BADAK'ALA COMPLETE HAUSA NOVEL

BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL

Ya d’an jima a wannan halin yana tunanin da sam babu mafita, yana cikin haka yaji wani sak’on ya shigo wayarshi, da sauri ya duba dan a tsorace yake, yana dubawa kuma me zai gani? Sabuwar lamba ce ta turo mishi hotunan Raihan tsirara, zunbur ya tashi tsaye ya rufe ido ya dafe kanshi yana so ya samu kowace irin addu’a a baki amma ya kasa, a karo na biyu sake sakin wayarshi yayi ya fad’i kan lallausan carpet d’in, voice not d’in da aka turo ne yayi saurin d’auka ya bud’e, tattausar muryar Saleem ce yace “Shin da kake nan zaune gida ka tura ‘yarka can kasan me take aikatawa ne? To wannan ma sanfuri ne, nan gaba zan turo maka da video yanda nake mu’amulantar ta.”

Cikin matsanancin sauri ya nemi lambar Raihan, tana d’auka daga can b’angaren cikin muryar dake son yin kuka yace “Kiyi gaggawa ki shirya kije airport, ki hau duk jirgin da kika samu ki dawo gida *Raihan*.”

Tabbas Raihan ta tsorata dan kuwa bata tab’a jin ya kama sunanta ba, cikin sauri kamar yanda yace ta tattaro kayanta ta nufi airport d’in, tayi sa’ar samun jirgin da zai tashi zuwa Abuja, dan haka ta hau aka juyo da ita babu shiri.

Suna gama yawa ya sake yin zaune yana matsa k’irjin shi da yaji ya mishi bala’in zafi, tunanin abinyi yake nema har saida yaji lambar nan ta sake turo mishi da sak’o kamar haka _”Kayi gaggawar aurar da ita, idan ba haka ba zan kafa mata tarihi kuma mummuna, idan bakayi abinda nace ba wannan hotunan zasuje inda baka tsammani ne, domin kuwa zan d’ora su a kafafen yanar gizo ta yanda kowa zaiga tsiraicin ‘yarka, a haka ma zata rasa mijin da kuka zab’a mata.”_

Had’a kanshi yayi da gwiwa ba tare daya shirya amsar da zai bawa mai turo sak’on ba, shi dai kawai yasan alhaki ne ya fara biyarshi tun yanzu, dama ance idan kayi da ‘yar wani za ayi da taka kaima, a hakan kuma yana ganin ko da ace Raihan bata tab’a sanin d’a namiji ba to angama dashi tunda har akaga tsiraicinta, kai shi sam bai ma yarda da babu abinda ya faru ba, tayaya namiji zai samu hotonta haka babu kaya a jiki inhar ba wani abu ne ya shiga tsakaninsu ba? Yana tsaka da wannan tunanin wani sak’on ya sake shigowa cewa _”Tunda baka da lokaci na zanyi abinda ya dace, da fari zan fara tura hotan a wayar mahaifiyarta, daga nan kuma zan sake shi duniya ta gani, ni ba kud’i nake nema a wurinka ba, ka aurar da ‘yarka kawai ga wanda ka zab’a mata.”_

Sai lokacin ya kira lambar Saleem na d’auka ya canza murya Abbas kuma yace “Bansan ko waye kai ba, amma dai nasan baka nufi na da alkairi, dan Allah karka saki hotunan nan domin kar mutumcin ‘yata ya zube, nasan gabarka ba zata wuce dani ba dan haka ka d’auki fansarka a kaina, dan Allah karta shafi iyalina.”

Cike da izza yace “Ka fad’i gaskiya, amma ka sani ba zan huce ba har sai naga ka tara taron jama’a zasu shaida d’aurin auren ‘yarka.”

A tak’aice yace “Zanyi, zan d’aura mata aure da safiyar gobe da Abdul, ban buk’atar had’uwa da kai, amma dan Allah ka goge hotunan nan daga wayarka, ba mutumcin ‘yata bace harda ni kaina.”

Cike da dariyar iskanci ya amsa da “Saina gani idan kayi abinda nace.”

Makullin mota ya zara tare da takardar da Ma’arufa ta bashi yayi gaba ya bar gidan, a hanya tunani kawai yake wanene kuma wannan? Shin tarbiyar daya bawa Raihan kenan? Meyasa haka ta fara faruwa dashi? Wayarshi ya d’auka ya duba takardar nan ya turawa Ma’arufa wannan kud’in, bayan kud’in sunje yana ganin tana kiranshi amma ya k’i dagawa harya isa gidan, falon Sameera ya zarce ya sameta zaune ta gama waya da Bashir tana tambayarshi ko yasan abinda ke faruwa, amma yace mata bai sani ba tun jiya ma da rana rabon da su had’u, tana ganinshi ta mik’e da sauri tana fad’in “Abban Ameer sannu da zuwa, lafiya ka fita daga gida cikin sauri haka?”

Saida ya kalli falon da kyau kafin ya kalleta yace “Idan Raihan ta zo kice ta same ni a falo na.”

K’ofar da zata sada shi da falonshi ya nufa ita kuma tace “Raihan kuma? Amma ai bata nan, ko ka manta ne?”

K’ala baice mata ba harya shige, ita kam mamaki da damuwa ne suka hanata zama sai kai da kawowa, haka yara suka dawo daga islamiyya suka sameta, kiran Harira tayi ta had’a ta dasu ita kuma ta ci gaba da tunani, tana haka taji sallamar Raihan, tana juyowa ta ganta da jaka ta kinkimo cikin doguwar riga sai d’an siririn d’an kwalin data d’ora, da sauri ta k’araso ta rumgumeta tace “Ammie na, ya kike?”

D’agota tayi daga jikinta fuskarta cike da damuwa tace “Mamana lafiya? Meyake faruwa ne? Ya kika dawo haka kwatsam? Meyasa Dadynki ke nemanki?”

Cikin sanyi tace “Ammie i don’t know, nima kawai Dady ya kirani a waya yace nayi gaggawa na zo, i hope komai lafiya?”

Girgiza kai tayi tace “Ba nace ba Mamana, amma kije yana son ganinki a falon shi.”

Ba tare da tunani ko damuwar komai ba ta aje jakarta ta nufi k’ofar tana fad’in “Ok Ammie.”

Da sallama ta shiga falon, ganinshi zaune ya d’ora gwiwar hannunshi kan k’afafun shi kanshi k’asa ya had’e hannaye, sai kuma k’afafun shi da yake d’an bunbugasu, sallama uku tayi amma bai iya amsa mata ko d’aya ba, tsoro ne ya fara ziyartar ta amma a haka ta k’arasa kusa dashi ta zauna k’asa cikin taushin murya da sanyi tace “Dady?”

D’ago kai yayi ya sauke kanta, gabanta ne yayi muguwar fad’uwa saboda ganin idonshi jawur kamar yayi kuka, mik’ewa yayi ya shiga bed ya dawo hannunshi rik’e da wata sharb’eb’iyar waya data sanya gudun gabanta tsananta, yana zuwa zaune ya sake yi ya kalleta ya d’auki wayar shi ya mik’o mata cikin rawar murya yace “Raihan waya d’aukeki hotonan?”

Hannu tasa ta karb’a danta gani, da sauri ta dafe k’irji ta d’aga kai ta kalleshi sai taji wata kunyarshi ta rufe ta, sake kallon hoton tayi ta k’ura musu ido, ita ce ke wanka kuma ba’a ban d’akin gidan nan ba na basraba, to kenan waya d’auke ta? Waya bibiyeta haka? Tana cikin kallon taji tsawa daga Abbas tare da kashe ta da mari yana fad’in “Nace waya d’auke ki wannan hoton? Gaban wani d’an iskan kika tub’e?”

Sakin wayar tayi ta dafe kunci hawaye wani na bin wani ta kalleshi a firgice, d’an siririn hannunta ya fizgo ta matso daf dashi cikin k’arajinmurya yace “Ba dake nake magana ba Raihan? Ke yanzu har ni zaki zubarwa da mutumci? Ina ganinki luf-luf yanzu nan ke har kinsan namiji? Raihan meyasa baki fad’a mana kina son aure ba? Amma shine zaki fita waje kina iskanci har ana d’aukar ki ana turo min da hotunan.”

Tsaye ya mik’e ya fara zabga mata bulalar nan baji ba k’akk’autawa, Raihan da zafi ya ratsata ta ko ina kuka take tana fad’in “Wallahi Dady ban san waya d’auki hoton nan, ka yarda dani ban tab’a iskanci ba a rayuwata, dan Allah Dady kayi hak’uri karka kashe ni.”

Sameera da taji kukan Raihan da gudu ta shigo falon, ta taho a sukwane zata tunkarosu ya d’ago ya d’aga mata hannu da cewa “Wallahi kika k’araso nan dake zan had’a.”

Tsayawa tayi tana kallo ya sake cin gaba da dukanta yana fad’in saita fad’a mishi ubanwa ya koya mata iskanci, da gudu Sameera ta sake fita sai part d’in su Ammie, ta sameta tana shirin kabbara sallah azahar, ai tana fad’a mata suka rankayo tare suka shigo, da k’yar Ammie ta dakatar dashi kafin ya tsaya cikin b’acin rai ya kallesu yace “Ko ku shirya ko karku shirya gobe zan aurar da ita kafin ta ja min abin kunya.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231 232 233 234 235 236 237 238 239 240 241 242 243 244 245Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected