BADAK'ALA COMPLETE HAUSA NOVEL

BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL

Haushi ne yasa Abba barin falon rai b’ace inda Ammie ta bi bayanshi, harsu Imranatu da su Naseer ma bin bayansu sukayi, Abbas ma cikin kamala ya fita tare da Imran d’in inda suka k’ara tattaunawa akan lamarin, daga nan shima gidan kakannin na su ya nufo wanda suka rasu shekaru da suka wuce yanzu sai yan uwan mahaifiyarsu ne a gidan da iyalensu, tun a k’ofar gidan ya had’u da Abba da su Bashir cirko cirko suna kallon Abba daya jefa jakarshi a mota, da mamaki Abbas ya kalli Ammie da ita ma take kallonshi jiki a sanyaye yace “Ammie lafiya? Ba dai tafiyar ce ba?”

Cikin k’asa k’asa da murya tace “Nima tun d’azu abinda nake tambaya akai kenan ya min shiru.”

Abba daya rufe boot d’in mota zai shiga mazaunin matuki ne yace “Duk mai tafiya ya zo mu tafi, wanda ba zashi ba kuma saiya zauna.”

Aabbas ne yayi saurin cewa “Abba ka barshi to zan tuk’a mu zuwa airport d’in, bara na kira Sameera.”

Da sauri ya shiga kai tsaye kuma d’akin da suke sauka ya wuce, kwance ya sameta akan gado, shi farko ma mamaki ta bashi daya ganta wai tana kuka, amma da yaji harda shashek’ar kuka take wai ita an mata magana sai ta ma bashi haushi, daga k’ofar d’akin yace “Malama ki taso mu tafi idan kin gama kukan to.”

Shiru tayi kamar ba tasan ma dashi a wurin ba, cikin dakakkiyar murya yace “Nace ki taso mu tafi ko, Abba ne a waje ke jiranmu fa, kinsan kuwa a kan ki ba zan yarda na sake b’ata masa rai ba.”

Ai kamar jira take sai ta d’ago cikin kuka ido sun mata jawur tace “Sai ka tafi mana, kasan ba zaka b’ata masa rai a kaina ba meyasa ma ka zo inda nake, ku tafi ku barni babu inda zanje ni.”

Ko takalmi bai cire ba ya shigo d’akin ya d’auki gyalenta dake kan gadon ya rik’e d’aya hannun kuma ya kama damtse ya jata, tuburewa tayi tana fad’in “Wallahi ka sake ni, ka rabu dani na fad’a maka babu inda zanje fa.”

Har sun fito fili gidan taga da gaske janta yake sai kawai ta kalli hannun nashi ta sunkuya ta gartsa masa cizo *(karo na biyu kenan)*, Abbas da saukar hak’oran kawai yaji baisan sanda ya saketa ba yace “Ashhhhh.”

Kallon hannun yayi har jini ya kwanta abinka ga farar fata, a fusace ya kalleta da niyyar zabgeta da mari ma’ana tarihi ya sake maimaita kansa, sai kawai ta zabga da gudu ta koma d’akin ta mayar da k’ofa ta rufe, cikin k’arajin murya take fad’in “Na ce ba zanje ba, ka rabu dani mana ko ana dole ne?”

Dafe k’ugu yayi ya sauke ajiyar zuciya, a ranshi yake ayyana gaskiya badan suna cikin mutane ba, to fa daya b’alla k’ofar nan yau saiya tab’a lafiyar jikinta, dan har yanzu tana wasu abubuwan ne saboda tab’arar da ita da Ammie keyi, amma ba dan haka ba ai abinda tayi yanzu ko Raihan tayi shi saika mata tsinannen duka bare ita uwarta, wata uwar oda da Abba yayi daga waje yasa Abbas zabura ya juya ya kalli k’ofar, sake dawo da kallonshi yayi ya ga k’ofar a rufe, matsawa yayi jikin k’ofar yace “Zan tafi, idan kinga dama ki tabbata a nan, amma ki sani cizona da kikayi bashi kika d’auka kuma zan rama.”

Daga cikin d’akin tace “Ka rama mana, ko kashe ni zakayi ba zanji ciwo ba indai har zaku tafi ku barni, dan wallahi saina ci uwar matar nan ko kuma na k’ona garin nan.”

Wata zuciyar ta fad’a mishi hushi ba naka bane tunda kasan halin kayanka, a hankali ya saisaita nutsuwarshi ya d’an had’a kanshi da k’ofar d’akin yace “please Sam kar kiyi abinda bai dace ba, dan Allah na rok’e ki, kinji.”

Cikin kukan daya tabbatar daga zuciyarta yake tace “Ba zan iya ba Abban Ameer, matar nan fa mahaifina ta kalla ta fad’a mishi mak’aryaci, kana ganin na zama ‘yar halak idan har na rabu da ita?”

Wata odar ya sake ji wacce ta sashi sake fad’in “Meera ki bud’e k’ofar nan ki fito mu tafi, Abba yana jiranmu kuma kinsan shi ma ranshi a b’ace yake.”

Ba tare data daina kukan ba tace ” Ba zan biku ba Abban Ameer, kawai ku tafi ku barni anan.”

Yasan tunda ta fara ba zata sauko da wuri ba, gashi kuma har ga Allah shi ma baida niyyar sake kwana anan saboda akwai muhimmin zaman da zaiyi a daren yau d’in, dan haka yace “Shikenan zan tafi na barki anan, amma ki min alk’awarin ba zakiyi fad’a da matar nan ba.”

Shiru tayi sai kukan da take rerawa har yanzu, a hankali ya sake cewa “Please, do it for me, karki manta cewa ni mijinki ne, sannan kin min alk’awarin yin duk abinda zai faranta min raina.”

Har yanzu shiru babu alamar zatayi magana, dan haka ya juya ya fita yana sake tattare gyalenta dake hannunshi, yana zuwa Abba bai bari ya amshi tuk’in ba, saida suka fara tafiya Ammie ta tambaya ina autarta? Yana fad’a mata tace ba zata taho ba ta kalli dake tuk’i kamar zaiyi ihu tace “Dan Allah ka aje ni na koma wajenta, gobe saimu dawo tare da ita.”

Wani wawan birki ya taka daya sa su tsorata, sauke jajayen idonshi yayi a kanta wanda yasa gabanta dukan dubu uku uku, da sauri tayi k’asa da kanta hakan yasa Abba cewa “Ki zab’a to, idan har na ajeki anan sai dai kuyita zama ke da ita, tunda abun na ku iskanci ne.”

Tun daga lokacin babu wanda ya sake magana a cikin su har suka isa airport suka shiga jirgi suka sake d’agawa, a haka suka kai gida tafiyar babu dad’i ko kad’an.

*Bayan tafiyarsu*

Tun bayan tafiyarsu da kwana biyu Ma’arufa da Ma’aruf suka zo Abuja a motar abokin Ma’aruf, shi da kanshi ya zo har k’ofar gidan wajen mai gadi yake tambayar ko yallab’ai yana nan? Kasancewar abubuwan da suka faru yasa Abbas d’aukar ma’aikata wanda suka san aikinsu yasa mai gadin cewa “Lafiya kake neman Alhaji?”

K’aryar da yayi cewa shi yaron yallab’ai ne yasa mai gadin cewa “To ka kira shi mana kaji inda yake.”

Cikin son lauyewa yace “Eh kuma fa hakane.” Daga haka ya juya ya bar k’ofar gidan, amma rashin sanin inda zai samu bayani akan Abbas na gari ko bayanan yasa ya fara sintiri a unguwar dan sanin ta yanda zasu fara, yana ganin lokacin da aka fita da yara idan zasu tafi school kuma yana ganin lokacin dawowarsu, haka kuma yana ganin shigar Saleem gidan wanda a wannan lokacin ke yawan sintiri gidan duk dan son samun kusanci da Raihan, idan zai zo haka yake kashe ma su Khalifa kud’i sosai sannan ya kawo musu da sunan tsaraba, faran faran yake nuna musu a fuska yayin da k’udirinshi kuma mummuna ne, kuma duk wani motsinshi Fadila ita ma a hankalce take da shi, sai dai har yanzu Raihan ta k’i yarda su keb’e daga ita sai shi bare harya fad’a mata wani abu da zai sa ta fahimta, a hakane washe gari kwana uku sai ga motar su Abbas sun dawo daga basraba wanda hakan ya wa Ma’aruf dad’i kuma ya hanzarta zuwa ya d’auko Ma’arufa a gidan da suka sauka.

Yaran sunyi farin cikin dawowar iyayensu da kakaninsu, amma basu ji dad’i ba da aka ce musu mahaifiyarsu bata taho ba, bayan sallah magriba Abbas ya shira tare da Abdul suka fita a motarshi, duk da yana sauri ya dawo dan akwai taron da zai shiga da compagninshi na motoci k’arfe *09:00* am saboda wasu manyan bak’in da suka zo bai hanasu tafiya a hankali ba suna hira, cikin minti ashirin suka isa asibitin kud’i wacce d’aya daga cikin yaran *ABBASIYA* ne mamallakinta, bayan sunyi parking ne Abbas ne ya kalli Abdul yace “Ka jirani ina zuwa.”

Cikin mamaki da fargaban abinda ya kawosu asibiti Abdul yace “Dady lafiya ko? Waye ba lafiya? Kai ne?”

Murmushi ya masa yace “Bani bane, kuma kowa lafiyarsa k’alau, kawai dai na zo ganin wani ne a ciki.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231 232 233 234 235 236 237 238 239 240 241 242 243 244 245Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected