BADAK'ALA COMPLETE HAUSA NOVEL

BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL

Cikin shewa da tapa hannaye tace “Wuuuu! Alhamdulillah Ina da mijin da zan iya nunawa, kuma nagode Allah daya bani mijin da nake jin dad’in dashi, ke fa? Har yanzu gantali kike a titi har kin tsofe a gari babu mai so, sannan kaf yarana na haife su a k’ark’arshin inuwar aure, har nayi zamani na ban aje d’an dak…”

Dan bai da kuzarin da zai tashi ne amma yayi niyyar marin fuskarta, dan haka kawai ya daka mata tsawa da cewa “Umaimah.”

Shiru tayi tana hararan Hamna wacce ita ma ke kallonta tana murmushi, cikin b’acin rai ya gyara zamanshi yana kallonta yace “Umaimah me yasa baki da hankali? Ta tsawarta miki ne saboda kina d’aga murya kan babba kuma d’an uwana da take da tabbacin ba zan ji dad’in abinda kika masa ba, yaushe zakiyi hankali ne wai?”

Wani harare ta sake dalla ma Hamna tana turo baki gaba tana gunguni, ba tare daya daina kallon fuskarta ba yace “Ba tace ki tambaye ni ba? Me yasa baki tambaye ni ba? To bari ni na fad’a miki kiji da babban murya, wannan dukan da d’an uwana aka wa shi wallahi ba zan sake cin abincin gidan nan ba har sai ranar da idona suka ga cikakkiyar lafiyarsa, Umaimah ina farin ciki sosai da godiya ga Allah da dukan nan ya tsaya kaina, yanzu haka na yafewa wanda yasa aka dake nin, amma da d’an uwana ya daka har abada babu yafiya tsakani na da shi, dan haka wuce d’akinki bana son ganinki a wurin nan.”

A hassale ta kalleshi tace “Ni ce ma mai laifi kenan? Ba damuwa.”

Ta fad’a tana wucewa d’akinta, da harara ya bita cike da takaicin hallayarta yana fad’in “Inma da damuwar fa sai me.”

“Hahahahahahahahahahha, wuuuuuuuuuu, wayyo Allah na, Hajia kin gani ko?” Cewar Ammar kenan dake nufa kusan Hajia, nuna mata Hamna yayi yace “Allah Hajia yarinyar nan so na take, kiji fa yanda take fad’a dan an tab’a mata ni, wuuu! Gaskiya zamuyi kyau da aure.”

D’ora kanshi yayi kan kafad’ar Hajia cikin jin kunya yace “Dan Allah Hajia ki daure ki aura mata ni, kinji?”

Me Hamna za tayi ba dariya ba, har ga Allah shirmenshi ko rashin kunyarshi suna bata haushi da takaici, amma na yau saiya bata dariya da yace wai ta daure ta aura mata shi, kallonta yayi ya kalli Hajia yace “Kin gani ko, na fad’a miki ai.”

Junaid ne yace “Yanzu ya maganar d’aukar fansar to? Ka hak’ura kenan?”

Kallonshi Husseina tayi kallon ya kuma zaka tuno masa? Kallonshi yayi yace “Hak’uri fa? Ai wannan maganar ma bata taso ba yaro.”

Hanyar fita yayi Hajia ta fizgo hannun Hamna cikin rad’a tace “Ki wa Allah Hamna naga kamar ke d’in aljanunshi na sonki ki dakatar dashi, karya je ya kashe d’an mutane.”

Kallon Hajia tayi ta had’e fuska tace “Ni kuma Hajia? Rufa min asiri na mutu maza su binne ni, ba wani aljanu wallahi iskanci ne.”

Cikin rad’a tace “Amma dai kinsan zai iya ko?”

Tunawa tayi da abinda ya faru jiya sai kawai tace “Gaskiya kuma.”

Turata Hajia tayi tace “Yi sauri to ce ya hak’ura ya dawo zan aura masa ke.”

Hararan Hajia tayi tace “Karku sa haukansa a kanku mana.”

Da sauri ta fita daga d’akin inda Amar ya kalli Hajia yace “Da zaku ji tawa Hajia sai nace ku aurar dasu, a yanda na fahimta duka suna son junansu.”

Murmushi Hajia tayi tace “Ba zasu yarda cikin sauk’i ba, amma zan musu na babba da yaro, in sun san wata ai basu san wata ba.”

Husseina ma dariya tayi tace “Gaskiya kam, musamman ma Hamna dai tafi taurin kai, amma shi na ga kamar k’uli yake duk inda ya fad’i gaba ne.”

Dariya Junaid yayi yace “Kai shi fa babu ruwansa, anya ma kuwa zai iya soyayya?”

Zeituna da tunda suka gaishe da Amar bata sake cewa komai ba sai yanzu ne tace “Ai kuwa idan ya tashi yi zai baka mamaki, dan soyayya ma sai tafi wahalar dashi fiye da tunaninka.”

Kallonta yayi yana dariya yace “Tanti Ammar kuwa zai bari soyayya ta bashi wahala, ba fa zai iya rarrashi ko lallab’a ba bare kalaman soyayya.”

Amar ma dariya yayi yace “Ai daya fara ma zai ce ke dan ubanki dan kinga ina lallab’a ki.”

Ihun Hamna suka ji yasa suka dakatar da dariyarsu suka fita da sauri sai Amar kad’ai ke zaune yana girgiza kai, ko da suka fito a farfajiyar suka same su yayi k’arfa k’arfa ya shiga har d’akin mai gadi ya d’auko labceciyar wuk’arsa ko kuma takobi, Hamna ce tace mai gadi ya rufe k’ofa shine fa ya d’aga takobin yace bari ya fara ta kan mai gadin, dalilin kuwarta kenan, cikin tashin hankali da son kwantar da tarzomar kowa ya shiga bashi baki, anan Hajia tace “To kai da yanzu muke maganar aurenku kuma kana so ka shiga gidan yari, kasan dai ba zan aura maka jikata bayan ka fito daga gidan nan ba ko?”

Husseina ce tace “Nima ban goyi da baya ba gaskiya, dan wata rana yar tamu zai kashe.”

Cikin nutsuwa Zeituna tace “Yah Ammar, ko ba komai dan Allah kayi tunanin yaranka mana, ko so kake ka mayar dasu marayu gaba da baya? Mahaifiyarsu ma Allah ya jikanta da rahama ba zata so ba hakan ba, ko ka manta ka tab’a fad’a min bata son rigimar da kake yi.”

Mik’awa mai gadi takobin yayi yace “Shikenan kun kashe wannan fitina, amma ku sani ban muku alk’awarin cewa idan na ganshi ba zan murd’e wuyan tsinanne ba.”

Kallon kallo suka shigayi suna ma kansu tambayar wannan ai shine an kashe maciji ba’a sare kansa ba, can kuma sai suka ji yace “Shiit, to ai kuma banga fuskarsa ba.”

Murmushi kowa ya saki na jin dad’i sai kuma ya kalli Hamna wacce tuni ta shiga rarraba ido dan tasan ba shakka zai koma kanta yace “Munafuka ke ai kin san shi, dan haka tare zamu fara yawo yanzu har sai kin nuna min shi.”

Hararanshi tayi tace “Saboda banda aikin yi? Ko kuma saboda kai na ya zare?”

Da sauri Hajia tace “To kai yanzu ka yarda kayi ta yawo da matarka a gari kowa na kallo?”

Kallon Hajia yayi yana murmushi yace “Mutane ai ba zasuyi kyau ba babu ido.”

“Kamar ya?” Cewar Junaid, kallonshi yayi yace “Idan na fara k’wak’ule maka ido zaka fahimta.”

Dariya yayi yana matsawa daga kusan shi, ta gabanta yabi ya shafi kumatunta yana fad’in “Allah ya gafarta miki duniyata, har nayi kewarta wallahi, da yanzu tana nan tana kuka tana cewa dan Allah yah Ammar ka tausaya min, karka fita ka zauna a gida, ni ka dake ni ma indai zaka huce.”

Da kallo su dai suka bishi har ya shige b’angarenshi, girgiza kai Hjia tayi tace “Allah ka shirya mana bawan nan naka, wannan idan muka k’ara samun wani kamar shi zamu mutu da ranmu.” Dariya kowa yayi suka shiga ciki suna sauke ajiyar zuciya.

*Da safe* ko da ya tashi da abun ya tashi a ranshi, sai yanzu ne yake asalin jin haushin abun sosai, ya zage shi ya zage abar son shi, a hakan ma wai bayan yasa an daddaka d’an uwanshi, a gaskiya ya gama shawowa dashi ba kad’an ba, wai shi ya kira da mai k’walwar kifi kuma dak’ik’i, shiryawa yayi ya fita bai tsaya ko ina ba sai alimentation, kifi ya siyo kifin ma babba ya kamo hanya ya dawo gida.

Cikin madafa ya shiga dashi su Zeituna na ta k’ok’arin had’a abin kari, da kanshi ya d’auki babban faranti ya juye shi ciki ya d’auki wuk’a, suna kallon ikon Allah su dai ya cire kanshi tare da bud’e cikinshi, kwatta kwatta ya dinga k’arewa kan kifin kallo, basu ankara ba suka ji ya jefa wuk’ar ta bigi tagar dake kallon bayan gidan yana fad’in “Kaji haushi Ammar, ya had’aka da kifi kuma babu abinda kayi.”

Juyawa yayi zai fita ya ga duk suna kallonshi, nuna musu kifin yayi yace “Ku je ku duba kuga k’walwar tashi sai kuji dad’i tunda ya kamanta ni dashi.” A hassale ya fita rai b’ace ya bar gidan gaba d’aya.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231 232 233 234 235 236 237 238 239 240 241 242 243 244 245Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected