BADAK'ALA COMPLETE HAUSA NOVEL

BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL

Har ta fara takawa sai kuma ta tsaya ta kalleshi, cikin gadara da isa da rashin tsoron abinda zai biyo baya tace “Saboda da kai na same shi.”

Wucewa tayi ta barshi tsaye, had’e labb’anshi yayi yana lasarsu, har ga Allah baisan ta yanda zai fara fad’awa yarinyar baya son ya ga ana nuna masa k’iyayya ba, musamman ma daga mutane masu mahimmanci a gare shi, saboda bata son shine yasa ma bata k’aunar d’an data haifa dashi, to wace irin k’iyayya ce take masa?Wani shu’umin murmushi yayi dan har ya tsara abinda zai rama shi ma, juyawa yayi ya nufi d’akin Ummy sai Hajia da tace masa “Bata nan.”

Tsayawa yayi ya juyo yana kallon agogon hannunshi, shi dai duk yau banga Ummy a asibiti ba, to kuma in bata gida tana ina kenan? Saida ya zo kusan Hajiar yace “Ina taje a wannan daren?”

Tsakiyar idonshi ta kalla yanda ba kowa da falon zaiji ba tace “Tana arlit yanzu, amma gobe Abbanka zai je ya taho da ita.”

“Arlit kuma?”

Bata bashi amsa ba sai kallonshi da tayi kawai, sunkuyawa yayi kamar zai fad’a kanta shima cikin rad’a yace “Hajia lafiya? Yaushe ta tafi ? Me yasa kuma ban sani ba?”

Kafeshi tayi da ido kawai hakan yasa yace “Dama ta fad’a min Abba na mata wasu abubuwada ni kaina fa bana jin dad’insu? Ko dai korarta yayi?”

Saida ta d’aga kafad’a tace “Kusan haka.”

“Kusan haka.” Ya fad’a yana jinjina kai, fita yayi daga falon yana tunanin abunyi.

Kamar kullum yaran sun tafi b’angarenshi suna ta wasarsu, Ameera yaja a jikinsa ya kwantar da ita saman k’irjinta yana lallab’a yana shafata, da wani abun ya d’auki hankalinta ta mik’e zata tashi saiya mayar da ita kwance, tun suna haka har ta gaji bacci ya d’auketa, ko da ya lek’a fuskarta yayi dariya yana d’an cike leb’enshi yace “Da kanki zaki zo na hukuntaki kan tsiwar da kika min.”

Ci gaba yayi da kallon yaran saida suka gaji suka ga dare yayi sannan Ameer ya kama hannun Imam yace “Abba gida zamu tafi, Imam bacci zaiyi.”

Aje Ameera yayi kan kujera yace “Muje na raka ku to.”

“Ameera fa?” Ya fad’a yana kallon Ameera dake bacci, saida ya kama hannunsu suka nufi k’ofar fita yace “Tayi bacci mana.”

Ameer ne yace “Abba Ummy fa ba zatayi bacci ba idan bata nan, tare suke kwana akan gadonta.”

Murmushi yayi yace “Sai ka ce ta zo ta d’auke ta to.”

“To.” Ya fad’a suna shiga b’angarensu, saida ya ga shigarsu falon kad’ai ya dawo, d’aukar Ameera yayi ya kaita d’akinshi ya shinfid’e ya dawo ya kashe wuta da tv ya kwanta kan kujera yana jiran zuwanta, ya sani ne dole ta zo dan zata iya hak’ura in cikin mazan ne amma banda Ameera, yarinyar data tab’a yanke hannu da reza wajen k’in ji, ita kuka yarinyar ma kuka aka rasa wa ya yanke d’in.

Ko da suka shiga ta k’are musu kallo tace “Ina Ameera?”

Ameee ne yace “Abba yace kije ki d’aukota tayi bacci.”

Sak’e tayi tana kallonshi, Abba kuma? Lallai ma ai ita d’in ba sakarya bace, bayan ihu da rashin kunyar data masa zata yarda taje su had’u, ai sai dai in a cikin mutane suka had’e, kallonsu tayi tace “Ku je ku kwanta to.”

Wucewa sukayi kowa ya kwanta a inda yake kwantawa, hannayensu duk suka d’aga tare da ita sukayi addu’a kafin suka shafa a jikinsu, tana hangensu har bacci ya d’aukesu cikin nutsuwa, tashi tayi ta k’ara gyara musu kwanciyar ta sumbaci kowane, dawowa tayi kan gadonta ta d’auki wayarta, lambarshi ta kira lambar data kasa gogeta a wayar kuma ko sak’on gaisuwa babu mai aika ma wani. Sanda kiran ya shigo wayarshi saida ya ji tsinkewar gaba dan abu ne da baya faruwa ko ya jima bai faru ba, saida ya k’ara gyara kwanciyarshi ya lumshe ido sannan ya d’auka, cikin muryar da ko a bacci ya tashi takan zama kamar ruwan d’umin dake wartsakar da gajiyarsa, muryar da ko hayaniya take masa yana iya tsayawa ya saurare ta, murya ce da ko halin rashin lafiya yake yasan zata iya zama wani muhimmin maganin da zai taimaka masa wajen warkewa, lumshe ido yayi sanda tace masa “Hello.”

Ba tare daya bud’a ido ba yace “Ya akayi?”

Saida ta sake tausasa murya tace “Ameera, tayi bacci ne?”

“Umm.” Ya fad’a k’asan mak’oshi, marairaicewa tayi tace “Dan Allah ka taimaka ka kawo min ita, ba zan iya bacci nesa da ita ba.”

Wani murmushi yayi yace “Wai ke mahaukaciyar ina ce?”

Cikin zazzak’ar murya kamar mai rera masa wak’a tace “Ta gidanku mana.”

D’orawa yayi da “Inba haukanki ba wa ke son ‘ya’ya kuma ya k’i ubansu?”

Jujjuya idonta tayi dan ta fahimci zai ja maganar da tsayi ne ita kuma bata da wannan lokacin, a hankali tace “Malam ni dai taimaka ka kawo min yarinta, yarana ina son su saboda suna da nutsuwa hankali da sanin ya kamata.”

Jim yayi yana fassara kowace kalma data fad’a, iska ya furzar yace “Ba damuwa, kankana, idan akwai abun rubutu kusa dake ki d’auka ki rubuta, wallahi akwai ranar da zata zo ba wai ki min rashin kunya ba, sautin muryata ma idan kika ji sai kin nemi wurin b’uya.”

Bushewa tayi da dariya tace “Ammar, amma zazzab’i na damunka ko?”

Shi kanshi murmushi yayi mai ciwo irin yanda wai Hamna ce ke soka masa iskanci irin na yaran zamani, cikin sigar gargad’i yace “Amman dai kinsan waye Ammar ko? Sannan kinsan kalar na wa iskancin, muje zuwa tunda haka kike so.”

Gyara kwanciyarshi yayi yace “Abu d’aya nake so dake shine, ki janye wannan kalmar da kika fad’a a kaina da kuma yaro na.”

Cikin k’aguwa tace “Zaka kawo min ‘yata ko sai na zo da kaina?”

Murmushi kawai yayi kamar yana gabanta bai tanka mata ba, hakan yasa ta kashe wayar ta aje kan gado, wayar ya bi da kallo kafin ya aje ta gefe, har ya shiga tunanin duniya kuma Hamna da taji ba zata iya hak’ura ba ta sake kiranshi, ko da ya ga kiran kashe wa yayi amma saida ta k’ara maidowa, sake kashewa yayi ta k’ara kira a karo na uku, a k’ufule ya d’auka yana fad’in “In mayya ce ke ki ci kanki kankana, wannan wace irin masifa ce ba zaki barni nayi bacci ba, ke dai da gani zakiyi jarabar tsiya.”

Ido ta zaro tace “Wace irin jaraba kuma malam? Daga kira ta waya.”

Cikin masifa yace “To uwar me zan miki? Me yasa ba zaki kira saurayin nan naki ba mai zubi da figaggar tantabara kiyi hira dashi ba.”

Cikin sanyin murya tace “Ammar me yasa ka daki d’an mutane? Wallahi ko sunanshi ban sani ba daga had’uwar farko ka same shi ka narka kamar kai ka haife shi, kasan dai baka kyauta ba kuma wallahi Allah zai saka masa.”

Tintserewa yayi da dariya yace “Ni ma Allah zai saka min na shiga hurumina da yayi, kuma ina so na nuna miki irin mazan da kike soyayya dasu duk babu wanda zai iya rik’e ki.”

Cike da gatsali tace “Sai kai kenan ko me?”

Murmushi yayi yace “Ni ai na fad’a miki goma kamar ki ma zan rik’e su, bare ke dana yi wa wanka na saka miki d’an wando da hannu na.”

Kamar sub’utar baki sai cewa tayi “Haba ko da nace, ashe tun ina yarinya ka gama lalata ni.”

Dariya yayi kamar yana gabanta yace “Da yanzu shekararki nawa da mutuwa to?”

Cikin rashin fahimta tace “Ban gane ba?”

Saida ya d’aga sauti yanda zata ji da kyau yace “Ina nufin a yanzun ma ba zaki iya d’aukata ba, ina ga tun a waccen lokacin ne? Hamna waccen ma maleji nayi kinji.”

Kamar zata fashe da kuka tace “Ammar Allahya isa, kuma karka manta ka ma yarinyata addu’a ka shafa mata, mugu kawai.”

Wata sanyayyar dariya ya bushe da ita yana kallon wayar data kashe, tashi yayi ya shiga d’aki ya samu Ameera, addu’a ya mata kamar yanda ya nema kuma yake wa yaran, shafa mata yayi tare da komawa d’akin marigayiya wanda har yanzu kayanta kenan ya kwanta, zanin rufar yaja ya rufe duka har kanshi. Abune daya zamar masa jiki yanzu duk zafin da ake saiya rufe kanshi da zanin saboda k’amshin turaren Amna da yake jikin zanin, da iskan turaren ya fara barin zanin saiya sake d’auka ya zazzaga, hakan na samar masa da nutsuwa sosai.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231 232 233 234 235 236 237 238 239 240 241 242 243 244 245Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected