BADAK'ALA COMPLETE HAUSA NOVEL

BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL

Tashi tayi ta fita ita kuma ta d’auki waya ta kira waziri, yana danna ok ya sake danna wurin nad’ar duk maganar da zasuyi kafin yayi magana, cikin tashin hankali tace “Waziri ka ce na bar komai a hannunka, amma gashi kana neman ka mana kwance da aiki, ko kasan cewa takawa ya nemi ganin liman? Yanzu haka suka turakarshi.”

“What!” Cewar waziri, sausauta murya yayi yace “Ki gafarce ni uwar d’aki, yau ba sai gobe ba zan miki maganin matsalar nan.”

“Ka tabbatar?”

“Na baki tabbacin haka.” D’if ta kashe wayar, sai lokacin kuma ta tambayi kanta “Amma me yasa baki tambayeshi meye zaiyi ba?”

Shiru tayi tana tunani kafin daga bisani ta d’aga kafad’a irin bai dameta ba tare da cewa “Koma me zaiyi indai zaisa a fasa auren kuma naga yarinyar can Ameera cikin garari to hakan ya isheni.”

A wajen takawa da liman kuma sun jima suna tattaunawa kafin ya mishi maganar neman auren Safiyya, nan liman ya nuna mishi ba komai ya kuma gamsu da bayanan takawa, amma duk da haka saida yace idan har akwai matsala to gwara abar maganar, takawa ya nuna mishi babu komai kawai suyi musu fatan alkairi, da haka takawa ya nemi alfarmar a d’aura auren nan kusa, amma liman yace a bashi lokaci dan sanar da mahaifiyar yarinyar da ita yarinyar kanta, cikin mutumta juna suka gama tattaunawarsu liman ya bar takawa lafiya.

Bayan tafiyar liman haka kawai takawa ya nemi ganin duka iyalin na shi a turakarshi, nan suka hallara uwaye da ‘ya’ya maza da mata, nasiha ya dinga musu da gargad’i da jan kunne akan rayuwa, daga bisani ya musu addu’a tare da jadadda musu rik’o da zumunci, kar su yarda su bari mulki ko abin duniya ya shiga tsakaninsu, da haka kowa ya tashi ya koma inda ya fito suka bar takawa lafiya k’alau.

Wannan ganin shine na k’arshe da suka mishi da numfashi a tare da shi, domin kuwa waziri ne ya biya wasu yan daba guda biyu sukayi shiga irinta fadawan gidan aka shigo dasu gidan a motar dreba ta kai yara makaranta, wajen takawa suka shiga suka taushe mishi kai da pillow har saida ya daina numfashi, tunda asuba kuma aka farga da rasuwar takawar, liman daya zo masallaci da k’arfin gwiwar sanar dashi kowa ya amince, kuma bayan nan yayi istikhara kan lamarin, duk da ubangiji ya nuna mishi wani duhu a cikin abun amma kuma hasken dake ciki shi yafi yawa, dan haka ya zo da niyyar idan sun gama sallah ya fad’a mishi ya amince ko juma’ar da zata zo ma za’a iya d’aura auren ba damuwa.

*Abuja*

Tunda asuba da sukayi sallah sukayi karatu suke zaune falo cikin raha da k’aunar juna, Abbas ne ya kalli Raihan yace “Mama na wai har yanzu sakamakon na ku bai fito bane?”

Cikin sakin fuska tace “Dady yau zai fito, anjima kad’an zamu je mu dubo.”

Kallon Abdul yayi yace “Abdul, anjima ka shirya zamu fita tare da kai a motarka.”

Da girmamawa ya amsa da “Ok Dady, zuwa k’arfe nawa?”

Kallonshi Abbas yayi yasan ya tambaya ne dan ya shirya kafin lokacin, dan haka yace mishi ” 08:00 pm.”

Jinjina kai yayi yace “Ok Dady.”

Cike da kunya Raihan ta kalle shi tace “Dady, alk’awarin mu?”

Da mamaki yace ” Wane alk’awari kuma nayi mama na?”

Sanda kanta tayi k’asa cikin kunya tace “Dady u promise me zaka fitar damu abroad idan result d’in mu yayi kyau.”

Murmushi yayi yace “To banda rigimar mama na ai result d’in bai fito ba, ki jira ya fito sai mu gani.”

Cikin sangarta tace “Dady gaskiya mun fasa zuwa abroad d’in, mu *Niger* muke so mu tafi.”

Murmushi yayi kafin yace wani abu Ammie dake zaune tace “Shawara mai kyau, kinga kenan lokaci yayi da zaku kaiwa auntynku ziyara.”

Rauda ce da sauri tace “Wace auntynmu kuma?”

Hararanta Ammie tayi tace “Husna da zatayi aure niger ba dalilin auntynku dake aure a can bane ita ma harta samu miji a can.”

Cikin yanayin na tuno Rauda tace “Ohhh hakane fa, ki ce aunty *Khairiya* (‘yar Bakura yaya ga Husna), gaskiya indai hakane aunty Raihan zanje tare da ke nima na ga niger.”

Cikin ruwan sanyi Raihan tace “Babu inda zaki bini yarinya, ki jira idan auren Husna ya tashi saiku tafi tare da Ammie.”

Abbas ne yace “To ai ko ke baza ki ba sai auren ya tashi, in ya so daga basraba saiku wuce niger d’in.”

Turo baki tayi tace “Amma dai Dady za’a baro ni can wurin aunty Khairiya ko?”

Mik’ewa yayi yana fad’in “U have a choice.” Ganin ya nufi kitchen yasa Khalifa cewa “Dady kayi b’atan kai, nan fa madafa ce.”

Juyowa yayi yace “Wajen matata zanje, dukanku nan kun manta da ita tana can tana faman girka mana abinda zamu ci.”

Dariya Khalifa yayi ya d’ago mishi yatsa irin yace “Fatan alkairi Dady, amma fa banda fad’a kuma, kar ku zo ku rikice mana sai munje rabo.”

Dariya Abbas yayi ya mishi dak’uwa yana fad’in “Hancin ubanka Imran.”

Yana bud’a k’ofar kitchen d’in Harira ce ya fara hangowa suna ta kai da kawowa, wani bak’in ciki ne yaji ya taso mishi tare da tuna abubuwan da suka faru a baya, k’aramin tsaki yayi ya juya zai fita sai kuma Sameera ta juyo, murmushi ta sakar masa ta mik’awa Razeena had’in kabejin da tayi tace “Ki saka a fridge kafin a kammala sauran.”

Karb’a tayi ita kuma ta juya wajenshi tana ci gaba da murmushi harta isa tana fad’in “Barka yallab’ai, har kun kammala karatun?”

Hannunta kawai ya kama ya nufi wajen cin abinci da ita, Harira na ganin haka cikin dubara ta aje aikinta ta bi bayansu, dan dama ana aikin banda hararan Sameera babu abinda take tana ayyanawa a ranta wai ita ce mai bayar da oda a duk fad’in gidan nan, lab’ewa tayi tana jin me suke fad’a, Abbas ne cikin rashin son magana yace “Sam, dan Allah me zai hana ki sallami yarinyar can? Idan taimakonta kike so kiyi why not ki bata kud’i tayi sa’a, amma dai ta bar gidan.”

Da mamaki tace “Why? Me tayi kuma yanzu?”

K’ura mata ido yayi yace “Tambayata ma kike? Kinga, ina so ne nasan zaki iya sallamarta ko kuwa?”

D’an had’e fuska tayi ta turo d’an bakinta gaba tace “Please sir forget about Harira, mun riga da mun gama maganar nan fa, kuma fa ni bance kai zaka biyata kud’in albashinta ba, so dan Allah ka manta kawai.”

Wani kallo ne ya mata baki bud’e sai yayi kamar zai girgiza kai sai kuma ya fasa, wai Sameera ce ke fad’a mishi ai ba shi zai biya mai aiki ba, sai lokacin ya girgiza kanshi tare da sakin mamakin dake kan fuskarshi yasa hannu ya shafi yalwataccen gemunshi yace “Ok, duk abinda kikayi d’aya ne, amma ki sani duk abinda zaije ya dawo babu ruwa na ni.”

Da k’arfi ya fara takawa da nufin tafiya b’angaren shi, da sauri ta rik’e hannunshi a lokacin kuma Harira dake lab’e harta koma kitchen, kafeta yayi da ido fuska ba annuri, ita kam cikin kwarkwasa tace “Do something now, ka samu kayi wanka kafin ka fito na had’a maka break a part d’in ka, dan bana son yara ma su dameka.”

Fizge hannunshi yayi yana fad’in “Sai me? Ina ruwanki idan sun dame nin?”

Juyawa yayi zai fice ta bishi da murmushi tana fad’in “Kayi wankan fa, yanzun nan zan kawo maka break d’in.”

Juyowa yayi harda dafe k’ugu yace “Mayunwaci ne ni? Kinga yunwa a jikina ne?”

Gimtse dariyarta tayi ta girgiza mishi kai alamar a’a, saida ya sake juyawa tace “Allah dai ya huce zuciyar mijina.”

Cak ya tsaya ba tare daya juyo ba, wato ta mayar dashi wani shagirigirbau, sake rik’e k’ugun shi yayi ya juyo yana kallon cikin idonta ya nunata da yatsa yace “Billahil-azeem idan ban b’arar dake ba ki ce d’an iska ne ni.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231 232 233 234 235 236 237 238 239 240 241 242 243 244 245Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected