BADAK'ALA COMPLETE HAUSA NOVEL

BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL

Cikin taushin murya Amna tace “Ummy kinsan yanzu ana kusan jarabawa ne, wallahi ana yawan yi mana jarabawar bazata a classe.”

Lieutenant ne yace “To akwai kud’i aljihunku ko?”

Hamna ta amsa da “Akwai Abba, sai mun dawo.”

Har sun juya zasu fita suka ji muryar Hajia tace “Ke ai kinji sak’o na ko?”

Juyowa sukayi sai Hamna da tace “Eh Hajia, na ji.”

Cike da gadara tace “Da kyau, tunda kin zab’i zama yar fashion amadadin zama matar aure sai kije kiyi, nasan dai duk tsiyar ba zata wuce uwarki ce ke zugaki ba, kuma ni nafi k’arfin ta wallahi, dan haka babu inda zaki ji har sai an gama bikin nan.”

Shiru Hamna tayi tana kallon k’asa tana gunguni inda maganar kuma ta kashe Amna, ita kullum Hajia saita zagar mana uwa ta d’ora mata laifin da bata ji ba bata gani ba, a wulak’ance tace “Ku b’ace min da gani.”

Juyawa sukayi suka fita a hanyarsu ta fita kuma suka had’u dasu Amar zasu shigo falon, gaisawa sukayi cikin mutumci kafin Hamna ta kalli Junaid sai taji kunyarshi ta kamata kar yayi tunanin ta k’i shine, shi kuma murmushi ya mata na suna cikin farin ciki kawai, fita sukayi Hamna na mamakin ko ina boss d’in yau, suna nufa inda zasu d’auki motonsu suka hangeshi yana waya.

Gabansu ne duka ya fad’i wanda a wajen Amna sabon al’amari ne daya fara zuwar mata yau, masha Allah cewar ta a zuciyarta, hak’ik’a k’ananan kaya na bala’in mishi kyau, kamar kullum kuma takalminshi k’afa ciki ne inda ya d’aure wuyanshi da cravete (nikctie) kai ka rantse *jan kunne* ne idan ba magana yayi ba, cikin tsoro Amna ke tafiya ta sanda kanta k’asa dan bata so su had’a ido, inda Hamna dake rik’e da makullin motanta take gaba sai kace idan sunje za tayi wata tsiyar, kasancewar ba tsaye yake wuri d’aya ba yana d’an kai da kawowa yasa shi d’an zaunawa kan motan nasu, suna isa suka tsaya inda Hamna ta d’an rik’e kan mota tana nesa da shi tace “Bossss…”

Da sauri ta kama bakinta dan tasan ko da gudu ya bita zai tarar da ita, shi kuma yana d’ago idonshi akan Amna ya sauke wacce ta tsaya daga gabanshi nesa da shi, ganin ta k’i yarda su had’a ido yasa shi k’arewa fuskarta kallo, saida ya gama kallonta tas ya d’an karkata idonta ya kalli Hamna dake bayanshi tsaye ta madubin moton, kowace shigar da tayi ta dace da ita, Amna kuma duk da tana jikin hijabi amma kasan ita ma yar duma-duma ce kamar ‘yar uwarta, hak’ik’a Hamna tafi haske, amma baisan dalilin da yasa yau kuma yanzu daya kalli Amna ba sai yaga duhun nata ma mai kyau ne, sannan sai yaga tafi mishi kyau akan ita Hamna, a hankali ya mik’e daga kan moton ya juyo da dubansa kan ta, babu alamar wasa bare raha, kallon da yake yamutsa mata lissafi ya mata cikin muryarshi dake tayar mata da hankali yace “Baki iya gaisuwa?”

Saida ta turo baki gaba tana zuntoshi tace “Ina kwana.”

Sake kallon surarta yayi sai yaji haka kawai ranshi bai mishi dad’i ba ganin kayan sun kama jikinta, duk da ba sosai bane suka matseta amma dayake anfitar da gurbin komai yasa komai d’in fitowa, masha Allah faffad’an k’ugunta ya kalla ta k’asan ido, da sauri ya d’ago cikin tsawa yace “Dan ubanki maza koma ki sanyo hijabi, kuma wallahi kika k’ara bari na ganki babu hijabi sai ci uwaki gidan nan.”

Juyawa tayi ta sa kukan shagwab’a harda bubbuga k’afafu take tana tafiya kamar zatayi gudu, “Shegiya!” Ya fad’a a ranshi a zahiri kuma yanda k’ugunta ke kad’awa yasa yace “Kankana.”

Dole ta tsaya ta juyo dan kiran sunan da yayi cikin wani yanayi ne dake nuna kifa kiyayeni, k’ara d’aure fuska yayi yace “Ba zaki iya tafiya a hankali bane har sai kin tashi hankalin wad’anda ke kwance k’asa?”

*Maganar nan da biyu, sai dai bangane manufarta ba*

Daina bubbuga k’afafun tayi amma bata daina saurin ba da kukan, saida ya ga shigarta ya d’an juyo a hankali, Amna na ganin zai juyo kanta tayi saurin cewa “Yah Ammar ina kwana.”

A hankali ya taka kusanta yana kallonta da mayatattun idonshi da lokaci d’aya ba zaka iya fahimtar manufar kallonshi, saida yaga ya k’ureta kad’ai ya tsaya kamar zai ci tuwo a saman kanta, Amna da ke jin kamar ta sako fitsari jira take taji yace dan ubanki bakiyi abu kaza ba, amma taji shiru gashi babu niyyar ya d’an bata wuri tasha iska, shi kuma baiwar da Allah ya mishi yasa yake iya hango yanayin da take ciki a goshinta, ji tayi yace “Kalle ni.”

Gudun laifi yasa ta d’ago da sauri ta kalleshi, kamar saukar aradu a kanta taji yace “Tun yaushe kika fara al’adarki?”

Wani bazawarin tari ne ya taho mata bata san da zuwanshi, da sauri ta rik’e tarin ta hanyar rufe bakinta gam tana kallonshi, gashi kuma yayi alamar kamar na shi yayi maganar ba, k’asa tayi da idonta ta kasa cewa komai, ji tayi ya sake cewa “Ki tabbatar kafin aurenmu kin shirya fad’a min lokacin da kike farawa, da lokacin da kike gamawa, sannan yaushe kike wankan tsarki?”

Yana gama fad’a ta hange shi cikin wannan takon nashi na in sojojin sun motsa a kanshi, baki sake ta maimaita kalmar ” *Kafin aurenmu*, kenan ma yana son auren? Anya kuwa zan iya?”

Firgigit tayi ta sake kai dubanta hanyar falon Hajia amma tuni har ya shige, yana shiga kuma Hamna ta fito da hijabi sai turo baki take, ko kallonta baiyi ba saboda fad’uwa da yaji gabanshi yayi, kamar yanda ya saba babu sallama babu fara’a ya k’arasa yana kallon kujerar Alhaji amma kuma baya nan, tun kafin ya isa kusan Hajia ya wani d’aga mata hannu irin na inka had’u da mutum a kan hanya kuna kan ababen hawa wato yar hannu, kai tsaye ya sauke hannunshi yace mata “Barka da zama.”

Ummy da tunda ya shigo dama take takaicin wannan d’abi’a tashi ta rashin sallama hararanshi tayi, wato dai baya jin magana? Yanzun ma so yake saiya ja mata bala’i sannan ya bar gidan, lieutenant ma kallonshi yake wato ita Hajiar ta ma samu barka da zaman? Su kuma ko oho ko? Juyawa yayi ya kalli Ummy yace “Na jiraki ne ko zaki taho a motarki?”

Rarraba ido tayi tana tsoron bashi amsa Hajia ta juye kanta, lura da yayi da hakan ne yasa shi juyawa ya kalli Hajia, ganin tana hararenshi tana so taga gudun ruwanshi yasa ya kalleta da kyau yace “Shi kuma wannan hararen me sunanshi?”

A hassale Hajia tace “Ubanka, nace ubanka.”

Mayar da fuskarshi alamun ko in kula yayi yace “To ba gaki ga shi ba.” Ya fad’a da nuna mata lieutenant da yake mamakin yanda Hajia ke biyewa lamarin Ammar, nuna shi tayi da yatsa tace “Kai bari kaji magana ta k’arshe, wallahi tallahi in ka sake zuwa gabana da wannan gaisuwar rashin mutumcin taka sai na ci ubanka nan gidan, Ammar ni zaka d’auka mahaukaciya? To wallahi ka kiyaye ni, idan ma k’wank’wanmai ne a kanka ka sani nawa sun dame naka sun shanye, kuma aure ne babu fashi ko zaku mutu sai an d’aura shi.”

Gyara tsayuwa yayi da kyau yace “To banda abinki Hajia na nuna miki bana son auren ne? Ba dai aure ne ba? To a d’aura, shawara kawai zan baki ki gogar da jikarki dubarun zama da ni, dan inba haka ba wallahi zata sake dawowa gabanki ta tare, aure kam ai ni shirye nake da a d’aura shi ko yau ne, lafiya ta k’alau wallahi ina da ingancin da zan iya tafiyar da mace hud’u ma a dare d’aya, ci da sha da sutura bata da matsalarsu saboda duk iyayenta masu kud’i ne, wannan hakk’in ne kawai ba zanyi wasa dashi ba wajen saukewa.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231 232 233 234 235 236 237 238 239 240 241 242 243 244 245Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected