BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL
Tana kallonshi ya fizgo d’an kwalinta ya jawo kanta ya matse a tsakiyar hammatarshi yasa kallabin ya fara darzar mata fuska yana fad’in “Bak’ar munafuka aiken Hajiar ne zakije sai kinyi kwalliya? Ko yau ma a matsayin kankanar kika fito daga gidan?”
Saida ya gama ya tureta ya jefa mata d’an kwalin, da k’yar ta bud’e idonta saboda tumurmusar da fuskarta tasha, d’aukar kallabin tayi ta d’ora akai a lokacin sun fara tafiya, babu mai magana su dai a haka suka isa shagon Ilu, fitowa tayi ta tunkari shiga shagon, Ammar dake kallonta ganin yanda rigar ta fito mata da surarta ga kuma wani namiji a cikin shagon shima yana siyayya hakanne yasa shi jin wani takaici, tsaki yayi ya daki sitiyarin motar yace “Uban wace ta fito a haka ma? Wato kankana zata koya miki ko?”
K’wafa yayi yana ci gaba da kallon yanda take murmushi suna gaisawa da wannan mutumin, wanda rabon ayi ne kawai yasa Amna gaishe shi ya amsa, ya gama siyayyarshi ya kalleta yace “Hajia sai anjima ko? Gashi zamu rabu bansan ko sunanki ba?”
Murmushi tayi tace “Allah sarki yaya na, suna na Amna.”
Cike da zolaya yace “Amna zanyi mata ta biyu dake idan kin amince? Ko zan samu lambar wayarki?”
Jim ta d’anyi tana kallonshi hakan yasa ya mik’o mata wayarshi yace “Da gaske fa nake, ki taimaka ki saka min sai muyi magana a waya ko? Dan bai kamata muyi magana akan titi ba.”
Ammar da tunda yaga hirar ta k’i k’arewa gashi dama tun jiya yake neman abokin masifa sai yaji kawai yarinyar ma ta raina shi, a fusace ya fito ya nufi shagon, kafin ta karb’i wayar Ammar yayi wuf da ita sai kuwa yayi cillin tsiya da ita akan titi, mutumin bai gama fahimtar meya faru ko zai faru ba sai kuwa yaji Ammar yayi sama da shi ya dasa a k’asa, kafin dai ya ankara da abinda ke faruwa Ammar ya fara kai mishi naushi a fuska yana fad’in ” Kai kwarton ina ne? Daga ganin yarinya kawai sai yi mata magana, kasan wacece ita?”
Ledar dake rik’e a hannun mutumin wanda yanzun akayi fatali da ita Ammar ya jawo, hannu yasa ciki ya rarumo wata leda kamar balam-balam ya buga mishi a fuska, sai kuwa man gyad’ar dake cikin ledar ya tarwatse a jikinsu dukansu, Ilu dake ta k’ok’arin d’aga Ammar daga jikin mutumin da shi yake k’ok’arin ya tashi amma Ammar ya hanashi damar hakan, mutanen dake kusan nan ne suka sukwano da gudu suka zo rabo, da k’yar suka tayar dashi daga jikin mutumin shi ma ya tashi, fad’i yake “Matar tawa zaka wa iskanci? Qur’ani saina kashe ka.”
Jin yana fad’in matarshi ce yasa mutanen ganin kamar waccen mutumin ne baya da gaskiya, dan haka suka jawo Ammar da k’yar suka turashi motar shi, Amna dake tsaye cikin shago har ta fara shashek’ar kuka wani ya kalleta yace “Dan Allah madame ki wuce ku tafi, ki samu ki kwantar masa da hankali, kuma ko da kunje gida kada ki biye masa, dan halin da yake ciki zai iya illataki.”
A firgice ta sake kallon mutumin tana maimaita kalmar ” *Illataki*.” Tasan babu abinda zai hana ya illatatan kuwa, dan haka ta girgiza kai tace “A’a, ya tafi kawai zan zo a bayanshi.”
Daga cikin mota Ammar yake iya fahimtar me Amna ke nufi, sake dantse leb’en shi na k’asa yayi bala’i kawai yake nema da mai yi, ganin bata da niyyar fitowa yasa shi fitowa daga cikin motar da k’arfin bala’i ya tunkari shagon, wannan mutumin da mutane suka zagayeshi har da Ilu mai shago saida gabanshi ya fad’i dan ya d’auka wurinshi ya koma, kai tsaye cikin shagon ya shiga, Amna na ganin haka ta durk’ushe ta had’e hannayenta tana fad’in “Ka dubi girman Allah y..ahhhhhh.” Ta saki k’ara saboda jawo hannunta da yayi da k’arfi, saida ya bud’e motar ya wurgata ciki ya zagayo ya shiga, da wani irin bala’in gudu ya fizga wanda yasa hankalin mutane dayawa komawa kan motar, wasu tuni suka fara jin tausayin yarinyar dansun san wannan ta shiga uku.
Saida sukayi nisa inda babu mutane ya taka birki ya kalleta a matuk’ar zafafe ya daki k’irjin shi yace ” Amna ni zaki rainawa wayo? Ni zaki wulak’anta a idon jama’a? A gaban ido na ki tsaya hira da wani har kina neman bashi lambarki, bayan kuma kinsan ke d’in *tawa*, tawa ce mallaki na, ko gani kikeyi waccen banzan zai fini iya hawa ruwa cikinki ne? Gani kike zai fini iya sukuwa a kanki kenan?”
Amna banda girgiza kai babu abinda takeyi, a fusace ya kwad’a mata marin da yasa jinta d’aukewa, ta dafe kunci kenan taji ya shak’o wuyanta da hannu biyu, cikin azaba ta zaro ido ta kama hannayen nashi da nata hannayen taa neman ya saketa ta numfasa, cikin k’aramin lokaci ta fara fafutukar neman numfashi dan ba k’aramar shak’a ya mata ba, shi kuma cikin hargagi ya kawo bakinshi daf da hancinta yace “Saurare ni da kyau Amna, ke da gangar jikin ki nawa ne, duk da akwai inda zuciyata tafi karkata, amma ki sani tunda kakarki tace ta bani ke wallahi kin zama tawan, saina moreki ko da baki son haka.”
Wurgata yayi saida kanta ya bugu ga gilashin motar, k’asa tayi da kanta tana sauke numfashin wahala, jan motar yayi suka isa gida, yana paka mota ta fito da sauri ta nufi falon Hajia, ganin yanda kunkuminta ke juyawa ya k’ara tunzurashi, kenan shima waccen mutumin abinda ya gani kenan? Ai da sauri ya fito yana fad’in “Ke ke! Zo nan.”
Tsayawa tayi ta kasa motsawa tana kallonshi wasu hawayen na zubowa, yana kawowa daf da ita ya kamo rigarta yace “Uban wa ma yace ki fito haka? Iyee! Wa yace ki fito haka kina tallar kanki?”
Shiru tayi sai sharar hawaye da take, haushi ne yasa shi ciro takalmanshi ya gaura mata a fuska, wata razananniyar k’ara ta saki ta dafe kunci, sake jibga mata shi yayi a baya hakan yasa ta zabura ta zube kwance a wurin, k’afa yasa ya fara harbinta yana fad’in “Wannan rigar data dace ki fita da ita ce? Ke bari kiji daga yau ba zaki sake fita daga gidan nan ba, kinji ni ko.”
Jin kururuwar Amna yasa mutanen gidan fitowa suka kawo mata d’auki, ganin abinda ke faruwa yasa Ummy tahowa da gudu ta durk’usa ta rumgumo Amna, babu namiji ko d’aya a gidan sai yaran hakan yasa Ummy kallonshi cikin b’acin rai tace “…
*Addu’arku yan uwa.*
22/06/2020 à 17:26 – Ummulkhairi: ❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️
*SANIN MASOYI*
_(sai Allah)_
*BAYA DA K’URA*
❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️
*NA*
_SAMIRA HAROUNA_
*Litattafan marubuciyar*
*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D’AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD’I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K’ADDARARMU_
*8* _K’ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k’ura)…_
*14* _BADAK’ALA…_
*SADAUKARWA GA*
_*MASOYA NA*_
_Bismillahir rahamanir rahim_
*TAURARIN NIGER*
“`(Tsintsiya mad’aurinki d’aya)“`
_12_
Ma’aruf ne yace “Wai ke yaushe ne zaki fito da kud’in nan a raba kowa ya kama gabansa?”
Ba tare data kalleshi ba tace ” Kana gaggawa ne da son samun naka kason?”
A d’an hassale yace “Ban gane? To idan ba’a raba ba uban kud’in zasuyi a account d’in? Kinga ki fito dasu kawai kowa ya d’auki nashi ya san inda dare ya masa.”
Aje wayar tayi ta zaburo tace “To idan fa na k’i? Ai dai kasan kud’in a account d’ina aka saka ko? Kuma sai ni ce ke da damar cirewa? Dan haka ka bini a hankali har lokacin da naga dama sannan na fito dasu mu raba.”