BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL
Haka akayi rabon gadon Alhaji inda kowa yaja nashi babban rabo, kowa ya k’ara yawan jari ya kud’ence abinshi, shagali kawai ake iyaye da yaransu, kowa ya k’ara d’ora yaranshi kan manyan harkoki, hakan ya tilastawa Ammar dawowa wata ukun bai cika ba aka duk’ufa harkokin duniya, wani lokacin kamar kanshi zaiyi bindiga tsabar abunuwa, yaje asibiti yaje station shaguna da sauransu, a hakan ma wai dan Amar ma da inda yake kulawa haka ma Kamal suna saka shi kowane b’angare tunda ya fara mallakar hankalinshi shi ma.
Tunda abun nan ya faru ko sannu shi da ita bata sake had’asu ba, ya watsar da al’amuranta ya sake rumgumar matarsa hannu bibbiyu, sau da dama sukan had’u ko wajen shiga mota ko farfajiya ko k’ofar gida ko kuma falon Hajia, amma kallonta ma baya yi bare yaga shigar jikinta abun ya dame shi, hasalima ko ganinta yayi canza fuska yake yi yayi abinda ya kawoshi yayi gaba.
*Wannan* shi ake kira da kisan mummuk’e, gashi dai ya fita harkarta kamar yanda take fad’a a kullum, ya daina ko kallon fuskarta, ko d’akin matarshi zai shiga ya ji tana ciki saida ya koma har sai ta fita, tun tana jin kamar dad’i take ji har ta fahimci ba dad’i take ji ba a zuciyarta, kawai tana nuna tana jin dad’in ne a zahiri, ita ma bata kula shi kamar yanda yake yi, sai dai bata jin dad’i ko kad’an. Amma kuma hakan baisa ta canza abinda duk shine ya jawo matsalar ba, sabon babin rashin mutumci da fitsara ta bud’e, Amie dama ita ma ba aure tayi ba dan haka ta taya b’era b’ari suke sharholiyarsu, yawan biki da bi-gari kullum cikinshi suke, sun shiga sahun manyan matan da ake kiran sunansu, wannan matsatsun kayan dai kullum sune jikinta, wani lokacin ko gyale bata d’orawa haka zata shiga mota.
Kud’i kullum cikin kashesu take wajen siyan anko na k’awaye da d’inki, anko ba wai guda d’aya ba a’a sama da haka, abune daya zama na yayi kowa na so a fad’i bikinshi, hakan yasa kamu bridel party kan amarya damu, duk wannan abubuwan anko ake fiddowa kuma tana siya da kud’i, wasu lokutan d’inkin da akayi iri d’aya akeyi duka yan mata, wani d’inkin ko wata shigar idan kaga sunyita ka rantse ba yayan musulmi bane.
Amar ne ma ya d’an fara k’orafi kan abinda take, shima daga baya ya ja bakinshi yayi shiru, Hajia na gani amma an rasa dalilinta na saka mata ido tana abinda ta ga dama, Ummy ce ke tsaye kanta take mata fad’a da magana, amma magana d’aya ce “Ummy ki yarda dani wallahi ba zan tab’a zubar muku da mutumci ba, ko ban fita biki ba ai zan je wajen sana’ata, dan haka ki kauda idonki daga abinda mutane zasu ce ko suke fad’a.”
Hadiza taga canji sosai a game da yar ta ta, hakan yasa ta tambayi yar uwarta Amna, a lokacin Amna ta ji a cikin gidan cewa Hamna ta ma Ammar rashin kunya shi kuma yace ba zai k’ara mata magana ba, yanda taji ta fad’a ma uwar wanda hakan yasa ranta b’aci fiye da kima, a waya ta kirata ta fad’a mata tana son ganinta, wannan karan ko da ta zo ko wurin zama ba’a bata ba bare ruwa aka balbaleta da masifa, ta inda Hadiza ta fita bata nan take fita ba, ta mata fad’a sosai kamar yawun bakinta zasu k’afe, tana gamawa kuma tace ta tashi ta koma bayan ta bata umarnin ta fito da miji wata d’aya kawai idan ba haka ba kuma zata dawo da ita gabanta ko da hakan zaisa sai tayi shari’a da dangin uban nata, haka ta juyo ta dawo tun a hanya take tunanin abinda mahaifiyarta ta fad’a, cikin jin haushi take tambayar kanta waya fad’a mata abinda ya faru? Wa zata fitar a matsayin miji? Ita fa bata shirya aure yanzu ba ma, idan fa tayi auren ma asiri ya tonu fa?Tsaki tayi ta d’an daki sitiyari saboda tuna abinda mama ta fad’a, a hankali ta shiga jero kalmomin data fad’a mata a k’walwarta.
*”Ashe shiyasa kika zama tsagera, saboda mai fad’a aji a gidan ya tsame hannayensa daga kanki, to ke inba hauka irin naki ba duk gidan nan waye zai tsawatar miki inba Ammar ba? Sa’ada dama ba mazauniya gida bace, sannan tun farko ita da lieutenant sun riga da sun lalata ku da sangarta, colonel a shekara d’aya zaman da yake a gidan lissafaffe ne, Labaran kuma dama tun farko baya shiga sabgar iyalin Hajia saboda baya son ta ci zarafin mahaifiyarshi, dan shi zai iya yin laifi amma har Hajiarshi saita wanke ta tas, to Amar Junaid Jibril dukansu aikin banza ne, babu wanda ya damu dake ko tsirara zaki fita, mahaifinku kuma kinfi kowa sanin baya da lokacinku, to ki fad’a min inba Ammar ba waye zai sa ido akan ki? Ke ba ma ke kad’ai ba kaf yaran gidan shi kad’ai ne mai taka musu birki, dan haka ki same shi ki bashi hak’uri in ba so kike kiga b’acin rai na ba.”*
Shawarar Amie tayi aiki da ita wajen fito da *Habib* a matsayin wanda zata aura, ba wai dan tana son shi bane sai dan shine yafi tsarin da take son mijin aurenta ya kasance, ba’a wani tsaya bata lokaci ba aka shigar da manya maganar kuma suma suka nuna manyantaka, dan danan aka saka rana inda aka kawo kaya, k’ok’arinshi ya birgeta dan yayi bajinta sosai. Matashi ne dake da jini a jika da ji da dala, nan fa, matarshi d’aya da yara biyu, nan aka fara shirye shiryen bikin Hamna su Amie aka fara shiga da fita, sai lokacin take tambayar Hamna me ke tsakaninsu da Ammar? Saboda taga sun had’u shi zai fita su zasu shigo ko kallonsu baiyi ba, data fad’a mata abinda ya faru sai ita kanta taji ta samu damar da zatayi aure, dan dole ta shigar da kanta wajenshi, ta mayar da wasa gaskiya ta zama mallakinshi, fad’ansu da Hamna kuma nasara ce wurinta, dan hakan na nuna Hamna ba zata shiga abinda ya shafeki ba, ma’ana ba zaisan komai a kanta ba, tunda k’awayence ne ake abisa taka dokar mutumtaka, Hamna tasan Amie sarai tasan rikakkiyar karuwar alhazan birni ce, amma duk da haka tana tare da ita, wanda hakan ma ya taka rawa sosai wajen goga mata pantin da ake mata kallon mutuniyar banza ita kanta.
An fito da anko kala har hud’u, sun shirya sun had’u da abokan ango sun fad’a musu abubuwan buk’atarsu, sun d’auki wanda hankali zai d’auka sun aje musu sauran, shirye shirye sunyi nisa sosai, amma har yanzu Hamna bata jin farin cikin da wannan aure, tana yin komai babu kuzari a ciki ko alamar so, idan suna hira da Habib wani lokacin Ammar ya kan shigo gidan, a matsayinsa na musulmi kuma wanda ya ga mutane yana sallama ya kuma bawa Habib hannu su gaisa, amma bai tab’a yarda idonshi da nata sun had’u ba sai dai ya fice, haka zata bishi da kallo har ya b’ace ma ganinta, haka ita dai take sukuku sai lokaci kuma dake k’aratowa.
*Har* bacci ya fara gaba dashi Amna ta tashe shi kan ya manta bai siyo madaran daya yara sabonta ba, kowa zai iya bacci bai sha ba amma banda *Ameera*, saida ya lumshe ido yace “Ke dai kina jin bak’in cikin kiga na kwanta baccin alhalin ke ma baki kwanta ba ko?”
Dariya tayi tace “Ta ya ba zan so ganinka kana hutawa ba? Ai farin ciki na ne.”
K’ok’arin saukowa daga kan gadon yayi yana fad’in “K’arya kike, ai da sai ki tuna min tun kafin na shigo gidan.”
A hankali tace “Wallahi na manta ne gaba d’aya, kuma naga tun kafin ta ida kake kawo wata.”
Cikin sumalin bacci yace “Bansan ya akayi bane na manta wallahi, yanzu kuma zata hana kowa bacci a gidan nan in babu ita.”
Da kallo ta bishi har ya canza kaya zuwa k’anana ya d’auki makulli yana fad’in “Allah yasa a samu a kusa.”