BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL
D’aki ne dake k’asa kuma babu tazara tsakaninshi dana Sameera, babu abinda babu a ciki dan Sameera ce ke kula da shi saboda saukar bak’i idan sun zo daga basraba, duk da wani lokaci idan ta b’atawa Abbas rai yana cewa kishiya zai mata kuma ya sakata a d’akin, amma sai tace ai babu mai k’arar kwanan da zata yarda ta shigo mata gida, ko shi saita k’ona shi da ranshi idan yayi wasa, to fa anan Ma’arufa ta sauka ta samu tayi wanka ta canza kaya, kafin ta kwanta Ammie ta turo Raudat da magani wai ta shafa a k’afar ta ko taji dama dama, har Raudat zata fita Ma’arufa tace “Ya sunanki?”
Juyowa tayi da fara’a tace “Raudat.”
Murmushi ta mata kafin tace “Zo zauna muyi hira lil sis.”
Dawowa tayi ta zauna tana kallonta ita kuma tace “Ina Ummynku take ne? Ko kuma mahaifiyarku ta rasu kamar ni? Dan na fahimci wacce kuke kira da Ammie kamar granny d’in ku ce ko?”
Bud’ar bakin Raudat sai cewa tayi “…
*Sub’ul da baka.*
12/06/2020 à 11:49 – Ummulkhairi: ❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️
*SANIN MASOYI*
_(sai Allah)_
*BAYA DA K’URA*
❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️
*NA*
_SAMIRA HAROUNA_
*Litattafan marubuciyar*
*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D’AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD’I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K’ADDARARMU_
*8* _K’ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k’ura)…_
*14* _BADAK’ALA…_
*SADAUKARWA GA*
_*MASOYA NA*_
_Bismillahir rahamanir rahim_
*TAURARIN NIGER*
“`(Tsintsiya mad’aurinki d’aya)“`
_9_
Tunda Allah ya halliceta take zaune shekara goma sha bakwai a matsayin matarsa bata tab’a sanin cewa baya k’aunar ta ba irin yau, to mana baya k’aunar ta, dan rashin imanin daya darza mata ko dabba kayiwa haka kasan sai dai a d’auki gawarta, tabbas tasan akwai fyad’e a duniya, domin kuwa ita ta hanyar fyad’en ma ya rabata da nata budurcin, amma sanin azabar dake tattare da haka bata sani ba kam sai yau, babu inda bata jin yana mata zafi a jikinta, kama daga labb’anta wanda har cizasu yake tsabar mugunta zuwa kan k’irjin ta daya dinga lindasu kamar yana wankin kayan da suka shekara ba wanki, k’asanta kam ko magana ma ba ayi, duk da uwa ce ita ta haihu amma gyara da kular da take bawa wurin yasa yake zam-zam, to a yau dai kam ta tabbatar ya gama wangaleta ta yanda ko d’inketa akayi ba zata sake birgeshi ba bare ya moreta, cikin wannan hali da take taji ya kasheta da wani tattausan mari wanda ita a wurinta wata azabar ce ya biyota da ita, mik’ewa yayi ya fad’a ban d’akin ta ya tsarkake kanshi, yana fitowa ma jakar daya jefar ya d’auka ya d’ora akan gado ya bud’e ya d’auki kayanshi ya saka, sai lokacin ya kunna hasken d’akin ya kalleta.
Sam baiyi dariya ba saboda baya so ta samu damar sauke mishi tijara, amma yasan yau kam mai rabasu sai Allah, ko bata zage shi ba saita dake shi, har zuciyarshi yasan tana buk’atar taimako, amma danya d’an fara bata tsoro idan yace tayi sau d’aya ba sai ya maimaita ba yasa ya k’are mata kallo ya fita a d’akin, tana ganin haka ta tattara k’arfinta ta mik’e zaune da k’yar, kallon kanta tayi ta madubin dake gefenta tace “Ni zai yi wa haka? Lallai ma mutumin nan.”
Misalin *09:00* na dare suna zaune dukansu kan dinning table, sanye take da doguwar rigar material mai kyau da tsada bleue light da d’an kwalinta, babu komai a fuskarta data shafa idan ka cire mai da lips a bakinta, tana hango Ammie zaune ta sake sangarta tafiyarta cikin shagwab’a ta k’arasa ta rumgumeta ta baya ta fashe da kukan sangarta, da sauri Ammie ta fara tambayarta “Auta ta lafiya? Waya tab’a min ke?”
Abbas da tunda ta fito yake kallonta, maganar gaskiya kallo d’aya ya mata ya ga har tayi wata ramar k’arfi da yaji, hatta tafiyarta ma ta kasa daidaituwa da kyau duk jikinta ya saki, wani haushi ne ya tokare masa mak’oshi yaji kamar ya mareta, shin bata lura da bak’uwar dake wurin bane? Idan ma bata ganta ba ai tasan Abdul na wurin yaron dake shirin zama sirikinta, kasa amsawa tayi yayin da yaran duk suka k’ura mata ido har da Ma’arufa dake mamakin karuwanci Sameera, Ammie ce ta gyara zamanta kan kujerar da nufin zaunar da Sameera kan k’afafun ta, amma suna had’a ido da Abba taga kallon da yake ma Sameera tasan duk yanda za ayi zai iya d’aukar wuk’a yace zai gagara mata, dan haka ta mik’e tsaye tace “Auta zo muje d’aki na ki fad’a min meya sameki, naga duk kin canza kamar ba ke ba.”
Hannunta Ammie ta kama zasu fice sai idonta ya sauka kan bak’uwar su, yanzun ma kamar ganin ta da ita na farko sai taji gabanta ya fad’i tare da jin haushin yarinyar, wani tunani ne ya d’arsu a zuciyarta take a wurin, shin idan fa k’addara tasa yarinyar ta aurar mata miji? Kanta ta bawa amsa ta hanyar fad’in “Ai kuwa babu abinda zai hanaki k’ona gidan nan kamar yanda kike fad’a masa.”
Da haka suka tafi part d’in su Ammie suka zauna falo, cikin rarrashi Ammie tace “Auta fad’a min meya miki?”
Turo baki tayi gaba ta kwantar da kanta saman k’afafun Ammie tayi shiru, cire mata d’an kwalin tayi ta fara shafar kanta data ji shi a jik’e, take ta fahimci komai, dama ba kunya ce tsakaninsu ba dan haka Ammie tace “Auta halan hukuntaki yayi saboda baki taho tare da mu ba?”
D’agowa tayi ido taf da hawaye kamar zata fashe da kuka tace “Ammie hukuncin ma mai tsanani, wallahi bai tab’a min irin shi ba sai yau, bansan a ina ya koyi wannan muguntar ba, ni gaskiya Ammie daga yanzu d’akin ki zan kwana har saiya bani hak’uri.”
Kwantar da kanta tayi tana daddab’ata b’angare d’aya tana toshe baki tana dariya, labari ta fara bawa Ammie yanda sukayi da matar waziri, dariya kawai Ammie take tana godewa Allah da abun ya tsaya iya mari kawai, suna haka sai ga Abbas ya shigo tak’im tak’im kamar wanda aka bawa sarauta, Ammie na ganinshi ta had’e rai tace “Kai kuma malam lafiya? Meya kawoka wajenta?”
Saida ya harari Sameera yace ” Ni ba wurinta na zo ba.”
Zaune yayi kan kujerar dake fuskantarsu ya kalli Sameera dake wurga masa harara yace “Ke tashi ki bamu wuri zamuyi magana da uwa ta.”
Sake mak’alk’ale Ammie tayi tace “Ba zan je ko ina ba, ka fad’i duk abinda zaka fad’a ina gaban uwata.”
Murtuke fuska ya sake yi, matsalarshi da ita daman kai tsaye zai bata umarni tace ita ba haka ba, kafeta yayi da ido kawai hakan yasa Ammie kallonta tace “Yarinyata, shiga d’aki na ki kwanta abinki gani nan zuwa yanzu, idan kin shiga ki duba a drower akwai kayan dad’i ki d’auka kinji.”
Mik’ewa tayi a kasalance ta wuce ko d’an kwalin nata bata d’auka ba, da kallo ya bita kafin ya kalli Ammie wacce tace “To ina jinka, lafiya da zaka wani katsewa yata jin dad’in ta?”
Mik’ewa yayi yace “Ba komai, dama zan d’an fita.”
Kafin tayi magana taga ya sa kai ya nufi d’akin nata kuma, girgiza kai tayi tace “Kaji da munafurcinka, da nace wurinta ka zo ai cewa kayi a’a.”
Sameera na sunkuye zata d’auki chocolat taji saukar mari a mazaunanta, da sauri ta d’ago ta dafe kayanta tana fad’in “Washhhh.”
Tana ganin yanayin shi sai kuma tayi shiru, cikin muryar shagwab’a tace “Dan Allah Abban Ameer ka daina wahalar dani haka, ya kamata fa ace yanzu na wuce ajin shan wahalarka, wacce na sha ma a baya lokacin da nake maka bauta ta isa haka.”