BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL
Ba tare daya ankara ba lieutenant ya kai mishi bugu a k’eya yana fad’in “Dan ubanka yi sauri kaje, daga nan saika biya gidan redio da telebijin duk ka fad’a musu ni Hassan na k’i baka million biyu.”
Juyawa yayi yace “Shikenan zaku gani kam.”
Kallonshi lieutenant yayi, irin tafiyar nan ce idan yayi hushi, hakan kuma zai iya sawa yayi komai, iska ya furzar ya d’aga murya yace “Me za kayi dasu?”
Juyowa yayi yana dariya har ya k’araso kusanshi yace “…
*Yan nigeria Allah ya saka muku da alkairi.*
09/09/2020 à 17:58 – Ummulkhairi: ❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️
*BADAK’ALA*
❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️
*Labarin Gaske*
*NA*
_SAMIRA HAROUNA_
*Litattafan marubuciyar*
*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D’AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD’I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K’ADDARARMU_
*8* _K’ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k’ura)…_
*14* _BADAK’ALA…_
*SADAUKARWA GA*
_*AHALI NA*_
*TAURARIN NIGER*
“`(Tsintsiya mad’aurinki d’aya)“`
_Bismillahir rahamanir rahim_
_37_
Juyowa yayi har ya k’araso kusanshi yace “Alawa zan siyo?”
Jin abinda ya fad’a yasa lieutenant yi mishi kallon baka da hankali ko me? tsaki yayi yace “Zan tsaya nan sauraren wannan shirmen naka ne?”
Kallonshi yayi tace “To Abba gashi na fad’a maka.”
Da k’arfi yace “Uwarka! Alawar uban me zaka siya ta million biyu? Ammar ka kiyaye ni fa.”
Kwalar rigarshi ya kama yana wasa dashi sannan yace “Zan fara tarawa jikokinka alawa ne.”
Girgiza kai kawai yayi cike da damuwa ya fito da k’aramin makulli a aljihunshi ya mik’a mishi yace “Ka samu mahaifiyarka.”
Karb’a yayi ya juya ba tare da yace komai ba, yana shiga falon Hajia ta kalleshi tace “K’aryar banza kawai, kud’in ma da za kayi birgar dasu baka da saika karb’a wajen ubanka.”
Murmushi ya mata yace “Magana sahihiya, kinji fa kema ubana kika ce, to idan bai min ba wa zai wa? Nine fa sanyin idanuyarshi na farko.”
Kai ta d’aga mishi alamar kai tafi can tare da fad’in “Kai dallah can, shalele shine sanyin idaniyar kowa a gidan nan.”
Kallon can ta matse muku ke da shalelen ya mata ya nufi d’akin Ummy, tana shirin fitowa suka had’e a k’ofar d’akin, mik’a mata makullin yayi yace “Inji Abba ki bani million biyu.”
Fizgar makullin tayi ta koma d’akin inda ya bi bayanta, juyowa tayi tace “Fice min a d’aki ka jira ni k’ofa.”
D’aga kafad’a yayi ya juyo ya tsaya k’ofar d’akin, tana d’auko mishi ta same shi da waya a kunnenshi yana amsawa, abinda taji yace kawai shine “Zan turo a duba ta, ni ina cikin cin amarci ne ba zan fara fita ba gaskiya.”
Ta gefen ido ta harareshi ta mik’a mishi kud’in, karb’a yayi yana kashe wayar tare da makullin, kallonta yayi irin ba wasan nan yace “Akwai majiyaciya a asibiti dake buk’atar kulawar d’aya daga cikinmu, Ummy kije ki duba ta.”
“Saboda me?” Ta fad’a a hassale, kallonta yayi yace “Saboda ni jiya aka d’aura min aure, ina hutu.”
Ganin tayi shiru bata da abun fad’a yasa shi wucewa yana fad’in “Duk kwanakin da kikayi ma ba kya zuwa da izinin wa?”
Da kallo ta bishi a ranta tana fad’in “Ya zanyi ma wannan yasan ina da cikin? Zai iya sakani gaba yana min dariya, a k’arshe ma yace na tsufa da haihuwa.”
Iska ta furzar tace “Allah gamu gareka.”
Yana daf da isa wajen Hajia Hamna ta shigo falon da alama daga waje take, riga da wando ne jikinta irin kayan nan na indiya, sai dai tsagar dake da rigar gefe da gefe har saman k’ugun ta, kallabin dake kalar wandon k’arami ne wanda ke saman rabin kanta, k’ura mata ido yayi yana kallo, har ta fice bata kula da tsiyarshi ba, juyawa yayi ya bita da kallo, shi kam ya fara gajiya da wannan yanayin da yake tsintar kanshi a ciki a duk sanda ya ganta, al’amarin girmama yake ba raguwa ba, har zuciyarshi canza salon bugawa take idan suka had’u. Hankalinshi yafi tafiya ga shigar data fita da ita, akan me Hamna bata jin magana? Me yasa ba zata taimaka mishi ba ta dinga rufe jikinta? Me yasa bata son kwanciyar hankalinshi ne? Hasalima bata damu da damuwarshi ba? *Ba zan lamunta ba gaskiya*, yana fad’in haka ya daka mata tsawa yace “Ke.”
Hamna data fara taka makala ko juyowa ba tayi ba, da k’arfi ya sake cewa “Kankana ke.”
Hajia dake zaune tana kallonshi ne tace “Wai kai ba zaka daina kiranta kankanar nan ba?”
Kallonta yayi fuskarshi a had’e rai b’ace yace “Akan me zan daina? A baya ma na kirata haka bare yanzu dana tabbatar.”
“Ka tabbatar dame?” Ta fad’a tana kallon idonshi, Ummy dake tsaye k’ofar d’aki tana nata jimamin tana jin haka ta zaburo tana dariya tace “Ya riga daya saba ne Hajia, zai daina ai.”
Kallon Ummy yayi wacce baiga komai ba a idonta sai tsoro, wato ta d’auka zai fad’a ne? Shi data barshi ma ya fad’a mata yanda zata fahimta, kai shi fa yanzu zai iya fad’a in ya so ayi duk wacce za ayi, sai lokacin ya kalli Hamna data juyo tana hararenshi, yana ganin haka ya bi ta bayan kujerar Hajia ya taka wurinta, da yatsa yake nuna kanshi yana fad’in “Ni dai kika harara ko? Bari kiga iskanci.”
Ai da gudu ta fara haurawa sama dan tasan tsaf zai mata iskancin kamar yanda ya fad’a, tana kaiwa ta mayar da k’ofar ta rufe, Ummy dake binshi da kallo kar ya ja mata magana yasa take fad’in “Dawo, kar tab’a min yarinya wallahi.”
Tab’e baki Hajia tayi dan ita dramarsu bata dameta ba dama, yana zuwa k’afa yasa ya tura k’ofar sai kawai ta bud’e, baya tayi da sauri tana nuna shi tana fad’in “Allah ka fita a d’akin nan, Ummy, Abba zai kashe ni.”
Murmushin gefen labb’a yayi yace “Kinga kuwa banyi tunanin haka ba.”
Da mamakin me yake nufi ta kalle shi, fahimtar da ita yayi ta hanyar fad’in “Eh mana, sai yanzu ne kika fad’a min cewa kasheki ne kad’ai zai zama maganin matsalata.”
Da k’arfi ya shak’o wuyanta da hannu d’aya, fitowa yayi da ita a haka yana fad’in “Ban fad’a miki ki dinga saka hijabi ba? Ban fad’a miki ki daina saka wannan d’an banzan gashin ba? Raina ni ne kikayi kenan da ban isa na fad’a miki kiji ba.”
Ummy da su Zeinabu da Zeituna suna ganin ya fito da ita a haka suka rik’e baki, Ummy ce ta tunkare shi ta fara k’ok’arin b’anb’are hannunshi tana fad’in “Wallahi saketa, Ammar kar ka kashe min yarinya, bana son iskanci fa.”
Saida ya kawota gaban Hajia ya watsota daf da k’afafunta ta fad’i k’asa, rik’e wuyanta tayi tana wahalallen tari da hawaye tsabar wahala, Hajia ya kalla yace “Madame Suley, ki zama shaidata, Allah kar na karya yarinyar nan wani yace zai tambayeni dalili, ki fad’a mata kar ta sake fita babu hijabi jikinta, sannan wannan gashin.”
Ya fad’a yana kamo gashin da hannunshi yaja da k’arfi wanda yasa ta saki k’ara da k’arfi tana rik’e hannunshi, d’orawa yayi da “Idan na sake ganinta dashi reza zan saka na yake shi har da asalin gashinta.”
Sakinta yayi hakan yasa ta tashi da sauri tayi baya tana hararenshi, Hajia ce ta wurga mata harara tace “Sa’anki ne shi da kike hararenshi?”
Sunkuyar da kai tayi tana k’ara jan d’an kwalinta saman kanta, a tsawace Hajia tace “B’ace min da gani malama.”
Rai a b’ace Hamna ta taka da sauri tana d’an bubbuga k’afafu tana gunguni kamar za tayi kuka, da kallo ya bita har ta haye sama sannan yayi k’wafa ya kalli Hajia, wannan kud’in ya mik’a mata yana murmushin shegantaka yace “Ga wannan ko, ni a wurina tafi k’arfin rak’umi d’aya sai biyu.”