BADAK'ALA COMPLETE HAUSA NOVEL

BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL

Wani k’arfi ne taji ya zo mata ta tunkari d’akin da gudu, babu wanda yayi yunk’urin binta a guje sai k’wala mata kiran da suka shiga yi, a lokacin Amar da Jibril sun fito sai cikin ma’aikatan asibitin dake binsu a baya zasu tafi da gawar morgue, yanda suka ji suna k’wala mata kira gashi sunyi karo da ita a k’ofar shiga yasa Jibril k’arfin halin rik’o hannunta, da k’arfin bala’i tasa d’aya hannun ta turashi baya har yayi tangal tangal sai kuma ya tsaya cak, ta, cikin ankarewa da mazantaka Amar ya rik’ota gaba d’aya, dan inba haka yayi ba zata zille masa, k’ok’arin kubcewa ta shiga yi da wani mugun kuka da iya k’arfinta, saida ya rintse idonshi gam ya had’e yawu yayi salati ga annabi sannan yayi k’unar bak’in waken d’ora kanta a k’irjinshi amma jikinta bai had’u da na shi ba, hanya suka basu suka je wucewa da gawar, kukan kura tayi ta rik’e gadon tana shirin bud’e zanin rufar dake jikinta, wannan karan kam k’arfi yasa mata yana son b’anb’are hannunta daga jikin gadon, zubewa tayi zaune ta rik’e gadon gam tana kuka tana fad’in “Wallahi bata mutu, bata mutu ba yer uwata ku sake dubata da kyau, Amna ki tashi dan Allah karsu rufe ki kinji.”

A lokacin su Hajia suka shigo suma suka fara rik’eta, da tsiya aka rabata da gadon aka turashi aka fita, daga zaunen nan tabi gadon da kallo tana zuwa k’ugunta har ta fuskanci k’ofar fitar, kuka take sosai sai Amar daya sulale ya bar wurin yana mai tausaya mata, take yaji wasu k’walla a idonshi shima daya tuna idan fa shine yau aka ce ya rasa nashi rabin jikin Ammar?.

Duk k’ok’arinsu na son su lailayeta zuwa mota su tafi gida sun kasa, sunyi juyin duniya ta k’i basu had’in kai, gashi sun dai babu mai iya d’aukarta, mai iyawa mutum d’aya ne kuma shima baisan a inda yake ba yanzu, hatta lieutenant da ya zo cikin mutuwar jiki bai iya cewa komai ba kallonsu kawai yake suna jata, zuwa Labaran ne kad’ai ya kwakwafeta ya lallab’ata ta tashi suka tafi gida.

Hamna kowa yafi tausayinta, tayi kuka kamar ita ma zata mutu, muryarta ta disashe idonta da fuskarta sun kumbura sumtum, ta k’i ci ta k’i sha sai kuka kawai, tana uwar d’akin Amna zaune rumgume da Ameera wacce yanzu ita kad’ai take yarda da ita. Hadiza da Ummy an rasa ina uwar Amna a cikinsu, dukansu sunyi juriya wajen tak’aita mata kuka,

Tunda aka kwantar dashi bai sake sanin me ke faruwa ba saida ya kwana ya hantse, tunda ya bud’a ido ya kafe wuri d’aya yana kallo, tashi yayi zaune ya sauko da k’afafunshi, kanshi na kallon k’asa yana tariyar abinda ya faru, a hankali yaji siraren hawaye na fita a idonshi, cikin zuciyarsa yake fad’in “Ta tafi? Da gaske ta tafi? Ya zanyi? Me yasa zata tafi a wannan lokacin?”

K’ofar da yaji an bud’e yasa shi d’ago kai amma bai kalli me shigowa ba, har saida suka k’araso suka tsaya kanshi suna kallonshi, a hankali Junaid yace “Ammar ya jikin na ka?”

Cikin girgiza kai yace “Ni ma ban sani ba?”

Amar ne ya zauna kan gadon yana kallonshi yace “D’an uwa, kayi hak’uri kaji, dama duk…”

Katseshi yayi da cewa “Ina take?”

Shiru sukayi na dak’ik’u kafin Jibril yace “Gidanta na gaskiya.”

Lumshe ido yayi, muguwar yunwar da yake ji ce ta had’u da wani zafin zuciya da yaji ya taso mishi, dafe k’irji yayi da d’aya hannu kua yana matsar cikinshi, ba tare daya bud’e ido ba yace “Me yasa baku bari na mata kallon k’arshe ba? Ina son ganin kyakyawar fuskarta.”

Dafa kafad’arshi Amar yayi yace “Kayi hak’uri Ammar, ka mata addu’a shine soyayyar da zaka nuna mata.”

Jinjina kai ya shiga yi kamar k’adangare yana fad’in “To, to naji, zan mata.”

Bud’a ido yayi ya zura k’afafunshi ya sauka daga kan gadon, jiri ne ya d’ebe shi yayi gefen da Junaid ke tsaye kamar zai fad’a masa, da sauri ya rik’e shi yace “Sannu, Ammar jiri ke damunka ka kwanta ka huta mana.”

Amar ne ya kalleshi yace “Ina ga fa kamar harda yunwa, mu kaishi gida sai a samar masa wani abu ya ci.”

Zamewa yayi daga rik’on da Junaid ya masa ya nufi k’ofa, layi yayi tare da neman fad’uwa a wurin Amar yayi saurin rik’eshi ta baya, saida ya gyara shi da kyau ya matseshi a hannunshi suka fita a d’akin.

Gashi dai zaune yana kallon mutane amma tunaninshi da hankalinshi na wani wurin daban, rayuwa bata da tabbas, ya gamsu ya rasa wani b’angare na jikinshi, ta tafi ta barsa da yaran da kullum ya kallesu zai tuna da ita, ta zauna dashi cikin aminci, tayi zama dashi zaman daya zama a tarihi a cikin rayuwarsu, ta mishi alkairin da shi dai bai ga abinda zai iya saka mata dashi ba, addu’a, addu’a ce kawai abu mai mahimmancin daya rage tsakaninshi da ita. Tun yana zama a wajen makokin har zazzab’i ya ci galaba kan shi ya kai kanshi d’akin maganinshi ya burmawa kanshi allura, anan ya kwanta kan gadon dake d’akin yana tuna ranar da Hajia ta yanke hukucin aurensu, ranar auren ta su da irin zamantakewarsu har ranar data yi nak’uda kan gadon nan da yake kwance yanzu.

_Lumshe ido yayi hawaye suka shiga sintiri kan fuskarshi, ba tare daya bud’a ido ba ya hasko ranar da yace mata “Duniya ta yanzu idan nace zan k’ara aure dan Allah ya zakiyi?”_

_Dariya ta masa tace “Ya zanyi kuwa daya wuce na tayaka k’wato zuciyar ko ma wacece har kayi nasara.”_

_Had’e fuska yayi yace “Kenan ba zakiyi kishi na ba?”_

_Sajenshi ta shafa tace “Zan yi mana, amma ba irin wanda kake tunanin zan yi ba.”_

_Hannu ya d’aga kamar zai mareta yana fad’in “Dallah can malama, ni da nake so kiyi tashin hankali ki hana ni ko da shan iska.”_

_Da k’arfi ta cakume shi ta kamkame jikinshi tana fad’in “Yi hak’uri yah Ammar, karka dake ni dan Allah, zanyi kishinka wallahi.”_

_Dariya ya mata ya rumgumeta sosai a jikinshi, cikin muryar shagwab’a tace “Yah Ammar zani kishinka sosai, amma ba zan yarda na tayar maka da hankali ba saboda kishi, ni dai kawai so nake ka min alk’awarin ko da ka sake aure ba zaka wulak’anta ni ba.”_

_Cikin laushin murya yace “Me yasa kike tunanin zan wulak’anta ki Amna?”_

_”Saboda ba ni ce zab’inka ba, kawai Hajia ce ta had’a mu.”_

_Rumgume ta ya sake yi yace “Karki damu duniyata, ina sonki har zuciyata ba zan wulak’anta ki ba.”_

Bud’a ido yayi ya tashi zaune duk k’ok’arinshi na son tare kanshi saida ya kasa ya fashe da kuka, wallahi a lokacin da za’a bashi zab’in rayuwa ko mutuwa daya bita shima su rayu acan, bansan taya zaiyi rayuwa bane yanzu babu ita, ita ke saukar dashi k’asa idan yayi samada k’arfin tsiya, an kai an kawo lokacin da Amna ko fita zaiyi waje saita gargad’e shi ya kiyaye abinda zai sa ranshi b’acewa, baiwar Allahn nan ta zab’i ya daketa ko da zai ji mata ciwo akan ya fita ranshi a b’ace yaja rigima, duk da ta kare shi ta kare mutumcin shi, to yanzu wa zai mishi wannan gatan? Wa zai bashi wannan kulawar? Ya rasa kenan har *abada*.

_*Allah ya jik’an duka mamatanmu ya gafarta musu, Allah ka kai rahama k’abarin iyayenmu mata har da ma mazan, mutuwa irin ta Amna Allah ka basu ladar shahada, Allah ka kyautata namu k’arshen.*_

*A gurguje*

Sanyi sosai kamar agogon da batirinsa ya k’are haka al’amarin ya zama a wajen Ammar da Hamna, shiru da zuba ido shi yafi yawa a cikin rayuwarsu ta yanzu, idon Hamna har sunyi fari fat tsabar yawan kuka da rashin saka kwalli, in dai har yaran zasu kewaye ta saita zubar da hawaye ta kuma aika mata da addu’a, kular da take basu kamar daga cikinta suka fito, a dalilinsu ta aje zuwa salon, tace bata da abinda ya kaisu bare ya kai daidai da su, idan ta tashi tun asuba tayi sallah, haka zata musu wanka ta shirya su cikin kayan makaranta, da kanta ta ke kaisu a motarta kuma taje ta d’aukosu, abinda suke son ci shi zata girka musu da kanta, idan na siyowa ne ta siyo musu da kud’inta, a tak’aice dai ta zama uwar yaran wacce ta haife su. *Ahmad* dama tanti Hadiza aka yanke shawara aka barwa ta tafi dashi, amma duk sati biyu sai Hamna ta tafi da yaran sun gano shi, wani lokacin har kwana suke a can kafin su dawo.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231 232 233 234 235 236 237 238 239 240 241 242 243 244 245Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected