BADAK'ALA COMPLETE HAUSA NOVEL

BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL

*CI GABAN LABARI*

Koda suka shiga b’angaren su kowa d’akin shi ya nufa ya shiga wanka, sai dai babu mai kuzari a tare da shi har suka fara fitowa, Junaid ne ya tarar da Jibril zaune ya k’urawa tv ido, zaune yayi shima ya kalleshi yace “Jibril tunanin Amna kake ko? Kayi hak’uri kaji, watak’ila hakan shiya fi zama alkairi a wajenka, muyi addu’a kawai Allah ya bamu hak’uri da juriyar cin wannan jarabawa.”

Numfashi ya sauke mai k’arfi ya kalleshi da murmushi yace “Sam d’an uwa ba abinda nake tunani ba kenan, yau ina cikin farin ciki Junaid, ni da ban tab’a ganin soyayya daga wurin Hajia ba, yau sai gashi ta kalleni tace ta bani Jamila, wacce daga tsatsonta ta fito, gaskiya naji dad’in haka, duk da ban samu Amna ba amma nayi farin ciki sosai da hakan.”

Amar daya shirya zai fito ne yaji suna hira dan haka ya tsaya yana saurare, Junaid ne yace “Ni ma ban k’i Hamna ba, amma ka tayani tunani mana, yanzu me iyayen Maryama zasuyi tunani? Zasu d’auke ni mak’aryaci kenan d’an k’ananan mutane? Sannan ita idan ta jini shiru za tace na gudu kenan ko kuma dama mayaudari ne ni? Wannan abun nake ta tunani wallahi.”

Cike da nuna damuwa Jibril yace “To meye abunyi yanzu? Gaskiya bai kamata ace ka bar Maryama a wannan rayuwar ba, ko da alk’awarin daka d’auka na zaka mayar da ita gida ne ka cika, sauran saika musu bayani yanda zasu fahimta.”

Jingina bayanshi yayi a kujera yace “Da ace zata lamunce min wallahi dana had’a na auri mata biyu a lokaci d’aya, sai dai nasan ba lallai ta amince ba.”

Ammar ne ya bud’o k’ofa ya fito hakan yasa Amar k’arasa fitowa shima, abun mamaki kayan baccin jikinsu iri d’aya ne, dan dama sau tari sukan samu wannan kamanceceniyar, kallon juna sukayi wanda yasa Ammar yin tsaki yace “Je ka cire kayan nan.”

Amar da baya yanayin farin ciki yace “Saboda me? Idan ka damu kai ka cire naka mana.”

Wani kallon zakuwa ga sani ya mishi yace “Oho, haka kace?”

Kama rigarshi yayi ta k’asa yayi sama da uta ya zage ya rik’e a hannu, wandon ma dama k’ugunshi roba ce, sab’ule shi yayi ya bar gajeran daya tsaya mishi a cinyoyi, jefawa Amar kayan yayi wanda ke murmushi yana ayyana rashin kunyar da Amna zata gani baiwar Allah, jin kayan a fuskarshi yasa ya yamutse fuska yace “Meye haka kuma?”

Saida Ammar ya zagayo ya zauna d’an nesa da Junaid da suka k’ura mishi ido yace “Ka had’a ka sanya duka, gigin tsohuwar can ya farka yasa ta mana mata a daren nan, kana so kayan bacci ma sai mun saka kala d’aya salon wata rana matarka ta k’wamuso ni a tunaninta kai ne.”

Jibril ne yayi dariya yace “To idan ta kama ka d’in ba sai kace mata ba kai bane.”

Kallonshi yayi da nufin magana amma ganin kallon da Junaid ke mishi yasa ya had’e fuska yace “Malam ko na mik’e na cire har wannan ma ta yanda za ka ga komai da kyau?”

Da sauri Junaid yace “Kai wa Allah ka rufa mana asiri, ina mu ina ganin wannan al’amari, in a matse kake da kayi tsirara ka jira ‘yar k’anwarmu ta zo, wannan ba laifi ba.”

Dogon tsaki yayi ya mayar da hankalinshi kan waya, Amar ne dake shirin fita ya cillo mishi kayanshi yace “Dan Allah ka saka kayanka, kasan fa har yara shigowa suke haka ma matan suna iya zuwa yin wani abun.”

Kallon Amar d’in yayi yace “To meye a ciki? Duk yaron daya ganni haka ai nima nayi zama kamarshi, kuma shima zai dawo kamar ni d’in, mata kuma da kake magana a kai duk abinda zasu gani suji kunya bai wuce wannan abun ba wanda kuma basa rayuwar jin dad’i sai dashi.”

Yanda ya k’arashe maganar yana nuna k’asan gajeran wandonshi da kuma had’e fuskar da yayi kai kace bashi ya fad’a ba yasa Amar cewa “Allah ya shirya ka.”

Ba tare daya kalleshi ba yace “Tare da ebolar gidanku ba.”

Jibril da tuni ya fahimta ne ya tuntsire da dariya sai Junaid da yace “Wace kuma ebola?”

Jibril ne cikin dariya yace “Wa fa inba Hajia ba, nasan dai ita yake nufi.”

Amar ne ya d’an b’ata rai yace “Wallahi Ammar kaji tsoron Allah, ka sani fa kakar ka ce, ya zaka rainata haka?”

Wani kallo ya masa galala yace “Allah ko? To zo ka ci uwani shalelen Hajia.”

K’wafa yayi inda Amar ya juya zai fita, muryar Ammar yaji yace “Bani kayana a hannu na.”

Juyowa yayi ya kalleshi yace “Kai daka cillo min a hannu na ka damk’a min? Kusa da kai fa suke ka d’auka kawai.”

Sake tamke fuska yayi cikin amon muryar da sam babu wasa a ciki yace “Na ce ka bani a hannu na ko.”

Tabbas Amar yasan inhar bai bashi ba sai sunyi fad’a, shi kuma yana so ya ga ya cika alk’awarin daya d’aukarwa Ummy na zai dinga hak’uri da d’an uwanshi dan wani lokacin al’amarinshi kamar mai aljanu yake, dawowa yayi ya d’auki kayan ya mik’a mishi kafin ya juya zai fita, kallon bayanshi yayi yace “Idan kaje ka sa mana matar nan ta rubuto maka kalar rayuwar da take so muyi da matan bayan an d’aura auren, dan mu hardace a kanmu ya zauna mana sosai.”

Girgiza kai kawai Amar yayi ya fice daga d’akin, d’aukar wandonshi yayi ya saka ya gyara zamanshi kamar zaiyi kwance a kujerar yana danna wayarshi yana shafar shafaffen cikinshi mai shegen fad’i, inda k’irjinshi kuma yace ja bani wuri saboda bud’ewar da yayi, jin su Junaid sunyi shiru yasa ya d’an saci kallonsu yace “Ka fad’a min indai kana sonta har yanzu ni kuma zan karb’omaka aurenta wajen iyayenta?”

Kallonshi sukayi sai Junaid da yace “Ina sonta har yanzu, amma tayaya zakayi haka? Gaskiya bana son wata matsalar Ammar, kuma naga kai kan ka baka tsira ba wajen Hajia.”

Murmushin gefen labb’a yayiba tare daya kallesu ba yace “Ku zuba ido kuga ranar da zan fito da wacce nake so, wallahi sai dai ta ganta da ciki kawai ba tare da tasan yaushe haka ta faru ba ma, shirun da kuka ga nayi saboda bana da abin fad’a ne kamar yanda na fad’a ma ita kanta tsohuwar, Amna kuma banda wani dalili na nuna mata tsana ko k’iyayya, dama wannan kankanar ce.”

Shiru sukayi dan sun san baida abin fad’a kamar yanda yace, da akwai kuwa daya fad’a ko da abinda zai fad’a zai jawo kwanciyar wani a gadon asibiti.

Amar na fita b’angaren iyayen ya nufa dan amsa kiran da Hajia ta masa, amma yana daf da shiga saiya samu Hamna har yanzu tana zaune tana kuka, tsayawa yayi ya sunkuya kusanta yana kallonta yace “Hamna.”

D’agowa tayi ta sauke matsakaitan idontaa kanshi, cikin tausasawa yace “Ke ma kina kukan zab’in da Hajia ta miki ne?”

Saida ta share hawaye da hannunta cikin muryar da tasha kuka tace “A’a yah Amar, yah Junaid d’an uwana ne, ba zan k’i shi, sai dai Hajia ta ruguza min burina na zama gogagiyyar mai tsara kaya (fashion designer) da kuma zama mai kwalliya, sanin kanka ne mu mata Hajia bata yarje mana fita daga garin nan ba da sunan karatu, toya kenan idan nace zan tafi da auren yah Junaid a kai na? Ba zata amince ba, kuma gashi mun riga da mun gama magana da wani compagnie dake *Abuja* zan je a hutun nan da za ayi dan fara d’aukar darasi na kwalliya, shiyasa kawai nake kuka.”

Shiru yayi yana kallon yatsun k’afar ta masu tsayi da tudu wanda na kusa da babban yatsan yafi kowane tsayi, ya d’an jima a haka kafin ya mik’e yace “Kiyi hak’uri kinji, zan shiga wajen Hajia yanzu na mata magana, insha Allah burinki ba zai ruguje ba.”

D’ago kai tayi ta kalleshi tace “Nagode yahAmar, dan Allah ka min wannan taimakon, idan ba haka ba babu wani abinda nake so sai dai na zama matar gida nima.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231 232 233 234 235 236 237 238 239 240 241 242 243 244 245Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected