BADAK'ALA COMPLETE HAUSA NOVEL

BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL

Tashi tayi ta fita sai Ammar daya shiga duba Alhaji yana kallon n’aurar dake haska bugun zuciya dana numfashi, dafe hannayenshi yayi kan gadon yana sauke numfashi, lieutenant ya matso yace “Ammar.”

Saida ya sake furzar da iska ya d’ago idonshi sunyi ja ya kalleshi, cikin amon murya mai gindayarwa yace “Bari na dubo likitocin.”

Ya taka da niyyar fita saiga docteur ya shigo d’akin, zaune yayi yana kallonshi shima yana duba shi, a hankali kuma saiya shiga cire mishi duk wasu wayoyi da abinda aka mak’ala mishi.

*Alhamdulillah*
14/10/2020 à 00:58 – Ummulkhairi: ‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍
*BADAK’ALA*
‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍

*Labarin Gaske*

*NA*

_SAMIRA HAROUNA_

*Litattafan marubuciyar*

*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D’AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD’I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K’ADDARARMU_
*8* _K’ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k’ura)…_
*14* _BADAK’ALA…_

*SADAUKARWA GA*

‍‍‍ _*AHALI NA*_‍‍‍

✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*
_(Tsintsiya mad’aurinki d’aya)_

☆ *[ T.M.N.A]* ☆ ️

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_

_57_

Mutuwa mai raba tsakani, sun d’auka Hajia zata iya ja musu matsala ita ma, amma sai tayi juriyar da basuyi tunaninta ba, kasancewar Alhaji babban mutum yasa cikin k’ank’anin lokaci mutuwarshi ta zaga garuruwa da dama, an shirya kaishi gidanshi na gaskiya a Maradi, dangi sun jijjiga anyi kuka kamar ba za’a tsagaita ba, magana d’aya ce ke fita daga bakin kowa ita ce “Alhaji akwai hak’uri, ga faran faran da kowa, ga hira idan kuka zauna dashi babu ruwanshi sannan ga alkairi.”

*04:30* na yamma jirginsu ya sauka, a filin jirgin aka taresu daga can zuwa mak’abarta, a wannan rana kuma a wannan lokaci duk wanda ya fito da niyyar zuwa wani wurin kuma ya had’u da motocin yan rakiyar nan, to fa dole ya tsaya ya gyara zama dan in mai saurin bacci ne ma saika fara gyangyad’i kafin ka iya wuce, mutune dai ba wata tsiya ba kace duka garin ne aka taru, mutane har saida suka koma kallon al’ajabi ba wai jimamin mutuwar ba, babu motar da babu a taron nan, idan aka wuce sai kaji kamar k’asa na girgizawa saboda rubdugun mutane, ance alamun kyakwayan k’arshe ne jama’a ma, sai dai fatan dacewa kawai amma ta wannan b’angaren Alhaji ya cinyesu har ma da d’oriya akai, hakan ma dan wasu suna wasu garuruwa basu samu halarta bane.

Gidan mutuwa ya zama kamar gidan biki, wannan jimami daga sanda aka kwantar da bijimin sa aka yanka aka shiga kiciniyar sarrafa shi, sai ga mata sun d’ora guma guman tukane na d’ori tare da girke buhun albassa ana ta yankewa, abu fa yayi k’amari sam kamar ba mutuwa bace a kayi, jimamin dai anbar na kusa dashi suyi, amma hira ta b’arke tsakanin mutane hira kuma ta duniya, ko da rana tayi aka dinga raba abinci da nama har ka ci kayi guzuri dashi, b’angare d’aya kuma masu karb’ar gaisuwa suna karb’a. *Kwana tashi* sai gashi an kwashe kwana uku, Hamna dama tare da mahaifinta da tanti Aissata suka zo, sai Amna data addabi Ammar tana so ta zo, da yace ma zai tura mata kud’i su taho tace ita ya barsu tana da kawai zata taho, da ita akayi sadakar uku wacce ta zo da jimamin mutuwar, mutane kuma suna kallonta da magana kan yanda ta k’ara girgijewa ta zama hamshak’iyar mace, haka ma yaranta sun zama yaran gwarawa dumur dumur dasu tubarkallah.

*A kwana na hud’u* tunda safe Hassana da Husseina da suka fi kowa jimamin rasa d’an uwansu d’aya daya rage musu suka kira lieutenant, Hassana ce take fad’a masa cewa “Dan Allah Alhaji maganar abincin nan yau dai kawai a canza, idan so samu ne a dafa wake na sadaka, dan ni abun ya fara damuwa wallahi, gidan rasuwa kamar gidan biki, wanda ya zo jiya shine zai dawo yau kuma ba zaka ji yayi addu’a ga mamacin ba, ba jimami babu rakashi da addu’a, shikenan dai shi daya tafi shi ya tafi kawai, ina ganin idan aka rage tukanen da canza abinci kaga wani abu ya sauya.”

Cikin ladabi lieutenant yace “To Hajka ya za ayi kenan? Har munyi waya da wanda yake kawo mana shanun, yanzu nasan yana daf da kawowa kuma babu dad’i ace ya koma da ita.”

Husseina ce ta kalleshi tace “To ai ba sai an yanka ba, za’a iya ajewa har wani lokacin.”

Murmushi yayi ya kalleta yace “Hajia mu zamuyi kiyonta ne? Kawai ku hak’ura na yau kad’ai sai a dakata.”

Shiru sukayi cikin rashin jin dad’i, fita yayi k’ofar gida sai Zeituna dake jinsu tana wankewa Fatima hannaye ta matso tace “Hajia indai kuna son a dakatar dashi yau to ba Abban Fatima zaku ma magana ba, dan ba zai iya ba shi.”

Kallonta sukayi Husseina tace “To wa zamu fad’a ma? Shine babba yanzu kuma mai fad’a aji.”

Dariya tayi tana kallon fuskokinsu tace “Ku ga Ammar, shine zai iya kawai, tsaf zai muku yanda kuke so, amma gaskiya nima abun ya fara hawa min kai na, wallahi idan ana cin abinci wani ya shigo yana addu’a ga mamacin amsawa da Ameen ma wahala yake.”

Murmushi Husseina tayi tace “Kin ce wani abu kema, tabbas shi zai mana maganin al’amarin, amma akwai buk’atar mu rufe idonmu da kunnuwanmu kan abinda zai fad’a.”

Daruya Zeituna tayi sai Hassana da tace “Kar mu musa ya ma mutane rashin kunya aje ana fad’armu da sharri.”

Husseina ce tace “Zai aika, amma kuma Ammar yana aiki da ilimi ai, yana saka komai a muhallinsa ne.”

Kafin su ce wani abu kam ya shigo gidan d’auke da Abba da yafu rigima sai Imam yana jaye dashi, kallonsu yayi yace “Hajiyoyi barkanku.”

“Barka Ammar, zo.” Cewar Husseina, matsowa yayi yana kallonsu yace “Allah yasa dai ba wasiyya ce zaku bar min ba kuma, dan ba zamu bari ku tafi yanzu ba ku kad’ai kuka rage mana.”

Dariya sukai sai Hassana da tace “Idan mun tashi tafiya ka rik’e mu to.”

“To ba laifi.” Ya fad’a yana aje Abba, zai fashe da kuka ya sake yin sama dashi yana kallonshi yace “Allah ba dan mai sunanka nan ina k’aunarshi ba da na zabgeka da mari, kaga yaro sai jarabar son jiki kamar mace.”

Dariya sukayi sai Husseina da tace “Kaga magana zamuyi.”

Kallonsu yayi d’aya bayan d’aya yace “Wa kuke so a kashe muku?”

“Kisa kuma?” Cewar Hassana, Husseina bata damu ba dan ita kayan gidansu ne taji fiye da haka, nan ta fad’a mishi abinda suke buk’ata da tattaunawarsu da mahaifinshi, saida ya gyara tsayuwa yace “Ku fad’i me kuke so ayi to? A watsa kowa ya tafi gidanshi? Ko kuma a musu rashin mutumci mai sanyin gaske da zaisa kowa ya tafi yana jimami? Ko kuma Ko kuma ya kike so.”

Da mamaki al’amarinshi Hassana tace “Yanzu duk zaka iya yin haka? To tayaya?”

Kallonta yayi yana dariya yace “Idan so kike na tashe su ta tashin hankali, barkonon tsohuwa kawai zan sa musu kowa ya watse, ko kuma na musu turaren wuta amma fa na ‘ya’yan tattasai, ko kuma na samu mata na biyasu suyi fad’a kamar masu aljanu.”

Kallonta yayi yana zaro ido yace “Ke Hajia abun fa dayawa da zan iya yi.”

Da sauri tave “A’a to ba haka muke so ba, kawai muna so muga gidan yayi kama dana mutuwa ne.”

Kallonta yayi yace “To ku dafa wake, sannan ku samo aduwa da yalo (d’ata) da magarya ku rarraba ma kowa ku ce kayan da Alhaji yafi so ne.”

Yana yayi hanyar b’angarensu Hassana tace “To ai kar mahaifinka kuma yace ayi girkin.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231 232 233 234 235 236 237 238 239 240 241 242 243 244 245Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected