BADAK'ALA COMPLETE HAUSA NOVEL

BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL

‍♀️ *KUTKALE*‍♀️

*(PRISON)*

_MA SADIJA BARKA BARKA DA KAMMALA NOVEL D’INKI *KUTKALE*, ALLAH UBANGIJI YASA MU ANFANA DA DARASIN DAKE CIKI, ALLAH YA YAFE MIKI KURAKUREN DA KIKAYI A CIKI, ALLAH YA BAKI LADAR FADAK’ARWA, SAI MUN JIKI A NOVEL NA GABA INSHA ALLAH._

*Sis Chappa*

_Barka da k’arin shekara 3 a duniya, Allah ya karo shekaru masu albarka, Allah ya baki lafiyar anfanarsu ta hanyar data dace, bébé Khalid yace yana tayaki murna._

✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*
_(Tsintsiya mad’aurinki d’aya)_

☆ *[ T.M.N.A]* ☆ ️

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_

_51_

Ummy ta fito goye da Shureim zata tafi duba jikin Ammar Hajia ta fito daga d’akinta, tana ganinta tace “Ke kuma ina zaki je yanzu da dare da kika goya shi?”

Cikin ladabi tace “Hajia zan duba Ammar ne.”

Da wani kallon rashin mutumci ta kalleta tace “Ban gane ba? Ammar d’in baya lafiya?”

“Eh Hajia, d’azu ne ya samu hatsari a hanya, amma da sauk’i sosai k’afarsa ce kawai ta bugu.”

Cikin fad’a tace “Amma kuma shine banda darajar da wani zai shiga ya fad’a min halin da ake ciki.”

Tsaki tayi ta nufi hanyar fita waje, Ummy kuma tunaninta ko dai ta d’auka Amar aka ce shalelenta, dan haka tace “Kiyi hak’uri Hajia, dan naga ba kya jin dad’i ne shiyasa.”

Bata juyo tace komai ba sai ci gaba da tafiya da takeyi, ganin dai sun doshi b’angaren tare yasa Ummy cewa “Hajia Ammar ne fa.”

Cak ta tsaya ta juyo tana kallonta tace “Ammar ne fa? Eh Ammar d’in, me kike tunani? To saurara kiji da kyau, na jima ina rayuwa cikin k’arya da yaudara, jiya zuwa yau ne kad’ai nasan masoyana na gaskiya, duk gidan nan babu mai k’aunata kamar shi Ammar d’in.”

Juyawa tayi ta shiga ita ma tana biye da ita, babu sallama ta shiga ta samu Amna ta gama gasa masa k’afarsa, zaune tayi kan kujera kusa dashi tana kallon k’afarsa tace “Mijin ya jikin? Ashe takaba ka kusa sani, kaji yanda zuciyata ta buga, kada ka sake min irin haka gaskiya.”

Yanda ta gama maganar da shagwab’a, dariya sukayi sai Ummy data saki baki tana kallon, me ya samu Hajia ne? Ammar ne fa ko ta manta? Yaushe haka ta fara faruwa? Cikin murmushi Ammar ya ja hancinta yana rera mata baitin wak’ar gari ya waye yace “Haba, na gwadaki ne kawai dan ramawa.”

Cikin turo baki tace “Kuma duk gidan nan babu wanda ya iya fad’a min ma sai yanzu na sani.”

Saida ya saci kallon Ummy sannan ya kalli Hajia yace “Ai Hajia sai munsha lahaula, dan soyayyata dake yanda zata jijjiga wasu zaisa a kafa mana na mujiya, dan tunaninsu yaushe ne kuma tayaya haka ta fara faruwa.”

Wani kallo Ummy ta masa jin ya karanta mata tunaninta, dariya Hajia tayi ta mik’e tana dafe k’afarshi tace “Zan tafi saida safe zan zo muyi hira.”

Murmushi yayi har ta juya zata tafi sai kuma ta juyo, ba zato ba tsammani ta rarumeshi ta rumgume tana fad’in “Nima na rama buru-ubar da kake min.”

Sakinta tayi ta juya shi kuma yace “Ramuwa mai citta.”

Fita tayi Ummy na kallo al’ajabi duk ya kasheta, kallonta yayi yace “Ummy zauna mana, kawo min shi dan Allah.” Ya fad’a yana tara hannu ta bashi Shureim.

Kujerar da tayi niyyar zama ta kalla sai taga makullin motar ta, takawa tayi ta d’auki makullin ta nuna masa tace “Dama shi na zo d’auka.”

Juyawa tayi ta fita suka bita da kallo, murmushi kawai yayi ya mayar da hankalinsa kan Amna dake d’an ciccije leb’e, cikin kulawa yace “Lafiya dai?”

Cikin yamutsa fuska tace “Ciwo nake ji yah Ammar, bayana ke wani irin abu ba dad’i.”

Cikin son gano abinda ke faruwa yace “Tashi ki d’anyi tafiya to ko haihuwa ce zata zo da sauk’i insha Allah.”

Had’e labb’enta tayi ta yunk’ura ta tashi, rik’e take da bayanta tana ta safa da marwa a tsakiyar d’akin, ikon Allah da yake haihuwar na kusa bata jima da fara wannan sassarfa ba taji ciwo na tasowa sama, kallonta yake duk inda tayi yana lura da halin da take ciki da kuma yanayinta, da fari duk sanda wuyan k’aramar rigarta ya fad’i saita jashi sama ta mayar, amma yanzu yaga bata kula ba har rabin k’irjinta duk a fili, ga kuma wata uwar zufa dake ta tsatsafo mata a goshi da wuya, sannan idan ciwon ya turnuk’ota saita rabka sallalami da dafe duk abinda ke kusa da ita ko ta durk’ushe k’asa, yanzun ma durk’ushe tayi amma kuma tashin ya gagara, hannunta ta d’ora kan k’aramin teburin dake wurin ta rintse ido sosai take fad’in “La’ilaha ilallah, ya hayyu ya k’ayyum bi-rahmatika astagisu, la’ilaha…”

Da k’arfi ta kalleshi tace “Dan Allah ka kaini asibiti karna mutu, yah Ammar ka taimaka min mutuwa zanyi.”

Da sauri ya taso yana taka k’afarshi da k’yar ya durk’usa kusanta shima yace “Kalleni Amna, kalli fuskata kinji.”

Kai ta dinga girgizawa cikin rad’ad’i tana fad’in “Ba zan iya ba, ka kaini asibiti dan Allah, ka kira min Ummy, bayana ciwo yake kamar zai tsage.”

Mik’ewa yayi tsaye ya dawo kan kujerar da yake ya d’auki makullin mota da wayarshi, dawowa yayi kusanta ya tallabota da nufin su fita, tana mik’ewa sai kuwa ta cakumo rigarshi tamau ta fasa ihun data shiga dodon kunnenshi, yanda yaga tana neman sulalewa k’asa yasa shi azamar tarota, ya fara takawa da ita sai yaji tayi wani irin nishi kamar dai wani abu ya tunkaro zai fito, tsayawa yayi ya kalleta da kyau sai yaga daga inda take durk’ushe har inda suke yanzu duk wasu ruwa ne suka b’ata wurin, dafe goshinshi yayi yace “Oh mon Dieu.”

Da sauri ya fara latsa wayarshi ya danna kiran wayar Ummy, tunda taga kiranshi a wannan lokacin tasa a ranta cewa Amna ce ba lafiya, dan haka ma saida ta mik’e da sauri ta rarumi gyalenta kafin ta tashi lieutenant, tana d’aukar wayar yace “Ummy Amna ba lafiya, kiyi sauri ki zo.”

“To gani nan.” Ta fad’a ita ma da sauri, tare da lieutenant suka fito yana rik’e da Shureim, fita tayi shi kuma ya je d’akin Hajia ya sanar da ita, tare suka k’arasa a lokacin Ummy na shiga Ammar yace “Ummy haihuwarta kusa take, ki dubata in zaiyi mu kaita asibiti.”

Kamata tayi ta kalleshi tace “Taimaka min da safa.”

Ya juya da niyyar shiga d’aki Amna ta sake wani nishi mai k’arfin gaske tana rirrik’e da hannun Ummy, haba mantawa yayi da ciwon k’afarsa ya juyo da gudu, yana zuwa makullanshi ya cillawa Ummy yace “Ummy bud’e min d’akin magani na.” Da sauri ta mik’e ta shiga gaba shi kuma kamar wata yar beby haka ya lailayeta da iya k’arfinshi ya bi bayan Ummy, suna shiga da ita d’akin ya kwantar da ita kan gadon dake wurin musamman na haihuwa, Ummy kuma safa ta sanya da sauri ta tunkarota zata duba ta, kafin ta ida k’arasawa kusanta ta sake d’an d’agowa ta danno wani nishin kamar dai wanda take yi, haba ai wani abu taji ya zubo kamar kayan cikinta tare da wani irin gumi, kukan yaron da suka ji ne yasa Ammar saurin dawowa inda yaji kukan yaron ya sake bud’e k’afafun ta, bai tsaya saka safa ko wani abu ba kawai ya d’auki yaron da cibiya ta laulayeshi, cikin nutsuwa ya fara warware mishi da wani faffad’an murmushi a fuskarshi ganin yaronshi a hannunshi, Ummy ce ta matso tasa almakashi ta yanke cinbiyar, zata kai hannunta da niyar janyo uwa sai kawai Amna ta damk’i hannunta ta sake dank’aro wani nishin, fit sai ga wata santaleliyar budurwa ta fad’o ita ma sai wutsilniya take da kuka a hankali, kallon fuskar Amna yayi yace “Ke duniyata, ya kike neman kashe ni da farin ciki, daga farawa saiki fara min da bibbiyu.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231 232 233 234 235 236 237 238 239 240 241 242 243 244 245Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected