BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL
Saida ta gama shiri tsaf yace ai tafiyarsu ba yau ba saiya koma gida, bata nuna bata ji dad’i ba saboda gudun tashin k’wank’wamanshi dan su rabu lafiya, da addu’a ta rakashi sam bata san tare da wa zai tafi ba, har d’akinta yaje ya tisota gaba suka fito, a motarshi daya bari suka d’auki hanya inda Hamna take addua’r sauka lafiya, gudu yake na ganganci da kauce k’a’ida, ita har ga Allah tasan a d’ane yake jaraba yake neman, a yanda yake tasan ko jami’an kan hanya yau saita Allah su rabu lafiya, ita kuma ba zata so ya ja mata kwana a magark’ama ba, a hankali ta kalleshi cikin rawar murya tace “Yah Ammar ka tafi a hankali dan Allah, kana taka doka fa.”
Ashar d’in daya malmalawa masu dokar da wanda ma aka d’orata yana wajen yasa ta ja baki tayi shiru tana girgiza kai, shirun da tayi kuma wata masifar ce sai ya fara fad’a wai ta maida shi mahaukaci tayi banza dashi, cikin salon rashin kunya tace “To Allah ya huci zuciyarka, bana so nayi laifi ne.”
Damtsen hannunta mai tarin tsoka ya mara yana fad’in “Ba dan kin raina mutane ba, wai ke har ki fito da wandon daya kamata ace mijinki ne kawai zai gani a gaban namiji, to me kile son nuna masa kenan? Ya gani yayi sha’awa ko me?”
Ta wutsiyar ido kawai tale kallonshi ba zata yarda tayi magana ba ya sata a boot ya rufe, cikin masifa ya sake cewa “Ke ko can na kaiki kika k’ara kula wani Hamna saina babbaka d’an iska sai dai uwarsa ta haifi wani.”
Baki bud’e ta kalleshi tace “Saboda me? Akan wane dalili? Kar nayi aure kenan kake nufi?”
Shiru ya mata baice komai ba dan haka tace “So kake na zauna haka har k’arshen rayuwata?”
Ba tare daya kalleta ba yace “Zakiyi amma ba yanzu ba, zan samo miki wanda ya dace.”
A ranta tace “Bigagge kamar ko?”
A zahiri kuma tab’e baki tayi ta kalli titi, suna cikin gudu sosai wata mota ta giftasu da gudu tana zabga oda ita ma ta wuce, zuro kai yayi tsabar neman fitina yace “Idan kunje ku d’auke hanyar kusa aljihu kar mu wuce.”
Dawo da kanshi yayi yana fad’in “Yan iska kawai mashaya.”
Ajiyar zuciya ta sauke ta rumgume hannaye, kallonta yayi ya taka birki da k’arfi yace “Meye? Na dameki? To koma baya.”
Zage ceinture d’inta tayi ta bud’a zata fita dan tafi son haka ma sai kuma ya jawota da k’arfi ya zaunar da ita yace “Ba zaki koma d’in ba tunda ba drebanki bane ni, kenan ma da gaske na dameki ko? Ba komai Hamna Allah yana gani.”
Gyara zamanta tayi ita dai ba tace komai ba har ya sake d’aukar hanya, kallonshi tayi kallo na nutsuwa da basira, yayi shiru abinshi, shigar yan gayu ce jikinshi bleue d’in jeans da bak’ar riga mai dogayen hannu amma ya lank’washe su har zuwa gwiwar hannunshi, takalminshi k’afa ciki bak’i masu kyau, gemun nan yayi luf dashi sai walk’iya yale idan suka gifta ta cikin rana, zara zaran gashin idonshi wanda ke rufe girman idonshi duk sanda ya rufe su, kakkaurar girar mai yalwargashi da tsayi, dogon hancinshi daya tafi daidai da tsayin fuskarsa abun gwanin sha’awa, amma kuma kyawun d’an maciji ne, nan idan yayi wani abun saika rantse a gidan mahaukata ne yake.
D’an kawar da kanta tayi ta kuma kallonshi har yanzu dai hankalinshi na ga tuk’i, cikin sanyayyan murya tace “Kai likitan zuciya ne, amma me yasa baka tsoron saka mutane a damuwa?”
Saida ya fara d’aga idonshi sama sannan ya d’an kalleta, da alama nutsuwa ta zo mishi dan cikin sanyin murya shima yace “Ba damuwa nake saka mutane ba, ina musu magani ne.”
A hankali tace “Comment?”
Kallonta yayi sosai sai kawai yayi murmushi mai sauti yace “Tu ne comprends rien, rien Hamna.”
Kallonshi tayi tace “Me yasa kace haka?”
Ba tare faya kalleta ba yace “Peut être wata rana.”
Cikin odonshi ta kalla tace “Ammar je te connais bien, (na sanka sosai), mai jusqu’à présent je ne comprends rien (amma har yanzu bana fahimtar komai a game da kai).”
Dariya yayi wacce ta fito da hak’oranshi yana girgiza kai yace “Idiote.”
Kallonta yayi yace “Dana bari kin fahimce ni da kin k’ara tagayyara ni kankana.”
Da mamaki ta kalleshi tace “Kamar ya?”
“Comme je le dit (kamar yanda na fad’a).” Ya fad’a yana kashe mata ido d’aya, girarta ta d’aga sama ta kalli titi tace “Moi aussi.”
Kallonta yayi yace “Ke ma me?”
kallonshi tayi tace “Dana tagayyari daka gane.”
Bushewa yayi da dariya yace “Ni na sani dama.”
Da sauri ta kalleshi tace “Vraiment?”
Sake kanne maya ido yayi yace “T’inquiète pas ma puce, chaque chose a son temps, petit à petit les oiseaux…”
Sai kuma ya bushe da wata dariyar yana k’yalk’yalewa da ita, ita ma da bata fahimce shi ba sai kawai taji ta bushe da dariya, kallonshi take tana tayashi dariyar kamar zararru, sun jima suna dariyarsu kafin suka tsagaita kuma akayi shiru, kallonta yayi yace “Me kika ma dariya?”
“Abinda kake ma.” Ta fad’a tana hararenshi, da wannan ne sai tafiyar tasu ta d’anyi dad’i, dan har tsayawa yayi a station d’in Alhaji suka sha mai suka wuce, haka ma saida ya siya mata kayan k’walama suka ci, tafiya tayi nisa sosai kawai ya tsayar da mota a gefe ya kalleta yace “Fita kiyi fitsari yarinya karki min shi a mota.”
Da zata ce masa bata ji, sai kuma taga ya raina mata hankali ma sai kawai tayi banza dashi, cike da zolaya yace “Ko na siya miki 4 (kun dai gane kalmar da english ai) ne kiyi?”
Fuska a had’e ta kalleshi tace “Eh, ko kuma penpers ba.”
Wani kallon shak’iyanci ya mata yace “Wannan ki bari sai zaki fara bulbuli.”
Yamutsa fuska tayi tace “Bulbuli kuma? Yara fa ke bulbuli.”
Kallon baki da hankali ya mata yace “Waccen bulbulin nake nufi wanda ku kukeyi duk wata.”
Murmushin baka da hankali ita ma ta masa tace “Da har na fara tunanin ko an canza ka ne da naji baka saka kaina yayi nauyi ba, amma yanzu na ji na gamsu da kai nake tare.”
Wayarshi ya d’auka yana dannawa inda Hamna ta gyara zamanta ta jingina sosai, Amna ya kira suka gaisa tare da shiga hirarsu ta soyayya, tana kallonshi har bacci ya d’auketa a haka, yana idawa ya kalleta, murmushi kawai ya saki ya ci gaba da tuk’i cikin aminci.
Ganinsu tare ya ba kowa mamaki, har d’akin Hajia ya kaita ya gindaya sharud’anshi wai ko fita karta sake yi ba tare da dalili ba, saida ya gama tsaf Hajia ita dai ta kalleshi tace “To za’a kiyaye.”
Ummy kuma kallon al’ajabi take da ikonshi, inda Hassana da wasu daga cikin dangin Hajia suka bishi da kallo suma, har zai fita Hamna ta fara gunguni k’asa k’asa tana fad’in “Wallahi babu wanda ya isa ya hana ni fita tunda ba yar zaman banza bace ni, kaji mutum kamar wani uba na ehee.”
Juyowa yayi ya kalleta yace “Ki jaraba ki gani to.”
Fita yayi duk suka raka shi da ido, a ranar dai kamar wasa Hamna ta rantse cewa ba zai hanata abinda tayi niyya ba kamar wanda ya haifeta, kai ita ko dan ta nuna mishi bai isa ba ma saita fita a yanda ta ga dama d’in. *Washe gari* tsaf ta shirya dan zuwa salon d’inta, doguwar riga ce ta saka ta kanti kuma ta mata kyau sosai, kallabin rigar ta yane kanta dashi ta fito, a falon suka had’e yana sallama da su Hajia zai wuce, gaisu tayi tasa kai zata fita tsohuwa mai tambaya tace “Amina (yanda take kiransu kenan) banji kin gaishe da shugaba ba?”
Juyowa tayi ta kalleshi sama da k’asa tace “Tsohuwa wane shugaba kuma?”
“Ammaru mana, ba yayanki bane da zaki fice baki gaishe shi ba?” Cewar tsohuwar, tab’e baki tayi tace “Sauri nake Hajjo.”