BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL
Ammar ne ya shigo falon cikin shiri da alamar fita zaiyi rik’e da leda a hannunshi, ba tare da lieutenant ya san da zuwanshi ba ya tsaya bayanshi yana kallon Zeituna dake zubar da hawaye, cike da nuna damuwarshi a kanta yace “Uwa lafiya? Meya faru kike kuka?”
A d’an tsorace lieutenant ya juyo dan baiyi tsammanin mutum a bayanshi ba, ganin Ammar yasa yayi tsaki cikin jin haushi yace “Kai wane irin sakarai ne? Sai yaushe ne zaka fara sallama idan ka shigo wuri? Dubi yanda ka tsorata ni dan Allah.”
Ko kallon inda yake baiyi ba yace “Dama a tsoracen kake shiyasa, meya samu uwata nake so na sani har take kuka?”
Mik’ewa yayi tsaye yace “Idan an fad’a maka me zakayi? Zak…” Bai k’arasa ba Zeituna ta d’ago kai ta kalleshi tace “Dan Allah Abban Ammar.”
Kallonta yayi ita kuma ta dinga lumshe mishi manyan idonta masu yalwar gashi, juyawa yayi ya fice a fusace daga falon, matsowa yayi kusanta yace “Uwa me aka miki kike kuka?”
Girgiza kai tayi tace “Ba komai, bana jin dad’i ne.”
Murmushin ba gaskiya bane ya mata yace “Uwa ko dai Hajia ce ta b’ata miki rai?” Kallonshi tayi da alamar tambaya a fuskarta, lura da hakan yasa yace “Eh mana, ita ce dai mai d’ab’iar b’atawa kowa.”
Murmushi tayi tace “Ba komai.” Tab’e baki yayi ya mik’o mata ledar yace “Ki bawa Amna wannan.”
Har ya juya zai fita Zeituna tace “Ba zaka shiga kaga Ummy ba? Kamar tana cikin damuwa fa.”
Yana juyowa ya kalleta da alamar damuwa da tashin hankali yace “Meya sameta? Wani abun ya faru ne?”
Girgiza mishi kai tayi hakan yasa ya mayar da akalarshi kan d’akin Ummy, yana ya tsaya bakin k’ofa, har ya d’aga hannu zai k’wank’wasa sai kuma ya tsaya, turawa kawai yayi ya shiga babu sallama sai dai babu kuzari a tare dashi, Ummy na fitowa daga ban d’aki ta wanko idonta ta ganshi tsaye, tunawa da cewa duk abubuwan nan da suka faru sanadinshi ne yasa Ummy jin haushi, aje k’aramin towel d’in hannunta tayi ta giftashi zata wuce ta bar d’akin, cikin taushin murya yace “Ummy me yake faruwa ne?”
A zafafe tace “Ban sani ba, koma meke faruwa ai kai ne sila, dan haka ka fita idona in rufe wallahi kafin na sab’a maka kaima.”
A sukwane ta fice daga d’akin ta barshi tsaye, a kasalance ya juyo ya fita shima bai bi takan kowa ba, mai gadi na bud’e mishi k’ofa ya taka motar da k’arfi zai wuce, kamar an tsayar dashi kuma saiya taka birki da sauri wanda ya haddasa tashin k’ura a bayanshi, gidan dake manne da na su gidan ya k’urawa ido yana kallo, tabbas ada akwai mutane cikin gidan ya kuma samu labarin barinsu gidan, sai dai baisan waye ya siye gidan ba da yaga yanzu an mishi sabon gini, irin ginin da akama gidan ne ma ke bashi mamaki, alamu sun nuna babban gidane daga ciki, daga wajen kawai zai iya d’aukar hankalin mai kallo daga waje saboda wata kalar panti da aka shafa mishi mai kama da carreau (tiles), ga shukoki gajeru da suka k’awata k’ofar gidan sunyi luf-luf dasu gwanin kyau, hak’ik’a an kwana biyu da yaga ana ginin wurin, amma yanda aikin yayi sauri yana bashi mamaki, taka motar yayi ya wuce inda zashi.
Tun bayan sallah la’asar dangi na kusa dana nesa suka hallaro, ranar ta yau kam babba ce dan haka ma takanas takano aka d’auko mawak’i daga Agadez, nan fa aka fara kid’in guitar (jita) ba kama hannun yaro, duka mutanen kowa na zaune kan manyan carpet d’in da aka shinfid’a tare da mangal da butocin shayi anata zugawa, wasu kuma a gefe suna gasa gurasa ana ci ana sha ana raha da nishad’i. Ana haka kuma bak’i suka fara zuwa daga garuruwa daban daban, zuwa sallah magriba gidan nan baya zaunuwa ga duk mai son shiru, dan kowa da nashi dangin da suka zo.
Amare na d’aki cikin shiga ta buzaye inda aka lullub’e su ruf da turkud’i, sai bayan sallah isha’i aka fito dasu dan kowace nata angon ya hallara a wurin ana so su musu kari, haka aka shigo dasu tsakiyar filin inda aka ta kid’in guitar kamar zai tashi gidan, buzaye da suka san darajar abin sai b’arin kud’i sukewa mawak’in, amaren na zuwa aka jerasu gaban angayensu, har fuskarsu rufe take hakan yasa kowane ango ya fara nazarin ina tashi amaryar, dan kayan manya ne wanda suka sa basu wani banbantasu ba sosai, Ammar tuni ya hangi tashi dan dama duk ciki tafisu kumari da albarkatun jiji musamman mazaunai, Jibril dake tsaye kusanta ne ya ji Ammar ya janyoshi ya ajeshi gaban Jamila yana fad’in “Dan ubanka ina kai ina wannan kayan? Ai sai ni babban yayanku.”
Kallonshi Jibril yayi yana dariya ya mishi rad’a a kunne yace “Ni ma da zaran ta shigo hannu na zan mayar da ita manyan kayan ai.”
Mayar da kallonshi yayi kan Amna yace “Allah yasa kana da ingantacciyar madarar da zata zamar mata vitamin a jiki.”
Jibril fashewa yayi da dariya ya kai mishi duka a kafad’a yace “Gaban k’annan ka kake fa.”
K’ala baice ba sai fito da kud’i da yayi a aljihu, sabbi ne a mik’e suke kar wanda bla (2000) nasu ma mai kyau ne, mayar da d’aya hannunshi yayi ya goya a bayanshi d’ayan hannun kuma ya fara zuba mata kud’in, suma dai kowa ya fito da tashi suka fara zuba musu kud’in, saida kowa ya gama sannan aka mayar da amare d’aki su Ammar na fita wasu matasa suka shigo gidan suka ce an aikosu da sak’o yana waje, biyu daga cikin dangi ne suka fita wajen, suna zuwa suka samu wasu manya manyan shanu guda biyu, d’aya ta Ammar d’aya ta Amar, gud’a aka saka tare da shelantawa na cikin gida abinda suka bayar, shanu guda biyu daga angaye ayi sabgar gobe dasu, ana cikin wannan farin cikin jiniyar motoci ta karad’e unguwar, GVR Gambo ne ya zo tare da matarshi, ikon Allah aka ce wai sai kallo, kowa na wajen yasan Hajia da yauk’i da kamkamba da miskilanci da shan k’amshi, amma sai gashi yau sunga surukurta wacce ta taketa a komai, ba kowa take kallo ba kamar yanda ba kowa take amsa gaisuwarshi ba, bugu da k’ari tare take da wasu matasan mata biyu, wanda kowa na gidan ya samu labarin cewa d’aya wacce zata dinga mata girki ce, d’aya kuma matashiyar mai yi mata kwalliya ce ta musamman, hatta masauki na musamman da aka ware musu saida tasa suka gyara mata shi sannan ta kwanta, sai dai bata ji dad’in yanda Hajia da kuma babbar matar gidan wato Ummy suka k’i kwantar da kansu a wajenta ba, domin kuwa Ummy a sama sama suka gaisa dan halin da take ciki ma ya isheta, Hajia ma k’amshi tasha sosai ta hakimce saida taje ta gaisheta. Yau ma haka gama sabgar saidai har gari ya waye wasu basu kwanta ba, saboda anata gyaran kayan abincin da za’a girka da safe wanda za aci bayan d’aurin aure.
*Weeding day*
()
Da misalin k’arfe *08:30* na safe dubbanin mutane ne suka shaida d’aurin auren amare uku da angayensu a k’ofar gidan *Alhaji Suleymane Gaga*, sai auren Maryama da aka d’aura shi a gidan malam Rabi’u dake nan cikin garin, su Husseina duka sun halarci d’aurin auren, bayan an d’aura anata gaisawa har Alhaji ya nemi gabatarwa da malam Rabi’u k’annan shi Hassana da Husseina dan su gaisa, Husseina na daf da shiga mota Labaran zai jasu Alhaji ya dakatar dasu ta hanyar fad’in “Yan biyu ku gaisa da kakan yarinyar mana.”
Juyowa Husseina tayi da murmushi a fuskarta, ido cikin ido, ido hud’u sukayi da malam Rabi’u, kakkafewa idonta sukayi a kanshi ta kasa katab’us, da k’yar ta d’aga yatsarta ta nuna shi murya na rawa tace “Kkk…kai, Rabi’u.”