BADAK'ALA COMPLETE HAUSA NOVEL

BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL

Malam Yacub da suley ne suka shiga nemanta amma shiru, bai ma yarda Saratu tasan bata nan ba har saida aka kwashe kwana biyar, tunda ya sanar da ita ta tashi hankalinta, a lokacin ne fa duk wasu tsofaffin ciwuna da take fama da su wanda basu bayyana sai suka fara bayyana, sosai take jin jiki Suley kuma na fama da k’ok’ari wajen samar mata magani na gargajiya, *ba’a rabu da Bukar ba an haifi Abu*, Alhaji Hassan shima saiya samu had’ari a hanyarshi ta zuwa kasuwa, gawarshi kawai aka dawo da ita gidan, tashin hankalin da suka gani a ranar bai misaltuwa, duk k’ok’arin Suley na ganin mahaifiyarshi bata san halin da ake ciki ba abun ya ci tura, dan koke-koken Ramma da yayanta Barira da Rahmatu shiyasa tasan meke faruwa, nan ita ma jiki ya yamutse aka gaza gane kanta.

Tsawon kwana sha hud’u d’in da akayi na rasuwar Alhaji Hassan Saratu bata san me ake yi ba, saida mak’wabtan su suka taimaka aka kaita asibiti, jinya take sosai inda ake kula da ita a asibiti, wasa wasa sai gashi ta kwashe sati biyu a asibitin, bayan an sallamota kuma sun dawo gida da kwana shida akayi wa Hassan sadakar arba’in.

A ranar kuma a gaban mutane Ramma ta nemi yan uwan Hassan da maganar a raba gado tunda anyi arba’in, duk da abun bai ma kowa dad’i ba amma dayake ta riga data dasa musu shakkunta a zuciyarsu yasa suka amince da maganar, bayan kwana biyu da faruwar hakan Ramma ta yiwa Suley kurciya ya bar gida gaba d’aya, wayar gari akayi babu shi babu dalilinshi, abun bai tashi hankalin saratu ba saida aka kwashe kwana uku, a haka kuma Ramma ta tilasta aka raba gado duk da a lokacin akwai k’arancin ilimin addini, an raba gado yayanta sun samu rabonsu inda saratu aka bata abinda ko kashi d’aya na mace d’aya bai kai ba, wannan bak’in cikin da k’uncin yasa Saratu ita ma cewa ga garinku nan, haka ita ma akayi na ta makokin inda abinda aka basu ya zama k’ark’ashin kulawar Hassana.

*Duk* abin nan dake faruwa Husseina na cikin garin, inda gaba d’aya ta lalace ta zama karuwa mai lasisi, duk da ba kowane lokaci take zaune garin maradi ba, dan wasu lokuta mawak’a suna d’aukarsu su tafi dasu wani gari dake nigeria da ake kira *hirji*, cikin jikinta kuma magajiya uwar karuwai ta so a zubar dashi amma tace a’a, da haka ta dinga rainon cikin kusan a wannan lokacin ita ce karuwar da wasu suka fi nema suna bayar da kud’i masu yawa dan su kwanta da ita saboda tana da ciki, saida cikinta ya tsufa ta aje harkar na d’an lokaci har saida ta haihu, namiji ta haifa wanda mata masu zaman kansu sukayi babban bidiri, mawak’a suka baje nasu kolin daga ciki harda irinsu margayi *Sa’adou bori*, ranar suna an kwana ana cashewa daga k’arshe dai yaro ya ci sunan *Labaran* a cewar Husseina shi yafi kowa bawa gidan karuwan tallafi, dan haka ya cancanci a mishi takwara, (duk wannan fa abun ya faru),duk da a lokacin ta samu labarin mutuwar mahaifinta amma sai tace “Allah raka taki gona.”

Rasuwar mahaifiyarta kad’ai ta girgiza ta data samu labari, amma duk da haka bata je gidan ba saboda tace bata son sake ganin unguwar ma, haka ma wajen Suley tafiya kawai yake yi, yunwa na ci k’ishin ruwa na ci, domin duk abinda yake samu yasa a cikinshi ba isarshi yake ba, hasalima ba komai ne yake samu mai kyau ya ci ba, haka yake tafiya ba um ba um um, ya galabaita sosai ya jikkata ta yanda ya fita hayyacinshi, haka Suley ya d’auki tsawon lokaci yana tafiya ba tare da yasan inda yake saka k’afar sa ba har tsawon *wata biyu*, a cikin tafiyarshi ne Allah ya had’a shi da wani mutum mai kirki d’an kasuwa mai sunan *Alghabit*, mutumin *Agadez* ne kuma hamshak’in mai kud’i, yana kan rak’uminshi ya ga Suley na tafiya kamar gunki, kallo d’aya ya masa ya tabbatar yana tare da k’ishin ruwa da kuma yunwa dama gajiya, dan kuwa har k’afafun shi sun kumbura kamar na mai tsohon ciki saboda tafiya, tsayar da rak’umin yayi dan a wannan lokacin shine abun hawan kuma mai daraja garesu, duk da akwai mota a lokacin amma dai bata damesu ba kamar rak’umi ko kuma moto, saida rak’umin ya durk’usa har k’asa ya sauka ya tunkari Suley, tare gabanshi yayi yana mishi magana da gurb’atacciyar hausarshi daya d’an kama wajen yawon kasuwancinshi a bakin hausawan, ganin kallonshi kawai yake ya tabbatar ba lafiya yake ba, hannunshi ya kamo ya zo kusa da rak’uminshi ya d’auki aglami (buzun sallah) da gorar ruwa da kuma wani d’aurin abu a cikin fata, gefe suka koma k’ark’ashin wata bishiya ya shinfid’a aglamin ya zaunar da Suley, ruwan ya fara bashi ai ko da sauri ya fizga daga hannunshi ya kifa baki bai sauke ba saida ya shanye, da mamaki da kuma tausayinshi ya zauna kusa da shi ya bud’e wannan d’aurin ashe akushi ne a ciki da abinci, nan ma abincin nan ya ci sosai kafin ya sake bulbulo mishi ruwa a yar babbar jarkar da ke d’aure da rak’umin. Tare ya tafi da shi a d’ora shi akan rak’umin, idan dare yayi su yada zango da safe su ci gaba, kwana goma sha bakwai suka d’auka kafin suka isa garin agadez.

*A garguje*

Haka ya sauke Suley gidanshi da taimakon iyalinshi, inda ya samu limamin unguwarsu ya zo da shi har gidan ya nuna mishi Suley, daga lokacin aka d’ora shi akan magani da rok’on Allah, Allah maji rok’on bayinsa sai gashi cikin *wata biyu* Suley ya samu lafiya ya dawo kamar yanda yake, Alghabit dama ‘ya’yanshi mata ne suka fi yawa, dan haka saiya rik’e Suley kamar d’an daya haifa, tunda jiki yayi kyau sai Suley ya d’aura d’amarar neman kud’i dan yaje ga ahlinshi ya tallafesu, hakan yasa duk safe ta Allah ya kan shirya ya fita kasuwa, lokuta da dama dakon kayan mutane yake ana biyanshi kud’i kad’an, wani lokacin kuma idan kayan manyan yan kasuwa sun zo sai su sauke kayan a biyasu, da irin wannan k’ok’arin na shi ya fara tara kud’in komawa gida, duk lokacin da zai fita idan Alghabit ya tambayeshi sai yace zaije zaga gari ne kawai, a haka wata rana Alghabit ya sake komawa fatauci, a lokacin ne Suley ya fahimci wani ha’inci da ake mishi idan baya nan kuma a cikin gidanshi, babbar ‘yarsa *Zeeya’atu* wacce gaba d’aya shekarunta basu haura sha shida ba tana ganin ya bar garin ita ma zata fara na ta yawon dan jin dad’in rayuwarta, kuma mahaifiyarta *Zaha* iya ke d’aure mata gindi tana bata umarni, babban tashin hankalin shine wani lokaci har ta kan iya kwana ba gida ba, nan yayi niyyar sanar da mai gidan idan ya dawo, domin kuwa babu mai zarginta, dan idan ta tashi fitar ta kanyi shiga ta kammala sannan tayi nesa da gida.

Bayan Alghabit ya dawo tuni sauran yaran dake tayashi kasuwanci suka rigashi isowa tare da sauran rak’uman dake d’auke da kaya, dan haka kai tsaye ya wuce kasuwar garin dan a sauke wannan kayan a rabawa k’ananan yan kasuwa, a nan fa yayi kicib’us da Suley a cikin masu sauke kayan, wannan abu shi ya birgeshi a tare da yaron ya kuma ji ya yarda dashi ba ko kokonto, hakanne yasa ko da suka iso gida bai bawa Suley damar fad’in abinda yayi niyyar fad’a ba yace ya d’ora shi akan harkokinshi, yanzu ya zama kamar magajinshi zai dinga tafiyar da komai, wannan karamcin da wa suley ya sa bai iya fad’an komai ba saboda kunya, ba b’ata lokaci Suley ya durmiya cikin kasuwanci ya fara sarrafa dukiyar yanda ya kamata, sai Allah yayi wa Suley baiwa ta nasibi ta yanda duk abinda ya tab’a yakan hauhawa, cikin wata *uku* sai gashi shi kanshi alghabit na mamakin yanda dukiyar take bunk’asa, sai kawai ya sake yarda da shi ta yanda wata ranar *alhamis* ya shirya yace wa mutanen gidan zaiyi wata yar gajeriyar tafiya ya dawo, fatan alkairi suka mishi amma babu wanda tunaninshi ya bashi wani abu.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231 232 233 234 235 236 237 238 239 240 241 242 243 244 245Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected