BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL
Sauka yayi daga kan gadon yace ” In aureki? Ke a wa? Ke tsaya kiji, halin da nake ciki fa bai haukatar da ni ba ta yanda zan iya had’a kaina dake ba bare kuma har na had’a ki da matata, dan haka ki canza wata buk’atar amma ba wannan ba.”
Zaune tayi tace “Kana nufin ba zakayi na kenan?”
Kai tsaye yace “Eh, haka nake nufi.”
Cike da gadara tace “Ai kuwa zuwa safiyar gobe mummunan sak’on nan zai sauka idon matarta ka.”
Yasan barazana ce dan haka yace “And so what? Ki nuna mata mana, kin d’auka mahaukaciya irinki? Wallahi kina nuna mata ba zaki bar gabanta ba har sai kin rasa k’afa ko hannu ko kuma ki rasa fatar jikinki.”
Jim tayi dan kuwa tasan gaskiya ya fad’a, to ai ita zata fad’awa wani wacece Sameera ba wai wani ya fad’a mata ba, dan haka tayi murmushi tace “Shikenan tunda haka kace, ni kuma zan nuna maka bana maganar banza.”
Cikin jin haushi yace “Shikenan mu zuba mu gani.”
Yana fad’a ya kashe wayar, dafe k’ugu yayi ya shiga zarya yana tunanin ta ina ita kuma ta shigo labarin? Ya akayi ta sani ko? Rasa amsa da jin haushi yasa shi buga wayar a bango take ta tarwatse, ganin haka yasa shi fad’awa kan gadon yana dafe da kanshi da hannaye biyu kamar ya kwamtsa ihu da iya k’arfin shi, tabbas yayi bacci amma baisan wane irin bacci bane, domin kuwa abubuwa ne fal a kanshi wanda yasa yake ji kamar ma a zahiri ne idonshi biyu.
*Washe gari*
Ko da Sameera suka tashi ta d’ora gyaran da suka tsaya jiya, da taimakon su Bilkisu aka had’awa Raihan kayan jikinta musamman kayan bacci wanda ake siyo mata duk jiya, wani abun kam saidai suyi godiyar Allah, ba dan akwai dalar ba antara ta cirewa kawai ake a account da sun d’ora hannu a kai, kasancewar Alhaji Khamis babban mutum ne yace amaryar kawai suke buk’ata, hakan yasa Sameera dan kar a raina mata ‘ya ta kashe mata kud’i kamar ba gobe ta fannin sutura wacce zata saka a gani dai, sark’ok’i ma na milyoyin kud’i aka siya mata ga kuma bala’in gyaran da suka saka aka aiko musu daga mai duguri da kuma sokoto, haka ma daga Niger saida aka kawo musu sak’o duk na gyaran jiki a safiyar yau da yake harka da kud’i, misalin *09:00* motoci uku ne suka paka cikin gidan Alhaji Khamis ya turosu su d’auki amarya da masu rakiyarta, sai lokacin kad’ai Abbas ya fito daga d’aki cikin doguwar riga kana ganinshi kaga damuwa, su Ammie da Abba ne da kuma Sameera suka mata nasiha sosai, daga bisani kuma k’annan ta kuka Uka dinga yi na rabuwa da yar uwa wacce aurenta ba zasu shaida komai ba, Raudat taso taje amma haka Abbas ya murje ido yace ai mutum biyu kad’ai zasu rakiyarta, Imranatu da Bilkisu da suka shirya tafiya da kuma Ammie suna ji suna gani sai Bilkisu ta hak’ura su biyu kad’ai, kuka Raihan keyi kamar ranta zai fita , sai duk ta jita kamar wata marar gata, haka suka d’auki hanya bayan hawaye da Sameera ta zubar ita ma.
Suna tsaye har suka ga fitarsu, Abbas juyawa yayi ya koma ciki Sameera ma juyawa tayi ta koma d’aki cike da jimamin yar ta, zata zauna kan gado sai kuma ta tsaya tana kallon bak’uwar wayar da bata san da ita ba, d’auka tayi tana k’are mata kallo tana jujjuyata, a saninta dai babu mai ita a mutanen data sani, gashi kuma ba taro akayi ba gidan bare tace wani ya manta, tunanin da tayi ne yasa taja sama sai taga ta bud’e da nufin ko zata samu wata shaida da zata nuna wayar wace, amma bud’awar ita tasa zuciyarta kusan daina aiki yayin da ta nemi numfashinta ta rasa, rawar da k’afafun ta keyi yasa ta durk’ushewa ta saki wayar, banda rawa babu abinda jikinta keyi sai hawayen da suka fara zarya a idonta, idonta sun kafe wuri d’aya kan wayar data fad’i gabanta, tana son d’auke idonta amma abun ya gagara, bud’a baki tayi tana wani irin numfashi da shashek’a duk lokaci d’aya, kai take girgizawa alamar a’a amma kuma ganin abun take yana k’aruwa, wani kukan kura tayi ta mik’e tsaye tare da wayar da gudun tsiya kamar wata yar shekara sha shida ta fita daga d’akin ko kad’an ba zaka rabata da mahaukaciya sabon kamu ba, part d’in shi ta nufa tana zuwa ta kama murfin k’ofar d’akin shi cikin sa’a ta bud’e, tana jin ta bud’e tayi wata fitinanniyar kururuwa tare da cire d’an kwalinta ta shiga d’akin, Abbas da kwantawarshi kenan jin wannan abu yasa shi tashi zaune yana kallon mai shigowa, ganinta a birkice yasan ba lafiya ba dan haka ya yunk’ura da sauri ya mik’e zai tarbeta, ai kamar mai tab’in hankali haka ta…
26/06/2020 à 19:39 – Ummulkhairi: ❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️
*BADAK’ALA*
❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️
*Labarin Gaske*
*NA*
_SAMIRA HAROUNA_
*Litattafan marubuciyar*
*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D’AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD’I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K’ADDARARMU_
*8* _K’ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k’ura)…_
*14* _BADAK’ALA…_
*SADAUKARWA GA*
_*AHALI NA*_
*TAURARIN NIGER*
“`(Tsintsiya mad’aurinki d’aya)“`
_Bismillahir rahamanir rahim_
_23_
Da dare ana ta kai da kawowa na hidimar bikin lieutenant inda aka fara gyara kayan cefanai na girkin gobe sai jiniya da odar motoci kamar zasu fasa unguwar, jim kad’an hayaniya ta fara gauraya gidan sanda mutane ke shigowa, mutanen gidan ne suka fara kimtsawa suna umartar yara da su koma sama, saida mutanen suka fara shigowa falon kad’ai aka fahimci ashe duk dangi ne na wajen Suley da kuma wasu daga cikin dangin Soueiba da mutanen arzik’i, duk girman falon nan sai gashi cike da mutane dan mace tafi talatin wanda suka zo kawo kaya, hakan kuma ya faru ne saboda maganar da Hajia ta fad’awa Husseina shiyasa take so ta bata mamaki.
Wata kyakyawar fuskar na gani sak Husseina sai dai wannan tafi d’an tsufa, amma fa ita ma tana cikin shiga ta alfarma da kuma dattako, su Zeinabu da Sa’ada ne suka matsa kusanta suka duk’a suna gaishe ta, cike da fara’a da sakin fuska ta amsa musu kafin ta kallesu a nutse tace “Ina su Ammar ne da Junaid? Yaran nan ko kad’an basa zuwa inda mutane suke sai dai in an zo inda suke.”
Murmushi Sa’ada tayi tace “Kiyi hak’uri Hajia, kinsan ayyukansu ne sai a hankali.”
Murmushi tayi ita ma tace “To, haka kuka ce dai, yanzu ina Hajiar take? Kayan jikanyarta muka kawo mata.”
Zeinabu ce tayi saurin mik’ewa tana fad’in “Suna ciki, bara na musu magana.”
Sa’ada ce tace “A’a ki barshi, ni zanje.”
Mik’ewa tayi ta nufi d’akin Hajia, ba jimawa ta fito suka ci gaba da kawowa bak’i ruwa da jus jus wasu ko sanyi babu saboda basu sanar da zuwan nasu ba, minti ashirin Hajia ta d’auka kafin ta fito, fitowarta tasa kowa ya mayar da hankalinshi kan uwar yan uku, masha Allah, shine abinda wasu ke fad’a yayin da wasu ke mamakin rashin tsufan matar, wata arniyar shadda ce tasa yayin da ta watso wasu sark’a da yan kunnai da zobuna da awarwaro na zinariya, ba dan komai ba sai dan ta bayar da tsoro, dan hayaniyar da taji tasan ba zasu yarda su mata wannan gayyar ba babu wani dalili, wani d’aurin d’an kwali ne ta kashe mai sauk’in gaske wanda yasa manyan kitsonta sauka har gadon bayanta, kwalli ne kad’ai a idonta amma tayi kyau sosai sai d’aukar ido take ga jar fatar nan tayi wani shek’i, kamar d’awisu haka ta tako har ta zo kujerarta ta zauna tana shan k’amshi da k’arewa mutanen kallon hadarin kaji kallon mai bisa ruwa.