai dai tasan yanda zatayi da yaran, dan ta nuna musu a shirye take yasa ta samu madara aka dinga basu, amma rainon yaran kuma Sa’ada ce keyi wacce ke karatun likitar ta a lokacin, a haka su Hamna ke wayo suna girma har Sa’ada ta so tafiya France dan zama doctorat, amma Hajia tace ina ba’a gidan nan ba, wanda tayi ma babu yanda zatayi ne, haka ta hak’ura ta barwa Allah, wanda lokacin ne kuma Hajia tace dole sai dai Junaid ya zama malamin makaranta, Amar kuma cikin ruwan sanyi ake ce shalele ya zama ma’aikacin banki, Ammar kuma da kullum suna tare da kawunshi indai yana gari babu abinda yake so daya wuce ya sa hular soja ya daidaita mata zama, sai Hajia tace ya zama likita shi yafi mishi, bore yayi yace sam sai dai ya nemi kud’i ya kai kanshi inda zai zama abinda yake so, amma haka Sa’ada ta rarrasheshi tace ya cika mata burinta sai su zama likitoci suna zuwa aiki tare, badan wannan dubara ba da fa sai dai idan sunji k’arar bindiga su fito suga Ammar ne ya zama soja, gashi Innusa da yasa ta d’auki wannan alhwashin ma ko kula da tsiyarsu bayayi, har yanzu jituwa ta kasa shiga tsakaninsu, su Ramma an jima da barin duniya, amma shi da yan uwanshi sun k’i d’aukar Suley a matsayin d’an uwa, komai zasuyi su kan wareshi ne, lokuta da dama idan zasu aurar da d’aya daga cikin yayansu sai dai yaji a gari, amma hakan baya hanashi fad’awa iyalinshi kuma ya umarcesu da su tafi, amma banda Zeeya wacce baya ma fara cewa ta tafi d’in, sai dai bamu sani ba ko anan gaba zasu iya neman alfarmar ko taimako, domin kuwa a cikin zuri’ar Innusa akwai d’alibai da dama masu neman ilimi, sannan akwai ‘yan kasuwa, masu shigowa da kaya, haka kuma ‘yan kwangila da wani lokacin kud’in da aka basu suke musu k’aranci dole sukan nemi bashi a hannun banki, sannan shi kanshi Innusa yana fama da ciwon k’afar da har ya fara shafar zuciyarshi.