BADAK'ALA COMPLETE HAUSA NOVEL

BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL

Sam Suley baya dawowa idan ya fita sai yamma, amma a ranar mantuwar da yayi tasa shi dawowa gidan lokacin da bai kamata, bai samu kowa a tsakar gidan ba dan haka ya shiga d’akin shi dake farkon shiga gidan, ya d’auko sak’on ya fito ya rufe d’aki zai juya kenan yaji sauti kamar kukan Zeeya’atu, A hankali ya dawo ya d’an daga k’afafun shi ya lek’o ta katangar data mishi shamaki da nasu d’akunan, ashe ciki ne da ita mahaifiyarta kuma ta amso mata maganin gargajiya dan cikin ya zube, ganin jini duk ya b’ata mata jiki ga bala’in kukan da take uwar na k’ok’arin shigar da ita d’aki yasa shi sukwanowa da nufin taimaka musu, yana daf da isa wurin su basu san da shi ba mahaifiyarta tace a harshen buzanci “Dangana mana Zeeya, ke da kin samu ma cikin zai zube.”

Duk da bai iya komai a hausarsu ba amma yana jin d’aid’ai, a cikin hakane ma ya gane ta ambaci sunan ciki, da kuma zubewa amma sauran kam baiji komai ba sai dai kasancewar shi matashi mai matuk’ar basira da d’aukar duk abinda yaji yasa ya hardace kalaman data fad’a a buzancin, juyowa yayi ya fita ya barsu nan, yaje kasuwa ya kai sak’on yana cin abincinshi na rana tare da wani shi ma yaron Alghabit ne, da k’yar yaron ya fahimci abinda suley ya fad’a mishi yace yana son sanin fassarar , haka dai ya had’a haussar da k’yar ya fad’a mishi abinda ake nufi, sosai wannan al’amari ya girgiza shi ya kuma yi niyyar fad’awa mai gidanshi.

*K’addara ta riga fata*

Ko da ya samu alghabit dan sanar dashi sai ya katseshi tare da cewa ya kira mishi liman, bayan sun dawo tare da liman ya kira Zaha da Zeeya, bud’ar bakin Alghabit shine ya baiwa Suley ‘yarshi Zeeya’atu wacce yafi so da k’auna, kuma baya buk’atar komai daga gare shi sadaki ma shine zai biya a matsayinshi na uban Suley, da sauri Suley ya kalleshi gabanshi na tsananta bugawa, juyawa yayi a hankali ya kalli Zeeya wacce take jin kamar ta mutu tsabar bak’in ciki, amma son nuna ita saliha ce yasa ko d’agowa ba tayi ba, zaha kuma kuma ba tace bata ji dad’i ba ba tace taji dad’i ba, kowa da abinda yake tunanin a zuciyarshi har Alghabit ya katsesu da cewa zai basu gidan da zasu zauna kuma gidan ya mallakawa Suley halak malak, sannan ya k’ara da cewa ya ware mishi jari mai yawa da zai tsaya da k’afar shi shima, wannan abun ne yasa Suley yin shiru ya karb’i auren Zeeya, gashi kuma Alghabit yace za’a d’aura auren juma’a ne ba b’ata lokaci.

*Allah ka gafarta mana.*
10/06/2020 à 12:07 – Ummulkhairi: ‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍
*BADAK’ALA*
‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍

*Labarin Gaske*

*NA*

_SAMIRA HAROUNA_

*Litattafan marubuciyar*

*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D’AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD’I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K’ADDARARMU_
*8* _K’ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k’ura)…_
*14* _BADAK’ALA…_

*SADAUKARWA GA*

‍‍‍ _*AHALI NA*_‍‍‍

*TAURARIN NIGER*
“`(Tsintsiya mad’aurinki d’aya)“`

_Bismillahir rahamanir rahim_

_13_

Lafiya lau Suley ya zo maradi kuma wannan karan tafiyar tashi tayi goshi, domin kuwa da idonshi yaga k’anwar shi da irin mummunar rayuwar da take, wacce a lokacin take d’auke da yaronta Labaran daya ke da shekara d’aya da haihuwa, wani ikon ubangiji cikin sauk’i Suley ya shawo kanta suka dawo gida tare, amma bata yarda ta biyo shi gidan mahaifinsu ba saida ya tabbatar mata da yana da kud’i zai siye musu gida su zauna tare saiya kawo iyalinshi, kasancewar lokacin akwai albarkar rayuwa yasa ya siye lafiyayyen gida kuma a farashi mai sauk’i, gyara yasa aka ma gidan sosai tare da ware d’akuna uku, nashi, na Zeeya, na Husseina, saida aka gama gyaran gidan Husseina ta tare a ciki sannan ya juya ya koma agadez dan sanar da mutanen can halin da ake ciki tunda ba waya ke akwai ba a lokacin, nan Husseina ta ci gaba da zama a gidan tana jiran dawowarshi, babu wani abu da bai bar mata ba duk dan tsoron karta sake sub’uce musu, wanda wannan zaman da tayi kuma mutane aka sake d’ora mata ido, dan dama gidan daya siye ba nesa ne sosai da gidan nasu ba wanda yanzu daga Ramma sai Innusa a gidan da matanshi biyu, haka yaje gida lfy kuma tun a zuwanshi iyalinshi Zeeya ya fara yi wa magana akan komai, kuskuren da yayi shine sanar da ita da yayi halin da Husseina ke ciki tunda farkon abinda ya faru har k’arshe, sannan yace a matsayinshi n’a mijinta dole ta shirya su koma mahaifarshi tare.

Kamar dai yanda yasan zai faru hakane kuwa, domin direwa tayi tace Allah ya tsareta da komawa garinshi ta bar na ta garin, kwana hud’u ya d’auka yana lallab’ata kan ta shirya su tafi amma tana botsarewa, dan haka k’arshe ya samu iyayenta ya fad’a musu komai da ake ciki, Allah sarki dattijon arziki Alghabit, nan ya rufe ido duk da son da yake mata ya mata tatas tare da bata umarnin ta had’a kayanta su tafi, sannan yace Suley zai iya siyar da gidan daya bashi saiya k’ara ya ci gaba da kasuwancinshi, haka kuwa akayi sai dai hakan ya d’auke shi kusan wata d’aya kafin suka d’auko hanya kuma suka zo da izinin ubangiji.

Duk da a lokacin ana ganin yara ‘yan biyu, amma ganin ‘yan uku kam ba’a cika samu ba, dan haka wannan yara na Suley sai suka samu farin jini a cikin unguwarsu fiye da kima, gasu kuma dama sak mahaifiyarsu suka d’auka buzuwa jawur da su kuma tub’ur tub’ur, hakan yasa mutanen sintiri cikin gidan ana duba yaran wasu ma har uwar kallonta suke suna son tayi magana suji harshenta da hausarta ke da ban sha’awa da dariya, sai dai ba anan gizo yake sak’ar ba, tunda suka zo ta ga d’akin daya fitar ma da Husseina ma had’e yake da nata saita mayar da ita kamar kishiyarta, wani haushinta take ji tare da k’yamarta, ita ma Husseina a lokacin da sauran d’anyan kai na rayuwar da tayi saiya zama babu ruwanta da harkar matar yayan nata, dan haka babu mai shiga shirgin kowa, hatta yaranta Zeeya bata bari ko da rarrafe suje d’akin ta, suna dosa zata taro su tana habaici da bak’ak’en maganganu a harshenta na buzanci, Husseina kuma tunda ta fahimci yayanta ma zaman hak’uri yake da ita kuma kullum yana cewa tayi hak’uri da halin Zeeya’atu sai kawai take ba banza ajiyarta, duk da zamansu gida d’aya baisa ta d’aga mishi k’afa ba na salon rashin mutumci, zai kawo abinci mai rai da lafiya ta sarrafa amma idan ta gama sai tace bata dafa da shi ba sai ita sai ‘ya’yanta, shi kuma sai yace yaji dad’i tunda ma an dafa da ‘ya’yan nashi, maganar saduwa kam shi har ma ya manta rabon daya kusanceta, dan tun kafin su fahimci tana da ciki, yanzu kuma daya nuna mata buk’atar shi sai tace ai ina, bata sake shirya haihuwar wasu yaran ba, idan ya isheta da magiya saita dinga cewa wai ai da karuwa a gidan yaje ya biya kud’in shi mana ya samu nutsuwa, hakan yana k’ona masa rai sosai, da wannan rayuwa har ya saba da shan jar kanwa da lemun tsami, Husseina kuma ta fad’awa yer uwarta Hassana wacce ke gidan aurenta ita ma halin da d’an uwansu ke ciki, shawartarshi sukayi yayi aure, kuma bai watsa musu k’asa a ido ba, sai dai Allah ya hukunta Zeeya ita ce matarshi ta har abada a duniya, watak’ila tanadin da ubangiji ya mishi ne mai girma a lahira, shiyasa duk yarinyar daya nema maganar bata zuwa ko ina sai a barta, harya gaji yace ya hak’ura ba zai zama kamar mane-min mata ba kullum a hanyar zuwa gidan yan mata, mutane kuma da ‘yan uwa sun alak’anta hakan da Zeeya wacce take kallonsu tace eh tabbas ita ce, ba zai tab’a had’a ta da wata mata a duniya ba, kuma har ga Allah babu boka babu malam a lamarinta, kawai tana tauna tsakuwa ne dan aya taji tsoro, k’iyayyar Husseina ta sake hudawa ta shiga zuciyar Zeeya a sanda duk in ta k’i bashi abinci ita take bashi, ya zamana ma harda rana ita ke dafawa tana zuwa kasuwa da kanta tana kai mishi, hakan yasa take ganin ba tada maraba da kishiyarta, saidai duk masifar da take daga Suley har Husseina babu mai tanka mata.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231 232 233 234 235 236 237 238 239 240 241 242 243 244 245Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected