BADAK'ALA COMPLETE HAUSA NOVEL

BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL

Da sauri ta girgiza kai sai rufe baki take da hijabi, cikin jin haushi D’iyar baba ta taso ta shak’o hijabin Mari, ita kam ana jawota saita fad’i k’asa ta fashe da kuka tana fad’in “Wallahi Ayya banyi ba, ba laifina bane, ki tsaya na fad’a miki abinda ya faru, shi ne fa ranar kawwww…”

Marin da D’iyar baba ta watsa mata yasa ta dafe kunci ta kwamtsa k’ara, kafin ta sake cewa wani abu D’iyar baba ta d’auki kujerar data mik’e a kai ‘yar tsugunno ta maka mata a kai, wannan azababbiyar k’arar da tayi tasa kakarta dake shigowa saurin d’aga k’afa ta ida shigowa tana sallallami da tambayar kai lafiya? Ganin wacce ake jibga yasa ta zubar da ledar hannunta ta k’arasa ta rik’e ta cikin harshensu na barebari tana fad’in “Ke dube min yarinya, me tayi miki? Kamar kin samu jaka.”

D’agowa D’iyar baba tayi ta nuna Mari cikin son d’aukewar numfashi tana fad’in “A..a…a..ta cu..ceni, cikin…sh..eg..e…”

Zubewa tayi wajen sumammiya, ai fa sai wani tashin hankalin ya samu kuma, take bakinta ya karkace saboda hawan jinin da take fama dashi, amma duk da haka nuna Mari take tana fad’in “Allah ya isa…Allah ya miki abinda kika min…bani ba ke Mari har abada.” Duk da maganarta ba’a jin sosai amma Mari ta fahimci me take fad’a, ai kawai sai kakarta ta kifa mata wani marin ta fara masifa ita ma wai zata kashe mata ‘ya har tana fad’in “Wallahi idan ‘yata ta mutu dalilinki kema sai kin mutu, da ubanki *Muhammadu* yana raye kikayi wannan abun kunyar da shima ya tsine miki albarka”.

_Masu karatu karfa ku manta babu kirkira a ciki, duk abinda ya faru ne da wasu mutanen nake rubutawa bayan an bani labarin._

Wannan yammaci Mari bata kwana gidansu ba, domin kuwa D’iyar baba tace ita ba yarta bace , kakarta kuma da zasu tafi asibiti saida ta watsowa Mari kayanta sannan ta rufe gidan, a daren nan duk inda Mari take tunanin samun taimako na yan uwa saida taje, amma da sunga yanayinta suka tambayeta lafiya ta k’i fad’a sai wasu suce ta koma gida zasu zo su ji meya faru sai a sasanta, har gidan *malam Rabi’u* taje a tunanin kamar kaka yake gareta saboda da shi da kakanta wanda ya haifi mahaifinsu uwa d’aya uba d’aya suke, sa’a da ta ci shine baya gari kasancewarshi malami ne na tsibbu, shiyasa ta baro gidan da tunanin da yana nan daya karb’e ta tunda malami ne shi.

A tak’aice dai Mari a gindin wata bishiya ta zauna ta rakub’e, kuka take da tunani barkatai na yanda lokaci d’aya komai ya canza mata, mahaifiyarta ta kasa tsayawa ta saurareta, yanzu ya zatayi kenan? Meye abunyi? Ina zata je? Wannan tambayoyin ta dinga jerawa kanya kafin daga bisani zuciyarta ta fad’a mata ta je gidan k’anwar mahaifinta *Khadi*, ta san matar kuma tana nuna mata soyayya saboda Maryama sunan mahaifiyarsu ne aka saka mata, ko rasuwar mahaifinta saida ta so ta tafi da ita amma dai ta jinkirta har wani lokacin, matsalar d’aya ita ce ba garin nan take ba, tana Maradi ne da aure, amma a yanda zuciyar Mari ke tafasa dole ta shirya ta kuma k’udira gari ya waye ta tafi can duk da bata da kud’in mota, a haka kuwa aka fara kiran sallah asuba, tashi tayi daga wurin ta samu wani masallaci tayi alwala da butar nan, gefe ta koma tayi sallah kafin ta d’auki hanyar zuwa gidan mota.

A k’ofar shiga gidan ta fara rarraba ido tunda ita dai ba kud’in mota gareta, haka ta shiga ciki tana ta zagaye ta rasa abunyi, tana ji kamar ta rok’i wani amma tana jin tsoron k’ara neman taimako, tana haka wani matashi da gani kasan d’an makaranta ne dake shirin tafiya hutu wani garin ya mata magana, a tak’aice dai shi ya taimaka mata ya biya mata kud’in motar bayan ta fad’a mishi bata da kowa anan tana so taje gida ne, tare suka zauna kujera d’aya matashin nan duk inda aka tsaya saiya siye abu ya bata, duk da tana tsoron sakewa da shi har saida ta d’an saki jiki, kallonshi tayi tace “Dan Allah me sunanka? Sai tafiya muke har yanzu baka fad’a min ba.”

Kallonta yayi yana murmushi yace “Ke ma ai baki fad’a min ba, kawai kince min kinyi b’atan kai ne shiyasa ni kuma zan taimaka miki.”

Tayi tace “Sunana *Maryama*, amma wasu na kirana da Mari.”

Murmushi ya mata shima yace “Ni kuma *Issa*.” Da haka suka d’an dinga hira kafin Allah ya kaisu lafiya, suna sauka ya nemi lambar wayarta tace bata da, ya nemi kwatancen gidan tace bata san ya zatayi ta kwatanta mishi ita ma dan ta jima rabonta da garin, ya yarda da hakan dan ko harshenta bai gama fad’awa a hausar ba, taxi suka shigo tare har aka ajeta k’ofar gidan tanti Khadi wacce labarin abinda ya faru ya riga Mari isowa wajenta, hakan kuma ya faru ne lokacin da Mari taje gidan wata yar uwarsu, bayan tafiyarta hankalinta bai kwanta ba saita kira kakar Mari, cikin hushi ta fad’a mata wai Mari cikin shege ta musu dan tozarci, yanda abun ya daketa ne yasa ta kasa hak’ura ta kira Khadi tana tambayarta wai hakane? Ita kuma sai lokacin taji meke faruwa, ita ma dai kusan sumar tayi, amma daga baya haka ta dinga fad’a tana masifa wai Mari ta zubar musu da mutumci, su a zuri’ar su kaf babu wanda ya tab’a cikin shege sai ita, har ta wayi gari tana wannan kwakwazon, abun bai bar tunaninta ba kuma sai ga sallamar mari ta diro garin daf da magrib, tunda ta k’ura mata ido bata d’auke ba har mari ta tsargu, yan uwa in dai kaiku in baro Khadi ma bata karb’i Mari ba, cewa tayi sam ba da ita ba kawai ta koma wajen uwarta data d’aure mata gindi (duk da ta ji uwar fa suma tayi), duk magiyar duniya ba wacce bata mata ba amma ta rufe ido, har saida tace mata “Ki gode Allah da kawu *Rabi’u* baya gari abin nan ya faru, ba dan haka ba da har kasheki zai iya yi, dan shi baya lamuntar wannan iskancin.” Sai lokacin Mari ta fahimci dalilin da yasa bata samu malam Rabi’u ba, kenan da yana nan da abun ya munana?haka ta fito da kunyar ganin bak’on data tsayar da niyyar ta shiga ta kawo mishi ruwa tantin ta kuma ta mishi godiya na alkairin daya mata, haka suka jera ita da shi basu san ina zasu je ba, shi dai ba zai iya tafiya da ita gidan da ya zo hutu ba, to meye abunyi, har aka gama sallah magrib suna tafiya kafin Mari shed’an ya zugata tace saurayin ya bata lambarshi zata kirashi idan taje wani wurin, rubuta mata yayi yana kallo harta b’ace ma ganinshi, doguwar tafiya tayi har ta zo wucewa ta ranpoint d’in hôpital, anan ne suka fara had’uwa da Iklima, kallon farko da Iklima ta mata sai ta ji tausayinta saboda tana tafe tana kuka da yake nuna k’unci a tare da ita, tsayar da ita tayi suka gaisa ta tambayeta ko lafiya? Da farko kasa fad’a mata komai tayi, amma sai Iklima ta mata karamci ta hanyar zuwa da ita gidan da suke zaune ita da sauran yan mata masu yawa, sauran abinci ta bata ta ci sannan tace ta saki jikinta, cikin fargaba ta kwashe komai ta fad’a mata abinda ya faru da ita, tab’e baki Iklima tayi tace …

“Ai matsalar iyayenmu kenan, zaki shekara dubu kina kare mutumcinki, amma rana d’aya idan tsautsayi ya fad’a miki ki kayi ciki to sun manta, nima abinda ya faru dani kenan, sai dai ni da amincewata na yarda da saurayin saboda ina son shi, shigar rabo yasa na samu ciki, amma haka suka fara min horon yunwa ga tsanani ko kulani basa yi a gidan, ça tsangwama da hanta ta yayyu na, shiyasa ni kuma da naga yunwa na neman halakani na bar musu gidan, yanzu nan nake rayuwata duk da mahaifiyata na so na koma gidan yanzu, kuma cikin dana fito da shi ina haihuwarshi na kaiwa ubanshi, ni kuma na ci gaba da neman kud’i na.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231 232 233 234 235 236 237 238 239 240 241 242 243 244 245Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected